Yadda aka kashe Farfesa a gaban ’yan sanda da sunan Boko Haram
A ranar Asabar din da ta gabata ne wadansu mutane da ba a san ko su waye ba a garin Kibiya ta Jihar Kano suka kashe Darektan Cibiyar Binciken Aikin Gona (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Ahmad Falaki tare da raunata kaninsa a gaban ‘yan sanda a bisa zargin cewa ‘yan […]

A ranar Asabar din da ta gabata ne wadansu mutane da ba a san ko su waye ba a garin Kibiya ta Jihar Kano suka kashe Darektan Cibiyar Binciken Aikin Gona (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Ahmad Falaki tare da raunata kaninsa a gaban ‘yan sanda a bisa zargin cewa ‘yan Boko Haram ne,kasancewar ba a dauki tsawon lokaci ba da wadansu ‘yan bindiga suka kai hari kan ofishin ‘yan sanda na garin.
A lokacin da abin ya faru Farfesa Ahmad Falaki yana tare da dan uwansa mai suna Abbas Mustapha da kuma direbansa mai suna Lawal Ahmad. Rahotanni sun bayyana cewa da misalin karfe 4:30 na yamma ne wadansu ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zato ‘yan kungiyar nan ne ta Boko Haram
suka kai hari a ofishin ‘yan sanda na garin Kibiya, lamarin da ya jawo aka yi musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da kuma ‘yan bindigan, har a karshe ‘yan bindigan suka gudu. A lokacin da suka gudu a kan baburansu ne suka ci karo da marigayi Farfesa a gefen hanya suna kokarin gyaran tayar motarsu, a nan ne suka karbe motar suka gudu da ita.
Bayan ‘yan bindigan sun tafi da motar Farfesan ne sai shi da wadanda suke tare suka nufo cikin gari don neman motar da za ta kai su cikin Kano. Daga nan ne kuma dandazon matasan garin suka yi kan tawagar Farfesan da sara da duka har said a suka kashe shi.
Aminiya ta zanta da dan uwan marigayi Farfesa wanda kuma suna tare a lokacin da aka kashe Farfesan, mai suna Abbas Mustapha, ya bayyana cewa,sun samu matsalar taya ce a kan hanyarsu ta dawowa daga wani gari mai sunaYada-Gungume a kasar Ningi da ke Jihar Bauchi. “Muna kan hanyarmu ta dawowa daga wani gari a Ningi ta Jihar Bauchi sai tayarmu ta lalace a wani gari mai suna Fala da ke karamar Hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano, sai ga wadansu ‘yan bindiga a kan baburansu suka same mu suka nemi mu ba su mabudin motar Farfesa kirar Toyota Hilud. A take ba tare da musu ba Farfesa ya umarci direbnasa da ya ba s u mabudin, inda suka shige motar suka ba ta wuta.”
Abbas wanda a halin yanzu yake jinyar raunikan da ya samu a lokacin wanann arangamar, ya bayyana cewa ‘yan bindigar ba su yi musu ko kwarzane ba, kasancewar ba a samu jayayya a tsakaninsu ba. Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da ‘yan bindigan suka tafi sai Farfesan ya umarce mu da mu taka da kafarmu zuwa cikin gari don mu samu motar da za ta mayar da mu Kano. Lokacin da muka shiga cikin kauyen sai mutanen garin suka fara zarginmu, kasancewar wadansu daga cikinsu sun ganmu a lokacin da muke gyaran tayar motarmu a bayan garin. A nan dai muka yi musu bayanin cewa wadansu ‘yan bindiga sun kwace mana motar. Sai Farfesan ya nemi su taimaka mana mu samu wata motar da za ta kai mu Kano, kasancewar dare ya fara, don har karfe 6:00 ta yi. A daidai wanann lokaci ne sai ga ‘yan sanda sun zo daga Kibiya. Ana cikin haka kuma sai ga dandazon ‘yan kauyen suka bullo, daga nan suka fara dukanmu. Nan da nan sai Farfesa ya nuna wa ‘yan sandan katin shaidarsa na aiki inda ya nemi da su hana ‘yan kauyen dukanmu, amma ‘yan sandan ba su yi hakan ba. A nan suka ci gaba da dukan Farfesa tare da kai masa sara da adda da kuma yankarsa da wuka. Ganin hakan ya sa na gudu cikin daji, inda kuma wani dan sanda ya bi ni da harbi, sai dai bai same ni ba saboda kwanciya da ni. Nan da nan ‘yan kauyen suka yi yo kaina da duka da sara da yanka a fuskata da kuma sauran sassan jikina.” Inji shi
Malam Abbas ya kara cewa, daga nan sai ‘yan kauyen suka zuba su a cikin motar ‘yan sanda suka kai su can ofishin ‘yan sandan, inda su kuma sauran ‘yan sanda suka rika murnar cewa sun kashe ‘yan Boko Haram.
