Yadda aka saba dokar tazara yayin Sallar Idi a Kano
Yayin da akasarin Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen bukukuwan Karamar Sallah a ranar Lahadi, Aminiya ta gano yawancin masallatan Idi a Kano ba su bi dokar bayar da tazara da amfani da kyallen rufe fuska yadda ya kamata ba. Masana harkar lafiya dai sun dade suna ba da shawarar a […]
Yayin da akasarin Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen bukukuwan Karamar Sallah a ranar Lahadi, Aminiya ta gano yawancin masallatan Idi a Kano ba su bi dokar bayar da tazara da amfani da kyallen rufe fuska yadda ya kamata ba.
Masana harkar lafiya dai sun dade suna ba da shawarar a kaurace wa cunkoson jama’a, tare da tilasta yin amfani da kyallen kare fuska a tsakanin mutane don takaita yaduwar cutar.
Amma binciken da Aminiya ta yi ya nuna kusan dukkan masallatan da suka yi Idi a Kano sun gudanar da sallar ne kamar yadda suka saba yi kafin bullar annobar coronavirus.
A babban filin Idin Kano da ke Kofar Mata alal misali, Aminiya ta gano cewa gwamnan jihar da mataimakinsa, Sarkin Kano da wasu manyan mukarraban gwamnati sun bayar da tazara a tsakaninsu kuma sun yi amfani da kyallen na rufe fuska.
To sai dai akasarin sauran jama’a sun kasance a cunkushe.
Gwamna Abdullahi tare da Sarki Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayin Sallar Idi a Kano ranar Lahadi.
A masallacin Marigayi Isyaka Rabi’u da ke Unguwar Gwauron Dutse ma haka abin yake.
Sai dai Aminiya ta shaida ana zuba wa duk wanda ya sami damar shiga cikin harabar masallacin sinadarin tsaftace hannu na ‘sanitizer’.
A masallacin Jami’ul Ansar da ke Unguwa Uku, da Masallacin Zam-Zam na Hotoro Tsamiyar Boka, da na Malam Karami, da ke Tudun Yola da kuma masallacin Tsohuwar Jami’ar Bayero, dukkansu haka lamarin yake.
Ko da yake wasu jama’ar sun yi amfani da kyallen rufe fuska a radin kansu, amma ba don an ba da umarni ko an tilasta musu yin hakan ba.
A makon jiya ne gwamnatin Kano ta sanar da sassauta dokar kulle a jihar don ba wa mutane damar halartar sallolin Juma’a da Idi.
Hakann zuwa ne bayan shafe sama da makonni biyar ba tare da yin sallar Juma’a a masallatai ba.