Yadda aka sace mai kusunbi a Kano
Wadansu ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da wani matashi mai kusumbi a gidansu da ke unguwar Bachirawa cikin yankin karamar Hukumar Dala a birnin Kano. Aminiya ta gano cewa matashin mai suna Mudashir Abubakar, wanda aka fi sani da Mudan, mai kimanin shekaru 28, yana gudanar da sana’ar sayar da katin wayar hannu ne a […]

Wadansu ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da wani matashi mai kusumbi a gidansu da ke unguwar Bachirawa cikin yankin karamar Hukumar Dala a birnin Kano.
Aminiya ta gano cewa matashin mai suna Mudashir Abubakar, wanda aka fi sani da Mudan, mai kimanin shekaru 28, yana gudanar da sana’ar sayar da katin wayar hannu ne a shagonsa da ke kusa da gidansu.
Rahotanni sun bayyana cewa tun a cikin daren ranar Asabar din makon da ya gabata ne da misalin karfe 3 na dare wadansu mutane da ba a san ko su waye ba suka fada gidan Alhaji Mudashir inda suka dauke shi suka sanya shi a cikin mota suka kuma yi gaba da shi.
Aminiya ta ga yadda dimin jama’ar unguwar ke tururuwa zuwa gidan su Alhaji Mudashir don yi wa iyalansa da suka hada da mahaifiyarsa da kuma ‘yan uwansa jajen sace shi da aka yi.
Abdullahi Abubakar yaya ne ga Mudan, ya bayyana wa Aminiya cewa suna tare a daki daya da dan uwansa nasa a yayin da ‘yan bindigar suka dauke shi. “Muna tsaka da barci a dakinmu ni da kanina Mudan sai na rika jin motsin da ban saba ji ba. Da na kasa kunne sai na ji ana magana kasa-kasa a dakin daya kanin nawa mai suna Yakubu. Hakan ya sa na tashi na leka ta tagar dakinmu sai na ga wadansu mutane sun shiga dakin mahaifiyarmu. Hakan ya san na yi saurin komawa kan shimfidata na
kwanta ina ta addu’a. Can sai na ji an danno kofar dakinmu, sai ga wadansu mutane biyu sun shigo. Ina daga idona sai daya daga cikinsu ya sa mini bindiga tare da barazanar cewa za su kashe ni idan har na yi ihu. Hakan ya sa Mudan ya farka a gigice yana tambaya ta wai su waye? Nan da nan sai daya daga cikin mutanen ya fice daga dakin, inda dayan ya ci gab da tsare mu da bindiga. Jim kadan sai na ji karar mota ta tsaya a kofar gidanmu. Daga nan sai wancan mutumin ya dawo tare da wani,n kasancewar kanin nawa gurgu ne, sai su wadannan mutuane biyun suka ciccibe shi suka fita da shi suka jefa shi cikin mota. Duk abin nan da ake yi dayan mutumin yana tsaye a kaina da bindiga. Sai da ya tabbatar sun gama sanya kanin nawa a mota sannan sai ya kyale ni ya kuma rufa musu baya ya yi waje. “ inji shi.
Malam Abdullahi ya kara da cewa, “Bayan na ji tashin motarsu ne sai muka fito kofar gida ni da dan uwana Yakubu amam ba mu ga kowa ba. Daga nan muka karaso har kasan layinmu muka tambayi wadansu mutane ko sun ga wata mota suka ce ba su gani ba. Hakan ya tabbatar mana cewa ta lunguna suka bi suka fita. Daga nan muka je ofishin ‘yan sanda muka kai rahoto. A nan ‘yan sandan suka biyo mu muka zo gida suka gudanar da bincikensu sannan suka tafi. Washegari ma ‘yan sandan sun dawo suka sake yi mana tambayoyi.” Inji Abdulalhi.
Abdullahi ya bayyana cewa, ‘yan bindigan ba su dauki katunan wayar da Mudan din yake sayarwa ba, haka kuma ba su dauki ko kwabo daga cikin kudin cinikin da ya yi a daren ranar ba, sai dai wayoyin hannu na mutanen gidan da suka karba suka tafi da su.
Hajiya Bilki Abubakar ita ce mahaifiyar Mudan, ta bayyana yadda labarin sace dan nata ya iske ta, kasancewar a lokacin ta tafi Jihar Sakkwato don ta’aziyyar mijin kanwarta. “Muna Sakkwato a lokacin da asubar fari sai wata ‘yar kanina da muka yi tafiyar tare da ita ta zo ta same ni har ta kira sunan sai ta yi shiru, sai na ce mata lafiya? sai ta ce ai babu lafiya a Kano. Na yi na yi ta gaya mini abin da ke faruwa, sai can ta ce wai wadansu mutane ne suka je gida suka dauke Mudan. Ni dai ba abin da na iya fadi sai salati kawai nake yi. A haka muka shirya muka taho Kano a wannan rana. Muna isowa muka zo muka iske gida jingim da mutane, kai ka ce rasuwa aka yi. Hankalina bai kara tashi ba sai da na shiga dakin su Mudan din na ga babu shi, sai dan kekensa na guragu.”
Hajiya Bilki wadda ta yi wannan bayyanin tana cikin kuka, saboda juyayin rashin sanin halin da dan nata ke ciki. Ta nemi jama’a da su taya ta addu’ar Allah Ya bayyana mata dan nata da ransa da kuma lafiyarsa.
Yawancin makabtan gidansu Mudan da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana shi da cewa mutum ne mai son jama’a ga shi kuma da iya mu’amala da mutane.
Binciken Aminiya ya gano cewa, a ranar da al’amarin zai faru an ga wadansu bakin fuska maza biyu suna shawagi a kusa da gidansu Mudan din, inda kuma anan ne yake gudanar da sana’arsa.
Haka kuma jama’a da dama na ganin cewa an sace Mudan din ne don a yi tsafi da shi, sakamakon gabatowar zabe.
ASP Magaji Musa Majiya shi ne Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, ya tababtar da faruwar lkmarin, inda ya ce duk da cew ba su san dalilin sace ,mai kusunbin ba, amma suna nan suna gudanar da bincike tare da bin hanyoyin ganin an kubutar da shi.