Yadda aka kasa gyara titin Kaduna-Abuja a shekaru 6

Ministan Ayyuka, Umahi ya ce nan da watanni 12 za a kammala aikin

Yadda aka kasa gyara titin Kaduna-Abuja a shekaru 6

Aikin gyaran titin Kano zuwa Maiduguri

Kimanin shekaru shida ke nan da gwamnatin Najeriya ta bayar da kwangilar sake gina hanyar Abuja zuwa Kaduna, amma har yanzu abin ya gagara, lamarin da ya sa hanyar ta zama abin tashin hankali ga matafiya.

Ranar 20 ga watan Disamba, 2018 tsohuwar Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ba da kwangilar tare da na bangaren Kaduna zuwa Kano da wa’adin shekaru uku.

An fara bayar da aikin Abuja zuwa Kano mai tsawon kilomita 375.9 me a kan kudi Naira biliyan 155.

Amma an kara kudin a shekarar 2021 zuwa Naira biliyan 642.2, sannan aka sake karawa zuwa biliyan 797.2.

A watan Janairun 2024, Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ya ce dan kwangilar, kamfanin Julius Berger, ya nemi a sake kara kudin zuwa Naira Tiriliyan 1.35, amma Ministan ya ce gwamnati ba za ta iya ba.

Dan da aka ba kwangilar ya kwashe kayan aikinsa a bangaren titin Abuja zuwa Kaduna, duk da cewa  da kyar mataya ke iya bin hanyar.

Muhimmancin titin

Titin Abuja zuwa Kaduna ya hade Kudancin kasar nan da shiyyar Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas, sannan shi ne babbar hanyar zirga-zirgar jama’a da kayan abinci da sauran su.

Duk da cewa ana biyan kudin aikin hanyar ne daga asusun bunkasa ababen more rayuwa na fadar shugaban kasa, aikin bangaren Abuja zuwa Kaduna, bai samu nasara kamar sauran sassan ba (Kadunz-Zariya da kuma Zariya-Kano) da ake gab da kammalawa.

A ranar Alhamis din mkon jiya Aminiya ta sa wakilanta sun tashi takanas su bi bangare hanyar daga garin Zuba mai tazarar kilomita 58 daga tsakiyar birnin Abuja, su bibiyi halin da aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna mai tsawon kilomita 150 yake ciki, har zuwa garin Gonin Gora, da ke da tazarar kilomita 14 daga garin Kaduna.

Wakilan namu sun kuma jiyo ta bakin direbobi da fasinjoji da mazauna kauyukan da ke kan hanyar game da halin da hanyar ke ciki da kuma jinkirin aikin gyaran.

Tarko Mutuwa

Wakilan namu sun ce hanyar a yanzu ta shinkafa da wake, wani bangare an kammala gyara, an tsallake wasu bangarorin da aka fara aiki, a wani wurin kuma tsohuwar hanyar ce ko taba ta ba aka fara ba, ga kuma ramuka.

Binciken ya nuna cewa a kullum, ana yawan samun hadurra da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a kan hanyar.

Kazalika matafiya suna fama da ciwon jiki sakamakon yanayain hanyar da kuma irin girgizar da suke sha a wurare daban-daban a babbar hanyar.

Ramuka sama da 100

Kananan ramuka akalla guda 78 da kuma manya guda 47 ne wakilanmu suka kirga a yayin tafiyar mai nisan kilomita 150 daga Abuja zuwa Kaduna.

Sun ce lalacewar da akasarin sassan hanyar ta sa dole masu ababen hawa tafiyar cikin taka-tsantsan.

“Misali, akwai ramuka bakwai daga dajin Zuba zuwa shingen binciken sojoji da ke kusa da Dutsen Zuma.

“Babu nisa daga nan kuma, kana zuwa Gauraka akwai ramuka da dama kowanne da irin girmansa.

“Masu ababen hawa suna kokarin kauce wa ramukan, wadanda yanzu ruwan sama ya sa sun koma tafkuna.

“Daga nan babu nisa, kana zuwa barikin sojoji na Zuma za ka hau bangaren farko da aka kammala sake ginawa na babbar hanyar.

Masu ababen ha da dama kan kara gudu a wannan bangare saboda kyanta.

“Bangaren da aka sake ginawa ya kare ne ’yan kilomitoci kafin zuwa mahadar Diko a jihar Neja.

