Yadda aka raba jadawalin neman gurbin shiga gasar Euro 2024

An hada Ingila da Italiya a rukuni daya.

Yadda aka raba jadawalin neman gurbin shiga gasar Euro 2024

Tawagar Italiya wadda ta lashe gasr Euro 2020

An raba jadawalin neman gurbin shiga Euro 2024 da Jamus za ta karbi bakunci, inda aka hada Ingila a rukuni da Italiya – wadda ta doke ta a wasan karshe a Euro 2020 a Wembley.

Ingila da Italiya suna rukuni na uku da ya hada da Ukraine da Arewacin Macedonia da Malta.

Sifaniya tana rukunin farko da ya kunshi Scotland da Norway da Georgia da kuma Cyprus.

Wales wadda take rukuni na hudu za ta kece raini da Croatia da Armenia da Turkiya da kuma Latvia.

Rukuni na takwas kuwa ya hada da Ireland ta Arewa da Denmark da Finland da Slovenia da Kazakhstan da kuma San Marino.

Jamhuriyar Ireland tana rukuni na biyu mai zafi dake dauke da Netherlands da Faransa har da Girka da kuma Gibraltar.

An raba rukuni 10 inda aka yi bakwai dauke da tawagogi biyar – da kuma rukuni uku mai kasashe shida kowanne.

An kuma sa tawaga hudun da suka kai wasan daf da karshe a Nations League a bana cikin rukuni mai dan sauki da suka hada da Croatia da Netherlands da Italiya da kuma Sifaniya.

Dukkan tawagar da ta yi ta daya da ta biyu a kowanne rukuni 10 za su je Euro 2024 kai tsaye da Jamus za ta karbi bakunci.

Jamus ta samu shiga gasar a matakin mai karbar bakunci, za kuma a buga wasan cike gurbi domin zakulo ukun da za a hada da sauran tawagogin.

Za a fara wasannin cikin rukuni daga 23 ga watan Maris, sannan a karkare ranar 21 ga watan Nuwambar 2023.

Yadda aka raba rukunin neman gurbin shiga Euro 2024:

Rukunin farko: Spain, Scotland, Norway, Georgia, Cyprus

Rukuni na biyu: Netherlands, France, Republic of Ireland, Greece, Gibraltar

Rukuni na uku: Italy, England, Ukraine, North Macedonia, Malta

Rukuni na hudu: Croatia, Wales, Armenia, Turkey, Latvia

Rukuni na biyar: Poland, Czech Rep, Albania, Faroe Islands, Moldova

Rukuni na shida: Belgium, Austria, Sweden, Azerbaijan, Estonia

Rukuni na bakwai: Hungary, Serbia, Montenegro, Bulgaria, Lithuania

Rukuni na takwas: Denmark, Finland, Slovenia, Kazakhstan, Northern Ireland, San Marino.

Rukuni na tara: Switzerland. Israel, Romania, Kosovo, Belarus, Andorra

Rukuni na goma: Portugal, Bosnia and Herzegovina, Iceland, Luxembourg, Slovakia, Liechtenstein

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50