Yadda aka kama yaran da suka sace min da

Mahaifin yaron da aka sace Alhaji Muhammad Dan’azumi da ke Unguwar Jaja kusa da Unguwar Borno a garin Bauchi ya ce lokacin da suka nemi yaron suka rasa sai suka ba da cigiya a gidajen rediyo. “Da karfe 11 sai suka kira wayar dana Ibrahim suka ce a ba su lambata. “Dana ya fada min […]

Yadda aka kama yaran da suka sace min da

Mahaifin yaron da aka sace Alhaji Muhammad Dan’azumi da ke Unguwar Jaja kusa da Unguwar Borno a garin Bauchi ya ce lokacin da suka nemi yaron suka rasa sai suka ba da cigiya a gidajen rediyo.

“Da karfe 11 sai suka kira wayar dana Ibrahim suka ce a ba su lambata.

“Dana ya fada min na ce ya ba su, sai suka kira ni suka ce su suka dauki dana.

“Da na samu lambarsu sai na je ofishin ’yan sanda na yi rahoto.

“Bayan na yi ta ba su hakuri suka ce in ba su Naira miliyan 2 da dubu 500, na yi ta ba su hakuri har muka daidaita da su a kan Naira miliyan daya.

“Kuma duk lambar da suka kira ni da ita in an jima sai su yar da ita su canja wata lamba.

“Haka dai har washegari na koma wajen ’yan sanda suka sake kira na suka ce kudi ya samu, na ce eh.

“Suka ce in je wajen gidan man AYM Shafa in shiga hanyar Inkil a hanyar Gombe.

“Daga nan suka ce in juya in bi rukunin gidajen Ibrahim Bako. Na je sai suka ce in juya in bi ta Tirwun.

“Daga baya suka ce in bi ta sabuwar hanyar da Gwamna Bala Mohammed ya yi.

“Da na zo wajen suka ce in juya in dubi Arewa zan ga mutane suna aiki, kada in yi wa kowa magana suna ganina”, inji shi.

Ya kara da cewa, “Na juya suka ce yaya ba su ga kudin ba, na ce yana mota suka ce in koma in dauko, na koma na dauko na je wajen wani ruwa suka ce in haye, na haye.

“Na je gindin wani dutse suka ce in hau, na ce gaskiya ba zan iya hawa ba, suka ce in je in ajiye kudin a gindin wata kuka na je na ajiye.

“Dama sun ce za su kai mini yarona gida, da na ajiye jami’an tsaro kuma sun kewaye wajen. Bayan kamar minti 25 suka zo za su dauki kudin, sai ’yan sanda suka kama su”.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi, Lawan Tanko Jimeta ya ce lokacin da ’yan sanda suka samu rahoton bacewar yaron sai sashen bincike na rundunar ya fara aikinsa kuma ya samu nasarar kwato yaron ba tare da ya samu rauni ba.

Wannan lamari ya jawo damuwa, ganin yadda kananan yara ke aikata miyagun laifuffuka.

Wadanda muka zanta da su sun ce wannan shi ne karo na biyu da yara ke satar dan makwabtansu.

Na farko da suka saci dan wani likita wata hudu da suka wuce sun kashe shi bayan sun karbi fiye da Naira miliyan uku daga wajen mahaifinsa a matsayin kudin fansa.