Yadda aka sayar da jariri sabon haihuwa N2.5m a Legas — ’Yan Sanda
Rundunar ta ce tana bincike domin kamo wanda ya sayi jaririn.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, ta kama wani likita, ungozoma da kuma wasu masoya bisa zargin sayar da jariri sabon kan kuɗi Naira miliyan 2.5.
A cewar majiyoyin ’yan sanda, mahaifiyar jaririn mai shekaru 28 da saurayinta sun yanke shawarar ba za su riƙe jaririn ba, inda suka fara neman waɗanda za su saya tun kafin a haife shi.
- Idan na ci zaɓe zan sasanta da ’yan bindigar da suka shirya ajiye makamai — Obi
- Yaƙi zai sake ɓarkewa idan Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon — Iran
Da farko an kai matar wajen wata ungozoma domin ta haihu.
Sai dai ta samu matsala yayin naƙuda, lamarin da ya sanya aka garzaya da ita wani asibitin kuɗi da ke yankin Ikorodu, inda wani likita ya yi mata tiyata, aka ceto rayuwarta da ta jaririn.
Masu bincike sun ce an kammala yarjejeniyar sayar da jaririn ne a cikin asibitin bayan an haife shi, inda aka miƙa shi ga wanda zai say kan Naira miliyan 2.5.
Asirinsu ya tonu ne bayan da mahaifiyar jaririn ta yi ƙorafin cewa an ba ta Naira 700,000 kacal daga cikin kuɗin da aka amince za a biya.
Daga bisani wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu suka shiga lamarin tare da kai wa ’yan sanda rahoto.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Mista Fatai Tijani, ya bayar da umarnin lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID), inda Sashen Yaƙi da Safarar Bil Adama ke gudanar da bincike.
’Yan sanda sun ce har yanzu ba a samu nasarar cafke wanda ya sayi jaririn ba, saboda adireshinsa da lambar waya da ya bayar duk na bogi ne.
A halin yanzu, likitan, iyayen jaririn da ungozomar na tsare, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Haka kuma jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto jaririn tare da kamo wanda ya saya.