Yadda aka kashe Janar Alkali a Jos – Mai bayar da shaida a kotu
An dai kashe marigayin ne a kauyen Dura-Du da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu
Manjo Janar Umar Ibrahim Muhammed (mai ritaya), wanda aka dora wa alhakin gudanar da bincike kan kisan marigayi Janar Idris Alkali a shekara ta 2018, ya bayyana yadda aka kashe marigayin a Jihar Filato.
An dai kashe marigayin ne a kauyen Dura-Du da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a wancan lokacin.
- ’Yan bindiga sun kashe limami sun sace uwa da ’ya’yanta a Kaduna
- Jarumin fin din ‘The Transporter’ ya bayyana goyon bayansa ga Falasdinawa
Janar Muhammed ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a gaban Babbar Kotun Jos ranar Laraba, a matsayin babban mai bayar da shaida a binciken.
Ya ce an yi wa Janar Alkali kisan gilla ne sannan aka daddatsa gawar shi, kafin daga bisani a birne gawarsa a cikin wani dan karamin kabari.
Shaidar ya kuma ce, “Marigayi Janar Alkali ya bar Abuja ne da nufin zuwa Bauchi a shekara ta 2018, yayin da yake kan tafiya sai ya yi kiran wayar shi na karshe a kauyen Dura-Du da ke Jos ta Kudu. Daga nan ne wayar tasa ta dauke ba a sake jin duriyarsa ba.
“Bai je Bauchin ba a lokacin, kuma ba a sake jin shi ba. Bayan kwana uku, sai iyalansa suka bayyana cewa ya bace, a ranar uku ga watan Satumban 2018 ke nan.
“A lokacin ni ne Kwamandan runduna ta uku ta sojin kasa na Najeriya, kuma ni aka dora wa alhakin yin bincike kan kisan na shi. Abu uku aka dora min alhakin ganowa; na farko ko yana raye ko kuma ya mutu, mu nemo motarsa kirar Toyota baka mai lamba MUN 679 AA, sannan mu gano wanda yake da alhakin batan nasa.
“An hada ni da wani Manjo Janar da wasu sojoji 30 domin gudanar da binciken. Mun bincika dukkan asibitoci da ofisoshin ’yan sanda, amma babu labari. Mun je kamfanin sadarwa na MTN, inda muka gano wayarsa an kashe ta ne a kauyen Dura-Du. Ta yadda muka zurfafa bincikenmu ke nan a kauyen.
“Sai da muka bincika wasu kududdufan hakar ma’adinai kimanin guda 32, amma daga bisani muka mayar da hankali a kan wani guda daya. Daga bisani matasan garin suka debo mata kusan 500 suka yi zanga-zangar neman hana mu aikin, amma duk da haka ba mu karaya ba, mka ci gaba.
Mun kai kusan mako biyu muna kwarfe ruwa, kafin daga bisani mu gano motar Janar Alkali a ranar 29 ga watan Satumban 2018 a cikin kududdufin, sannan a cikin motar muka gano kakinsa mai dauke da sunansa da hularsa da takalmi da hula.
“A haka muka ci gaba da bincike a kududdufin, sai a ranar daya ga watan Okotar shekarar muka gano wata motar bas, wacce aka bayyana batan direbanta kimanin shekara bakwai da suka gabata. Mun kuma gano wata mota ja kirar Rover da wata motar kirar a-kori-kura da babura masu kafa uku da masu kafa biyu da dama.
“Daga nan ne muka ci gaba da bincike domin gano gawar, inda wani da ake zargi ya amsa cewa bayan sun kashe shi, sun zagaya da gawarsa a kauyen suna jan ta a kasa, kafin su je su birne ta a wani waje da ake kira da “No man’s land” sannan aka birne shi a wani rami.
“Da bisani bayan dauko wani kwararren kare daga Abuja, mun gano cewa an riga an dauke gawar daga wajen zuwa wani kauye mai suna Buchwet mai nisan kimanin kilomita 10 daga Dura-Du, mun gano gawar ce ranar 30 ga watan Oktoban 2018.
“Binciken kwararru ya gano cewa makasan sun daddatsa gawar Janar Alkali ne, a haka muka ci gaba da bincike da hadin gwiwar iyalansa, har muka tabbatar da cewar gawar tasa ce.
“Binciken ya gano cewa an raba kansa gida biyu, sannan aka daddatsa sauran sassan jikin shi, hakan ne ya tabbatar mana cewa kisan gilla aka yi masa,” in ji shaidar.
Shi ma mai bayar da shaida na biyu, Manjo Arashinga Bulus, wanda yanzu haka sojan kasa ne na Najeriya, ya bayyana irin rawar da ya taka wajen binciken, inda ya tabbatar da cewa mutun 21 din da aka kama su ne wadanda ake zargi da aikata kisan na Janar Alkali.
Bayar daukar bayanan masu bayar da shaidar su biyu ne kotun ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa nan da ranar 6 ga watan Nuwamba mai zuwa domin karbar karin shaidun.