Yadda aka shirya wa Buhari kasaitaccen bikin Hawan Daba a Daura
Ana bikin ne saboda taya shi murnar kammala mulkin shekara takwas lafiya
Garin Daura, mahaifar tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya yi cikar kwari yayin gagarumin bikin Hawan Dabar da aka shirya masa na murnar kammala mulkinsa lafiya.
Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar ne ya shirya bikin ranar Talata don taya shi murnar kammala mulkinsa na shekara takwas lafiya.
- Abba Gida-Gida ya nada shugabannin Hukumar Alhazai
- Gudun yamutsi ne ya hana ni zuwa rantsar da Abba —Ganduje
A ranar Litinin ce Buhari ya koma Daura daga Abuja, bayan ya mika mulki ga sabon Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Bikin dai na samun halarta daga mutane da dama daga sassan masarautar, Jihar Katsina da ma sauran sassan Najeriya.
Buhari dai ya sami halartar wajen inda yake karbar gaisuwa daga Hakimai da sauran jama’a masu yi musu fatan alheri.
Daga cikin masu rike da sarautar, har da dan tsohon Shugaban, Yusuf Buhari, wanda shi ma ya yi shigar sarauta
Kazalika, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da takwaransa na Borno, Babagana Umara Zulum, suna halartar bikin.
Sauran manyan bakin da ke halartar bikin sun hada da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa lokacin mulkin na Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari da tsofaffin Ministocin Kudi da ta Jindadi da Walwalar Jama’a da na Sufuri da na Yada Labarai da kuma Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Adamu.
Buhari dai ya sha nanata cewa bayan kammala wa’adin nasa, zai ci koma mahaifar tasa ta Daura da zama dungurungum.