Yadda aka kona ’yan fashi da makami uku kurmus a Kuros Riba

Al’ummar Amana da ke Karamar Hukumar Obanliku a Jihar Kuros Riba sun tarwatsa gungun  wadanda ake zargi ’yan fashi da makami ne da suka addabe su a ranar Litinin, inda suka kama tare da kone uku daga cikinsu. Wani mazaunin kauyen Ogar Edim ya shaida wa Aminiya cewa ’yan fashi sun dame su sai suka […]

Yadda aka kona ’yan fashi da makami uku kurmus a Kuros Riba
Yadda aka kona ’yan fashi da makami uku kurmus a Kuros Riba

Al’ummar Amana da ke Karamar Hukumar Obanliku a Jihar Kuros Riba sun tarwatsa gungun  wadanda ake zargi ’yan fashi da makami ne da suka addabe su a ranar Litinin, inda suka kama tare da kone uku daga cikinsu.

Wani mazaunin kauyen Ogar Edim ya shaida wa Aminiya cewa ’yan fashi sun dame su sai suka tashi tsaye wajen ba al’ummarsu kariya, “Aka yi sa’a gungunsu suka shigo mana, aka yi masu kofar rago aka kama uku adag cikinsu, sauran biyar suka tsere,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, DSP Irene Ugbo, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda  ta ce “Gaskiya ce wannan abu ya faru, sai dai ba mu ji dadin yadda suka dauki doka a hannunsu ba, duk da irin fadakarwa da wayar da kan jama’a da muke yi na a guji daukar doka a hannu.”