Yadda aka nada ni sarautar Wakilin kabilar Zuru mazauna Zazzau

Aminiya ta zanta da Wakilin Zuru mazauna Zazzau, Alhaji Muhammad Usman inda ya bayyana yadda aka zabe shi ya wakilci mutanen kasar Zuru mazauna Zazzau. Ya ce zai yi wahala a samu masarauta da ake bai wa kabilu dama su yi mulki sosai kamar suna kasarsu irin yadda Masarautar Zazzau ke bayarwa: Yaya aka yi […]

Yadda aka nada ni sarautar Wakilin kabilar Zuru mazauna Zazzau

Aminiya ta zanta da Wakilin Zuru mazauna Zazzau, Alhaji Muhammad Usman inda ya bayyana yadda aka zabe shi ya wakilci mutanen kasar Zuru mazauna Zazzau. Ya ce zai yi wahala a samu masarauta da ake bai wa kabilu dama su yi mulki sosai kamar suna kasarsu irin yadda Masarautar Zazzau ke bayarwa:

Yaya aka yi sarautar Wakilin Zuru mazauna Zazzau ta faro0?

A jerin sarakuna da aka yi na mutanen Zuru a kasar Zazzau, ni ne na hudu. Basaraken farko sunansa Alhaji Umar Bako, inda ya fara sarauta a 1964 ya rasu a 1996. Na biyu shi ne Alhaji lbrahim Bawa Ribah, wanda ya kama a 1996 ya yi murabus a 1999, ya koma gida can Zuru. Sai basarake na uku shi ne Alhaji Garba Rambu, wanda ya karbi sarautar a 2000 zuwa 2016 da Allah Ya karbi rayuwarsa ce sai jama’ar Zuru suka zabe ni. A cikin mu uku da muka yi takara na samu kuri’a 93, wanda ya zo na biyu ya samu kuri’a 17 sai na uku ba a magana. To da alkalan zabe suka kai sakamakon zuwa fada, sai Mai martaba Sarkin Zazzau da ’yan majalisarsa suka aminta da sakamakon, sannan Mai girma Iyan Zazzau ya nada ni bisa umarnin Mai martaba Sarkin Zazzau. An yi bikin nadin a ranar Asabar 26 da Nuwamban shekarar 2016, inda aka tara jama’ar Zuru daga sassan kasar nan da shugabanninmu na wasu garuruwa.

Me sarautar Wakilin Zuru ke nufi kasancewar a Zariya kake?

Kasar Zazzau tana da kabilu da dama da suka kafu sosai a kasar. Kowane lungu ka shiga za ka iske kabilu daban-daban. To saboda tsaro da nuna karamci irin na Masarautar Zazzau sai ta umarci kowace kabila ta yi tsari ta bada wakilin da zai wakilce ta a fada, wanda ta hannunsa masrauta za ta rika isar da sako.

Shi kuma zai isar da koken mutanensa ga fada. Wannan wakilci shi ne aiki guda da aka fitar a fada wanda aikin yana karkashin kulawar Mai girma Iyan Zazzau, domin shi ke  da alhakin nada sarakunan kabilu, sannan bisa umarnin masarauta zai ba mu izinin nada wakilanmu na gundumomi kuma shi ne Shugaban Majalisarmu, domin a duk inda za mu yi taro a kasar Zazzau wurinsa muke karbar umarni.

Yaya alakar sarautar da Masarautar Zazzau a can gida Kebbi?

Alakar sarautar tana da karfi sosai saboda ina wakiltar Mai martaba Sarkin Zuru ne a Masarautar Zazzau. Akwai bukukuwan al’ada da ake yi a kasar Zuru duk shekara suna gayyatarmu bisa umarnin Masarautar Zazzau za a ba mu lasisi mu tafi can mu wakilci Masarautar Zazzau, sannan duk nasarar da muka samu kai- tsaye za mu kawow a Masarautar Zazzau, sannan idan Masarautar Zazzau ta shirya Hawan Daushe mukan aika wa Masarautar Zuru cewa za mu yi hawa kuma al’adun mutanen Zuru muke nunawa a wajen hawan. Sannan Mai martaba Sarkin Zuru da Mai martaba Sarkin Zazzau aminan juna ne.

Akwai alaka a tsakanin mutanen Zuru da Zazzau ne?

Kwarai da gaske, duk Arewacin kasar nan zai yi wuya ka samu jihar da mutanen Zuru suka tare da yawa su da iyalansu irin Jihar Kaduna. Hasali ma ina tabbatar maka cewa kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu ya sa har aka kulla auratayya fiye da yadda kake zato. Ni kaina Wakilin Zuru na Zazzau, Katsinawa mazauna kasar Zazzau wato bayinmu uku na ’yantar na aura, sai ta hudu kuma na auro musu uwargidarsu ’yar Zuru.

Ko kana da wata alaka da Sarkin Zuru?

Mai martaba Sarkin Zuru babana ne. Hasali ma mutumin Dabai ne a kasar Zuru, kuma mahaifina mutumin Dabai ne. Sannan ya yaba da irin yadda nake jagorantar mutanen Zuru mazauna kasar Zazzau sosai.

Ko kana da tarihin asalin zuwan mutanen Zuru kasar Zazzau?

Kwarai kuwa! Mutum na farko da ya iya bada tarihi kafin ya rasu sunansa Dudu, wanda ya zo kasar Zazzau tun 1919. Kuma koda ya zo ya samu mutanen Zuru su uku amma bai bincike su lokacin da suka zo ba.

Sannan yana kasar Zazzau aka kafa Makarantar Horar da Kananan Sojoji (Depot) a 1924. Daga nan ya shiga soja har ya gama aikin soja ya yi ritaya ya dawo garin Chikaji da ke Zariya ya ci gaba da zama. A nan ya rasu a 1970.

Mene ne kiranka ga mutanen Zuru mazauna kasar Zazzau?

Kira da zan yi ga mutanena da ke zaune a kasar Zazzau a zauna lafiya da kowa. Kuma kowa ya kama karatu da sana’a soboda zai yi wahala ka samu masarauta da ake bai wa kabilu dama su gudanar da mulki kamar suna kasarsu babu wulakanta wata kabila babu fifita wata kabila a kan wata kamar Zazzau. Ga girmamamu da ake yi, don haka kulum muke yi wa Mai martaba Sarkin Zazzau addu’ar Allah Ya kara masa lafiya Ya albarkaci zuriyarsa Ya zaunar da mu lafiya.