Yadda aka karrama mai Keke-NAPEP Da Ya Dawo Da N9m da ya tsinta a babur dinsa a Yobe

Kungiyar manyan sakatarorin jihar Yobe ta karrama Malam Ali Bulama, wani mai haya da Keke-NAPEP da ya mayar da Naira miliyan tara da wani fasinjan ya manta a cikin babur dinsa.

Yadda aka karrama mai Keke-NAPEP Da Ya Dawo Da N9m da ya tsinta a babur dinsa a Yobe

Kungiyar manyan sakatarorin jihar Yobe ta karrama Malam Ali Bulama, wani mai haya da Keke-NAPEP da ya mayar da Naira miliyan tara da wani fasinjan ya manta a cikin babur dinsa.

Da yake mika wa Bulama, mazaunin garin Jumban a karamar Hukumar Tarmuwa, takardar shaidar karramawa da kyautar tsabar kudi N100,000, shugaban kungiyar, Alhaji Maisandan Lawan, ya yaba wa mai Keke Napep din bisa gaskiya da tsoron Allah da Ya nuna.

“Wannan mutumin ya cancanci a san shi tare da karrama shi bisa yadda ya nuna gaskiya da sanin ya Kamata don zama misali ga al’umma.

“Duk da cewar da ya so zai iya mallake wadannan kudade da ya tsinta, amma saboda gaskiyarsa da tsoron Allah da malamin ke da shi, sai ya yanke shawarar yin abin da ya dace ta hanyar mayar wa mai shi,” inji shi.

Maisanda  ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Yobe da masu hannu da shuni da su mara wa Bulama baya a kan gaskiya tare da bin sahun abin da suka yi na karrama shi.

Ya kuma bukaci jama’a musamman matasa da su yi koyi da Bulama ta hanyar nuna gaskiya da rikon amana a duk inda suka samu kansu.

A nasa jawabin, Bulama ya ce, mai kudin kuma mazaunin Maiduguri ya hau babur dinsa ne a Jumbam da misalin karfe 9:30 na daren ranar 17 ga watan Nuwamba.

“Da misalin karfe 11:30 ne bayan na kai gida, sai na ga wani buhu dauke da wasu kayayyaki da suka rage a babur din.

“Lokacin da na gano cewa buhun yana dauke da wasu kudi, sai na yi gaggawar fita don neman mai shi, wanda kafin wani lokaci tuni labarin tsintuwar wadannan kudade ya bazu a wannan kauye namu na jumbam.”

“Bayan wani lokaci da taimakon wasu mutanen yankin, an gano mai kudin, inda na mika masa kudinsa.” inji shi.

Bulama, wanda babur din da yake amfani da shi ba nasa ba ne, hayarsa aka ba shi in yayi aiki ya kai balas ga mai shi, ya ce mai kudin ya ba shi N20,000 a matsayin nuna godiya.

Wannan  taron dai  ya samu halartar shuwagabannin al’umma da kuma jagororin masu amfani da keke Napep na karamar hukumar.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe