Yadda aka nada sabon Sarkin Katsinar Maradi a Nijar bayan watanni 18

An zabo Ahmed Ali Zaki Maremawa daga cikin mutum 68 da suka nemi sarautar, aka nada shi a matsayin Sultan na 24

Yadda aka nada sabon Sarkin Katsinar Maradi a Nijar bayan watanni 18

Sabon Sarkin Katsinan Maradin Nijar

An nada Ahmed Ali Zaki  Maremawa a matsayin sabon Sarkin Katsinar Maradi a Jamhuriyar Nijar, bayan an kwashe watannin 18 ana tantancewa.

A ranar Asabar 5 ga watan Nuwamba ne aka nada Mai Martaba Ahmed Ali Zaki Maremawa a matsayin Sultan na 2 na Katsinar Maradi.

An zabo shi ne a cikin mutum 58 da suka nemi sarautar; kai-tsaye kuma aka nada shi don ya gaji mahaifinsa, Marigayi Ali Zaki Maremawa.

Takaitaccen tarihin Masarautar Katsinar Maradi

Masarautar Katsinan Maradi, babbar masarauta ce mai dadadden tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajarta ta tashi daga sarki zuwa Sultan.

Mafi yawancin al’ummar Masarautar Maradi Hausawa ne da kuma wasu kabilu kuma ta kunshi Musulmi da kuma mabiya addinin Kirista.

Sarakuna 23 ne suka yi mulkin Katsinar Maradi kafin yanzu, kuma Dan Kasawa ne ya fara yin sarauta — kuma shi ya fara kafa masarautar.

Marigayi Sarki Buzu ya shekara 57 a kan karagar mulki kuma shi ne wanda ya fi dadewa a tarihin sarautar Katsinan Maradi.

Zamanin Alhaji Ali Zaki ne darajar sarautar Katsinan Maradi ta koma Sultan tun kafa masarautar.

Mahaifin wanda aka nada yanzu, Sultan Maremawa Ali Zaki ya shafe shekara 17 yana mulkin masarautar (2005-2021).

Masarautar Maradi ta yi iyaka da yankin Damagaram daga Gabas da yankin Tawa daga Yamma da yankin Agadez daga Arewa sannan daga Kudu ta yi iyaka da Najeriya, musamman jihohin Katsina da Zamfara da Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara