Yadda Aka Kama Sojan Da Ke Kai Wa Bello Turji Kayan Yaki
Ya fada a komar ’yan sanda a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’adda kayan sojoji a Zamfara daga Kaduna
’Yan sanda sun kama wani korarren soja da ke bai wa jagoran ’yan bindigan Jihar Zamfara, Bello Turji da yaransa kayan sojoji.
Korarren jami’in Sojan Saman Najeriyan mai suna Ahmed Mohammed, ya kasance yana samar da wa ’yan bindiga kakin sojoji na yaki da sauran kayan aikin jami’an tsaro, kafin dubunsa ta cika.
Aminiya ta gano cewa Ahmed ya yi aikin sojan sam kawai na tsawon shekaru biyar kafin a kore shi saboda wani laifin da ba a bayyana ba.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa, an cafke korarrren sojan ne tare da wani abokinsa a hanyarsu ta kai kayan jami’an tsaro da suka dauko daga Kaduna za su kai wani sansanin ’yan bindiga da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara.
Adejobi ya ce Ahmed ne ya yi wa wani abokin nasa mai suna Mushiri Abubakar, tayin sayar wa ’yan bindiga da kayan da sojoji.
A cewarsa, Mushiri Abubakar ya samar wa sansanonin ’yan ta’adda daban-daban kayan sojoji bayan wadanda ake zargin sun bai wa Bello Turji da tawagarsa.
Da yake gabatar da su a hedikwatar rundunar da ke Abuja, Adejobi ya ce kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da kakin sojoji guda 10, da huluna da rigunan sanyi dai dai sauransu.