“Muna wannan wuri ne aka kawo direban Farfesa wanda ya gudu. A lokacin da wadansu ‘yan sandan suka zo daga Kano sai suka yi mana tambayoyi, inda muka bayyana musu cewa mu ba ‘yan Boko Haram ba ne, kuma mutumin da suka kashe Farfesa ne a Jami’ar Ahmadu Bello.’ Inji shi.
Marigayi Farfesa Ahmad Falaki dai ya rasu ya bar matan aure uku da kuma ‘ya’ya 18. Wadanda mafi yawansu ke zaune a Zariya. Tun a ranar Lahadi da yamma aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
ASP Magaji Musa Majiya shi ne kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunarsu ta gano cewa su ‘’Farfesan ba ‘yan Boko Haram ba ne, motarsu ce ‘yan bindigan da aka rarako suka kwace suka tafi da ita. Mun kuma gano cewa matasan kauye ne suka kashe Farfesa, amma ba mutanenmu ba, saboda mu aikinmu shi ne mu kare rayukan talakawa ba kisa ba. Amma duk da haka za mu ci gaba da binciken don gano ko akwai sakacin mutanenmu a faruwar lamarin ko babu.” Inji Majiya.
Shi ma Dagacin garin Fala Malam Muhamamd Zangina ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce matasan kauyen ne suka kashe Farfesan a gaban ‘yan sanda.
Ya yi magana da ni mintoci kadan kafin a kashe shi -Matar Farfesa
Hajiya Asabe (Rukayya) Aliyu Bulama daya ce daga cikin mata ukun da marigayi Farfesa Ahmad Falaki ya rasu ya bari, ta bayyana wa Aminiya yadda labarin rasuwar maigidan nata ya riske ta, inda ta ce, “Tun safe muka yi sallama a kan cewa zai je ya duba wata gona a wani gari a Ningi. Lokacin da suka isa wurin ma sai da ya bugo m in waya ya sanar da ni. Haka lokacin da suka gama za su juyo gida sai da muka yi magana a waya misalin karfe 5:00 na yamma. Da wajen misalin karfe 6: 00 na yamma kuma sai ya yi min waya ya ce wadansu ‘yan bindiga sun kwace musu mota amma za su shiga cikin kauyen su nemi motar haya, a nan muka rabu tare da addu’ar Allah Ya kiyaye musu hanya. A lokacin sai da ya rarrashe ni da cewa kada na damu babu wani abu da zai faru kuma kada na gaya wa kowa halin da yake ciki, amma ni saboda gigita ban iya yin shiru ba sai da na shiga gidan yayarsa wacce muke kusa na gaya mata. “ Inji ta.