“Wannan bangare na daga cikin wuraren da ke firgita direbobin manyan motoci saboda wuraren juyawa guda biyun da ke nan suna da muni sosai, ga kuma manyan ramuka da ke kan hanyar, wadanda ke cike da ruwa.

“Sakamakon haka ne muka samu wasu manyan motoci biyu da suka lalace a kan hanyar. Daya duk kayan da ta dauko sun zube a kasa yayin da dayar kuma ta lalace”, in ji su.

Da muka gangara zuwa garin Tafa da ke karamar hukumar Tafa ta jihar Neja, ’yan jaridarmu sun gano cewa nan ma a akwai ramuka da ruwa kwance a cikinsu.

“Amma a dayan bangaren hanyar, wanda ke jihar Kaduna, hanyar da aka sake ginawa ce, har zuwa ’yan kilomitoci kafin a karasa garin Maraban Isa.

“A kan hanyar a garin akwai wurin aron hannun ababen hawa da ke da wani katon ramin, wanda ruwa ya ciki shi.

“Wurin aron hannun ababen hawan da aka yi ya nuna cewa a baya kamfanin yana aiki a wani bangare a wurin, don haka ya tilasta wa motocin yin aron hannu a wurin,” in ji su.

Wakilan namu suka ce irin wannan yanayi ne a hayar ta bangaren garin Jere da ke Karamar Hukumar Jere ta jihar Kaduna, inda masu ababen hawa ke tuki a hankali yayin domin wuce wadannan ramuka.

Irin wadannan ramuka daban-daban sun mamaye hanyar ta Rijana, lamarin da ya tilasta wa direbobi yin aron hannun zuwa Kaduna, duk da cewa ba a gyare take ba.

“Amma idan aka wuce Rijana har zuwa Olam sabuwar hanyar ce da aka kammala,” inda ‘yan jaridarmu suka dakatar tsaya.

Babu ma’aikatan Julius Berger

Duk da cewa ba a ga ma’aikatan Julius Berger ko kayan aikinsu a tsawon wannan tafiya ba, amma mun ga ana aki a cibiyar kamfanin ​​da ke Rijana, inda muka ga manyan motocin suna daukan kaya a kan hanyar.

Daga baya da muka bincika sai muka gano cewa kamfanin yana aiki ne a Gonin-Gora, mai nisan kilomitoci kalilan daga garin Kaduna.

Mazauna da matafiya

A wurin juyawar motocin da aka yi a Maraban Isa, Abdulhadi Saleh, daya daga cikin masu sayar da kayan sha ga matafiya da matafiya ya ce: “Tun da yake wurin kasuwancinmu ne, mukan yi amfani da duwatsu wajen cike ramuka don bai wa direbobi damar shiga inda za su.

“Yawancin lokaci ana samun hadurra kuma tirelolin kan yi karo a lokacin da suke kokarin juyawa ko kauce wa manyan ramuka.

“Wasu motoci kuma a nan suke lalacewa wanda hakan ke haifar da cunkoson ababen hawa,” in ji shi.

“Kwanan nan, kwantenan da ke kan wata babbar mota ya fado kan wata mota kuma mutane biyu sun rasa rayukansu a sanadiyyar wannan lamarin.

“Wurin yana da muni sosai a lokacin damina. Wasu daga cikin direbobin ma ba sa bi a nan. Suna guje wa hakan ne ta hanyar bin daya gefen hanyar da ita ma ake aikin gyara ta kafin a tare ta da kankare,” in ji Abdulhadi.

A cewarsa, kamfanin da ke da aikin ya dade da barin wurin.

“ Sama da watanni biyar ke nan da ganin su na karshe. Motocin aikinsu sun koma farfajiyar gidansu. Sai dai abin da suke yi a yanzu shi ne jami’an tsaronsu su zo su kunna janareta don karkatar da hasken wutar lantarki da daddare domin mutane su sani cewa wurin aron hannu ne,” inji shi.

Yayin da yake kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo dauki kan lamarin “domin titin na da cunkoso”, ya ce idan aka gyara hanyar yadda ya kamata, hakan zai rage hadurra.

Har ila yau, Aliyu Abubakar, wanda aka ga yana gyaran hanyar da ta bi ta Jere, ya ce shi da abokansa suna yin wannan aikin ne domin ceton rayuka.

