Yadda aka sako ’yata bayan biyan Dala dubu 15 a matsayin fansa – Dokta Ardo
Sace wata budurwa ’yar wani jigo a Jam’iyyar PDP, Dokta Umar Ardo a ranar Asabar da ta gabata a Abuja, ya tada hankalin mazauna Birnin Tarayya musamman wadanda ke da zaune ko harka a kwariyar birnin, saboda a baya matsalar tana aukuwa ne a wasu kananan garuruwan da ke wajen birnin. An sako wadda aka […]
Sace wata budurwa ’yar wani jigo a Jam’iyyar PDP, Dokta Umar Ardo a ranar Asabar da ta gabata a Abuja, ya tada hankalin mazauna Birnin Tarayya musamman wadanda ke da zaune ko harka a kwariyar birnin, saboda a baya matsalar tana aukuwa ne a wasu kananan garuruwan da ke wajen birnin.
An sako wadda aka sacen mai suna A’isha Umar Ardo mai shekara 24, washegari Lahadi da misalin karfe 10 na dare, bayan mahaifinta ya biya kudin fansa Dala dubu 15, (kimanin Naira miliyan 5 da doriya).
Aminiya ta samu labarin cewa an sace A’isha ce da misalin karfe 7: 45 na yammacin Asabar lokacin da take fitowa daga wani katafaren kanti mai suna Blinkers a Unguwar Asokoro, Abuja inda gidansu yake. Yankin da ke daya daga cikin unguwannin kasaita a birnin Abuja.
A zantawarsa da Aminiya, mahaifin yarinyar Dokta Umar Ardo wanda ya taba tsayawa takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa, ya ce wadanda suka sace ’yarsa sun fara magana da shi ne washegari Lahadi da misalin karfe 9:56 na safe, inda suka ba shi tabbacin cewa ’yarsa za ta dawo in ya ba su hadin kai. “Sai na ce da su shi ke nan, zan ba ku hadin kai idan kuka ka yi mini alkawura biyu. Na farko ba za ku cutar da ’yata ba, ma’ana ba za ku kashe ta ba. Na biyu kuma ba za ku ci zarafinta ba, ma’ana ba za ku yi mata fyade ba. Idan ba za ku iya wannan alkawari biyu ba, to ku yi duk abin da kuka ga dama da ita. To a nan sai wanda ya yi min wayar ya ce da ni, Dokta kai dattijon kirki ne, kamar yadda ni ma nake mutumin kirki, don haka na yi maka alkawarin wadannan abubuwa biyu.
“Daga nan sai na ce da shi to mai kake son in yi don ’yata ta dawo gare ni. Sai ya ce za ka biya Dala dubu 15.”
Dokta Ardo ya ce daga bisani sun sake yi masa waya misalin karfe 3 a ranar Lahadi inda suka bukaci da ya biya kudin fansar ta hanyar amfani da tsarin biyan kudi ta kwamfuta na bit coin.
“Na ce musu ban san yadda ake biyan kudi ta tsarin ba, amma sai mai wayar ya dage kan lallai sai na koya, sannan ya ce zai turo mini da adireshinsu na tsarin biyan, don in je in yi. Bayan nan sai ya ce yanzu ya rage gare ni, in yi ko kada in yi, sannan kada in manta cewa rayuwar ’yata na kan siradi.
“Sai dai na kara gode wa Allah saboda ina da kudin a asusun ajiyata ta kudin waje, daga nan sai na umarci wani ya aiwatar da biyan, kuma kasa da awa daya sai ga sakon tabbacin shigar kudin, wanda na tura musu don su gani. Bayan nan, na yi ta jiran bayani daga wajensa har zuwa karfe 10 na dare lokacin da kirar waya ta shigo, kuma ina daukar wayar sai na ji ’yata ce. Ta shaida mini cewa tana wani waje mai suna Drumstick a yankin Gwarinpa, kuma nan take na tafi wajen tare da sauran iyali muka daukota,” inji Dokta Ardo.
Daga farkon wannan wata na Satumba an samu rahotanni sace mutum 4 baya ga A’isha a kwaryar Abuja, da suka hada da wani malamin Jami’ar Baze da ke Abuja mai suna Abubakar Alkali, amma ’yan sanda ba su ba da tabbacin aukuwar ragowar ukun ba.
Sauran da a ba da tabbacin aukuwarsu ba duk da labarin aukuwarsu ya yi yawa a kafofin sada zumunta, su ne: sace wata mata mai suna Hannah Azubuike da aka ce ya auku a kusa da wani katafaren kantin sayayya na Habiba Plaza a Unguwar Maitama, sai kuma ta wadansu yara biyu da aka ce ya auku a lokacin da suke dawowa daga makarantar Islamiyya a Unguwar Wuse Zone 6, Abuja.
Binciken Aminiya ya gano cewa daga watan Junairun bana zuwa watan Satumban nan, an sace mutum 34 a wurare daban-daban na Abuja.
Da yake tsokaci kan lamarin wani tsohon Kwamishnan ’Yan sandan Birnin Tarayya, Mista Lawrence Alobi ya bukaci Rundunar ’Yan sandan Abuja ta karfafa aikin sintiri musamman a kwaryar birnin, inda ya ce a rika ganin jami’an tsaro na kai-komo a kan layuka kadai, na karya lagon masu nufin aikata laifi.
Sai dai ya ce ’yan sandan ba su da wadatattun motocin aiki da kuma jami’ai, inda ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya sa hannun a kan dokar kafa Gidauniiyar ’Yan sanda da Majlisar Dokoki ta Kasa da ta gabata ta kafa, don samar musu da kudin gudanar da ayyukansu a wadace.
Haka Mista Alobi ya bukaci mazauna Abuja su kakkafa na’urorin daukar hotuna a wuraren sana’o’i da ke cikin birnin don tallafawa wajen magance laifuffuka kafn aukuwarsu da kuma saukin bincike a kai idan suka auku. Ya ce lokacin da yake Kwamishinan ’Yan sandan birnin, ya rungumi tsarin girke ’yan sanda a wasu zababbun unguwannin Abuja irin su Maitama da Asokoro.
An rika yada jita-jitar an kama wadanda suka sace A’isha a Kano, amma hukumomi sun musanta wannan labari. Kuma sun koka cewa ana azizita batun garkuwa da mutane a birnin.