Yadda aka karrama ’yar shekara bakwai mai kwaikwayon Sarkin Dubai
Cibiyar al’adu ta Dubai ta karrama karamar yarinya da ke kwaikwayon Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, wanda shi ne m,ataimakin shugaban kasar Hadaddiyar Daular larabawa kuma Firayiministan kasar. Wannan yarinya ta shahara ne bayan da aka baje faifan bidiyonta tana kwaikwayon Sheikh Mohammed a shafukan sada zumunta na facebook da makamantansu da […]
Cibiyar al’adu ta Dubai ta karrama karamar yarinya da ke kwaikwayon Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, wanda shi ne m,ataimakin shugaban kasar Hadaddiyar Daular larabawa kuma Firayiministan kasar.
Wannan yarinya ta shahara ne bayan da aka baje faifan bidiyonta tana kwaikwayon Sheikh Mohammed a shafukan sada zumunta na facebook da makamantansu da ke intanet.
An karrama yarinyar ne a wajen wani taron bita da aka gudanar na ‘SIKKA mai kewaye birni wajen bibiyar masu basira, wanda aka gudanar a tsakanin ranakun 24 zuwa 28 na Yulin 2017, inda aka karfafa gwiwar yara su nuna fasaharsu wajen zayyana da ginin tabo da hotuna da maganganun fasaha.
Yarinyar ’yar shekara bakwai, mai suna Mahra Al Shehi ta samu karramawar ne kawai saboda bazuwar bidiyonta tana maimaita jawabin shugaban, har ma ta kai ga Sheikh Mohammed da kansa ya kai mata ziyara. Maganganun yarinyar an ce sun karfafa gwiwar matasan Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kuma halartar da Mahra ta yi wajen wannan taro na ‘SIKKA akewaya birni’ ya sanya yara da dama sun zaki da son ganin wannan gwarzuwa ta su. Mahra dai ta kasance a jerin yara kimanin 150 da suka halarci wannan bita da gwajin fasaha.
Fatma Al Jallaf, Manajar riko wajen shirya tarurrukan cibiyar Al’adu ta Dubai ta ce: “Muna cike da farin ciki ganin yadda taron bitar mu ya samu dimbin mahalarta, domin babbar manufarmu ita ce mu karfafi gwiwar yara su bayyana abin da ke zukatansu ta hanyar amfani da zayyana ko ginin tabo, ta yadda za mu bunkasa al’adu. Muhimmin al’amari shi ne muna cike da farin cikin karrama Mahra Al Shehi, wadda halartarta ya girgiza ruhin shirin, sannan ya tabbatar da cewa Dubai na cike da dimbin matasa masu basira.”
Mahalarta taron sun samu kulawar kwararrun masana kan fasahar kere-kere, inda aka sanya su suka yi aiki da hannayensu wajen yin zayyana a lokacin dogon hutu.
Shirin ‘SIKKA a kewaye birni na nuni da jajircewar Cibiyar Al’adu ta Dubai wajen tallafa wa masu basira da kirkiro sababbin abubuwa, kuma wani bangare ne na baje kolin fasahar zane-zane da zayyana.