Yadda aka sace sandar majalisa a gaban masu gadinta 250

Wata majiya ta ce akwai kimanin jami’an tsaro 250 da ke bakin aiki a majalisar dokokin jiya yayin da ’yan daba biyar da ba gano su ba suka kutsa kai cikin zauren majalisar dattawa yayin da suke zama suka sace sandar majalisar kuma suka gudu da ita.   Wasu majiyoyi wadanda suka hada da manyan […]

Yadda aka sace sandar majalisa a gaban masu gadinta 250

Wata majiya ta ce akwai kimanin jami’an tsaro 250 da ke bakin aiki a majalisar dokokin jiya yayin da ’yan daba biyar da ba gano su ba suka kutsa kai cikin zauren majalisar dattawa yayin da suke zama suka sace sandar majalisar kuma suka gudu da ita.
 
Wasu majiyoyi wadanda suka hada da manyan jami’an tsaro da ma’aikatan majalisar jiya da dare sun tabbatarwa Aminiya cewa akwai kimanin jami’an tsaro 500 da ke aiki a majalisar dokokin inda rabin wannan adadi suna bakin aiki a ranar da lamarin ya auku.
 
A cikinsu akwai jami’an ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da kuma jami’an da ke kare sandar.
 
Aminiya ta ruwaito cewa akwai ’yan sanda 100 da ke aiki da ofishin ’yan sandan da ke cikin  harabar majalisar dokokin, akwai kuma dogarawa 300 da ke bayar da tsaro a cikin majalisar, sannan kuma akwai kimanin jami’an hukumar NSCDC da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya.
’Yan dabar su biyar sun shiga majalisar  ne ta babbar kofar majalisar dokokin da bakar mota kirar kamfanin Renge Rover inda suka gayawa jami’an tsaron wurin cewa suna tare da Sanata Ovie Omo-Agege dan jam’iyyar APC daga jihar Delta wanda ya shiga majalisar tare da su.
 
Sanata Omo-Agege wanda majalisar ta dakatar tun ranar Alhamis din da ta gabata ya shiga zauren majalisar ne da misalin karfe 11 da minti 15 na safe daidai lokacin da ’yan dabar biyar suka shiga zauren majalisar.