“Muna gyara ne domin rage yawan hadurran da wadannan motoci, musamman tireloli ke yi.

“Wasu direbobi suna ba mu kudi saboda muna cike ramuka da duwatsu.

“Mukan shiga daji mu dauko duwatsun, sai mu samu abin hawa da za mu kawo shi inda muke gyara hanya don rage yawan hadurruran,” in ji shi.

 Da aka tambaye shi ko yana da adadin hadurran da suka faru a kan hanyar, sai ya ce: “Ba ni da ainihin adadin, amma kwantena, kananan motoci da tireloli suna faɗuwa sosai a nan, kuma suna haifar da cunkoson ababen hawa.”

“Motata za ta ci N2m kafin ta gyaru”

Mun samu motar Ibrahim Ladan kwance a gefen hanyar a kusada da ramuka da ke mahadar Diko, inda ta tare wasu motocin da ke bukatar shiga hanyar domin komawa kan hanyar zuwa Kaduna.

Ladan ya ce motar da ke jigilar katako tana kan hanyar zuwa Kaduna ne a lokacin da ta kife sakamakon wani hadarin da ya faru kwanaki biyu da suka gabata.

“Hatsarin ya kai ga rufe wani bangare na hanyar yayin da jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ke ba ni hannu kan inda zan bi, amma da na isa kan titin, sai motata ta kife da dukkan kayayyakin da na dauko tare sauka daga hanyar,” in ji shi.

“Alhamdu lillahi, kayan ba masu rauni ba ne don haka muka kwashe su; amma man fetur dina ya zube gaba daya. Zan bukaci akalla Naira miliyan biyu don gyara motar,” in ji shi.

Shi ma wani direba mai suna Abdullahi Yusuf, ya ce kwatsam babbar motarsa ta makale a kusa da  ta Ladan bayan ta yi irin wannan juyi, lamarin da ya shafi axle din bayan motar.

“Wannan Diko junction U-turn ya yi muni sosai kuma yana haifar da matsala ga direbobi masu amfani da wannan hanyar. Wannan shi ne karo na biyu da yake lalata axle din motata.

“Hanyar tana da wuraren jujjuyawa da ramuka masu zurfi waɗanda idan motarka ta shiga wasu daga cikinsu, za ta iya karye ko cire sifirin.”

Ya yi kira ga gwamnati da ta gyara hanyar, yana mai cewa: “Ku kalli yadda wannan tirelar ta fadi yayin da take kokarin juyowa saboda rashin kyawun titin. Abin tausayi ne,” in ji shi.

Ba za a ƙara jinkiri ba —Minista

Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da ’yan kwangila a Abuja a ranar Juma’a 12 ga Yuli, 2024, kwana guda bayan mun bi wannan titin, Ministan Ayyuka, Umahi ya ce nan da watanni 12 za a kammala aikin.

“Babu jinkiri; mun ware kudin kuma za mu yi aikin a kammala nan da watanni 12.

“Wasu daga cikinsu wadanda aka ba ayyukan hanyoyin za su kammala kafin watanni 12,” inji shi.

Ya ce kamfanin Dangote ke da alhakin gudanar da kashi na farko na hanyar a karkashin tsarin karbar haraji kuma kamfanin ya ba da aikin ne ga kamfanin Hitech Construction.

A cewar Umahi, sauran kason da za a gina shi ne kilomita 120.

A watan Janairu da Ministan ya danganta jinkirin kammala aikin da karancin kudi.

An sha canza lokacin kammala aikin

A ranar Juma’a 7 ga Yuli, 2023, Babban Sakataren ma’aikatar ayyuka ta tarayya ya yi rangadin rubu’in farko na aikin. Ya danganta jinkirin kammalawar da “rashin tsaro da kalubalen kudade”.

Tsohon Ministan Ayyuka, Babatunde Raji Fashola, ya ce za a gudanar da aikin ne a matakai, kashi na farko shi ne sashin Kaduna zuwa Zariya mai tsawon kilomita 74, wanda ake sa ran kammala shi nan da kwata na hudu na shekarar 2022.

Fashola ya ce kashi na biyu wanda shi ne sashin Zariya-Kano mai tsawon kilomita 137, za a kammala shi ne a rubu’in farko na shekarar 2023; yayin da kashi na karshe, bangaren Abuja-Kaduna, ya kamata a kammala shi a watanni shidan farkon shekarar 2023.