Hjaiya Asabe, wacce malama ce a Kwalejin Ilimi Ta Sa’adatu Rimi, ta kara da cewa, “Daga nan ban sake ji ya kira ni ba, don haka sai na kira shi, amma sai ga shi wayar tana ta burari babu amsa a bangarensa, wanda kuma hakan bakon abu ne a wajen sa, ga al’adarsa ko a cikin taro yake idan
na yi masa waya yakan amsa sanann ya yi bayanin halin nda yake ciki tare da alkawarin kira bayan ya gama abin da yake yi. Amma a wanann karon sai na ji shiru. Hakan ya tayar da hankalina na kasa barci. Zan iya cewa yadda na ga rana haka na ga daren nan. A daddadefe dai gari ya waye. Da safe wajen misalin karfe 6:00 sai aka sanar da mu cewa wai an kai wata gawa a Asibitin Murtala. Nan da nan muka nufi dakin ajiye gawarwakin an Asibitin Murtala inda ana bude mana gawar muka tarar ta Farfesa ce. Bayan an yi abin da za a yi sanann aka ba mu gawar wajen misalin karfe 3 :00 na yamma.” Inji ta.
A cewarta, kamar yadda al’adar maigidan nata take, duk inda zai tafi yakan tafi tare da ita, amma a wannan karon da ya nemi hakan sai ta ba shi hakuiri da cewa ba za ta samu zuwa ba, sakamakon aikin makaranta, kasancewar tana da aiki na sa hannun takardun jarrabawar dalibai.
Da take bayani game da halin marigayin, Hajiya Asabe ta bayyana cewa mutum ne mai kyawun hali, wanda samun irinsa cikin mazaje sai an tona. “Babu shakka mun yi rashin jajirtaccen maigida, kasancewar shi mutum ne mai kula da iyali. Bawan Allah nan ya bauta wa iyalinsa kwarai da
gaske. A kullum a shirye yake ya warware wa iyalinsa matsalar da take damunsu. Babu abin da za mu yi masa sai addu’ar Allah Ya ji kansa da rahama.”
Cibiyarmu ta yi babban rashi -Farfesa Daniel
Daga Aliyu Babankarfi a Zariya
Aminiya ta ziyarci cibiyar binciken aikin gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke shika Zariya, inda ta ji ta bakin Mataimakin Daraktan Cibiyar Farfesa Daniel A. Aba game da marigayin, inda ya ce, “to da farko dai marigayi mutum ne wanda yake mun dade tare, tun muna karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya muke abota da shi, ya bar ni ya dawo Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar, bayan nan a shekarar 1981 ni ma na same shi a wannan cibiyar muka cigaba da aiki tare kafin a tura shi zuwa cibiyarmu dake Kano. Saboda kwarewarsa da kwazo sai ‘yan Sasakawa suka dauke shi domin ya taimaka musu, bayan ya kammala sai ya dawo Zariya inda aka ba shi Daraktan cibiyar a shekarar 2012 ni kuma ina mataimakinsa.’’
‘’Wani abun sha’awa da marigayi shi ne yadda yake gudanar da al’amuransa da ma’aikata manya da kanana, duk da ina mataimakinsa amman idan ya zo ofis dina saboda yana bakano mu kuma muna zage-zagi idan ya fara wasa da masinjana haka zai ta yi har ya shigo ofis dina mu yi ta wasa da dariya har sai ya fita.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’ A ranar da muka yi sallama da shi ni ina gabatar da kasida a wajen wani taro, mun rabu da shi ya tafi cikin wasa da dariya. A ranar lahadi na tafi coci sai ga matana da direbana suka ba ni labarin ai ga abun da ya faru cewa amininka Farfesa Falaki ya rasu, to a nan fa hankalina ya tashi sai na koma gida muka tattaru gaba daya muka wuce zuwa Kano domin jana’izarsa.’’
‘’Gaskiya na shiga halin damuwa kwarai da gaske, domin marigayi Falaki mutumin kirki ne kuma mai haba-haba da jama’a, kuma kwararre ne a fannin aikinsa, don haka a gaskiya mun yi rashi kuma a halin yanzu muna cikin damuwa kwarai da gaske.’’