Yadda aka kashe matasa 2 aka datse hannuwan na uku a Dakwa

Mako biyu da suka gabata ne wani gungun mahara da ba a tantance su wane ne ba, suka kai hari a wani masaukin baki da ke garin Dakwa da yankunan Abuja da Neja ke takaddama a kansa, inda suka kashe wani matsahi dan banga lokacin da ya kai dauki. Marigayin mai suna Adamu Zakari, dan […]

Yadda aka kashe matasa 2 aka datse hannuwan na uku a Dakwa

Mako biyu da suka gabata ne wani gungun mahara da ba a tantance su wane ne ba, suka kai hari a wani masaukin baki da ke garin Dakwa da yankunan Abuja da Neja ke takaddama a kansa, inda suka kashe wani matsahi dan banga lokacin da ya kai dauki. Marigayin mai suna Adamu Zakari, dan Dagacin Dakwa da ke karkashin masarautar Suleja ne kuma dalibi ne da ke ajin karshe a Jami’ar Abuja.

Wani dan uwan marigayin mai suna Sani Zakari, ya shaida wa wakilinmu cewa wadansu daga cikin wadanda suka kashe dan uwansa sun buya a hanyar zuwa wajen kuma dan uwan nasa na isowa, sai suka hau shi da sara sannan suka farka masa ciki. “Bayan an sanar da ni abin da ya faru da misalin karfe 2:00 na dare, mun garzaya da shi zuwa wani asibiti a garin Madalla sai dai bayan sun ce lamarin ya fi karfinsu sai muka karasa asibitin gwamnati da ke Suleja inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Aminiya ta samu labarin cewa bayan kamar kwana uku da faruwar kisan, sai kuma wadansu matasa da ake danganta harinsu da na ramakon gayya kan wannan kisan, suka auka wa wadansu matasa biyu inda suka kashe daya, na biyun kuma suka bar shi cikin jini, bayan sun datse masa hannuwa da kuma burma cikinsa da wuka.

Aminiya ta zanta da matashin da aka datse wa hannuwa biyu mai suna Husaini Muhammad wanda ke sana’ar kafinta. Ya ce duk da kasancewar shi dan asalin garin ne, ya jima baya wajen kasancewar yana  zama ne a garin Mpape, Abuja inda yake sana’ar kafinta amma sai wata jinya da ya yi, ta sa ya dawo gida Dakwa.

“To a yanzu na samu sauki kuma na fara aikin leburanci a nan. Muna aikin hakar ramin bayan gida ne a wata unguwa a Dakwa da muka yi kwana uku muna yi. To a yinimu na hudu sai muka yanke shawarar kwana a wajen da niyyar fara aikin tun daga bayan Sallar Asubahi, to a daren ne aka auka mana ni da abokin aikina Ibrahim Papa wanda shi sun kashe shi, ni ma suka dauka na mutu ashe kwanana na gaba,” inji shi.

Ya ce “A lokacin da suka iso wajen sun fara ne da harbe-harben bindiga, nan take suka kashe Ibrahim Papa ni kuma suka yanke min hannaye suka cake ni a ciki. Bayan tafiyarsu ne na farfado na samu nasarar mike wa na canja waje, bayan jama’a sun je wajen daga baya sai suka dauke ni, suka kawo ni wannan asibiti.”

Matashin ya ce ya shaida mutum biyu daga cikin wadanda suka auka masa da ya bayyana a matsayin Muhammadu Kwamandan ’yan banga da kuma wani mai suna Nura da suke aikin tare.

Mahaifiyar matashin wadda ke tare da shi a asibitin lokacin da wakilinmu ya ziyarci wajen, ta ce zuwa yanzu hukumar asibitin wanda mai zaman kansa ne, ta yanka musu Naira dubu 250, kuma ba ta san yadda za ta samu kudin ba, “Ina neman dauki,” inji ta.

Babban Jami’in ’Yan sandan Zuba CSP Muhammad Yahaya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun kama matasa biyu masu suna Nura Shu’aibu da kuma Muhammad Ibrahim. Ya ce an mika wadanda ake zargin ga sashin binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunarsu da ke Abuja don ci gaba da bincike a kansu.

Aminiya ta samu labarin cewa wanda aka kashe na farkon da kuma na biyu, jami’an ’yan banga ne da ke aiki a bangarori biyu mabambanta da ya raba garin biyu.