Yadda aka tsinci gawar yara uku cikin motar maqwabcinsu
A ranar Asabar xin da ta gabata ce mazauna Titin Surajo a Tudun Wada Kaduna suka wayi gari cikin tashin hankali, sakamakon tsintar gawar waxansu yara uku a cikin motar maqwabcinsu bayan kwana uku da vacewarsu. A cewar iyayensu, yaran sun vata ne da misalin qarfe 3:30 na yammacin Laraba, kafin a gano gawarwakinsu a […]

A ranar Asabar xin da ta gabata ce mazauna Titin Surajo a Tudun Wada Kaduna suka wayi gari cikin tashin hankali, sakamakon tsintar gawar waxansu yara uku a cikin motar maqwabcinsu bayan kwana uku da vacewarsu.
A cewar iyayensu, yaran sun vata ne da misalin qarfe 3:30 na yammacin Laraba, kafin a gano gawarwakinsu a cikin motar, lamarin da ya tayar da hankalin jama’ar unguwar.
Yaran su huxu ne suka vace an kuma ba da sunansu kamar haka. A’isha Sulaiman Hashim ’yar shekara uku da rabi da Rabi’atu Aminu Hashim ’yar shekara huxu da rabi da Abubakar Sulaiman Hashim shekara biyu da rabi sai Hamza Aminu Hashim shekara biyu da rabi. Sai dai an fito da Rabi’atu daga cikin motar a raye inda aka kai ta Asibitin Soji na 44, ana yi mata jinya.
Dukan yaran huxu jikokin Alhaji Hashimu Mai’atamfa.
Bayanai daga unguwar ya nuna sai da ’yan sanda suka hana matasa xaukar doka a hannunsu domin sun yi qoqarin qone gidan da aka tsinci yaran. Matasan waxanda suka fusata sun zargi maigidan Alhaji Abdu Musawa wanda dattijo ne kuma sananne a unguwar da kashe yaran, inda hakan ya sa dole ’yan sanda suka tafi da shi domin amsa tambayoyi kan abin da ya sani.
Sulaiman Hashim wanda shi ne mahaifin A’isha da Abubakar Hashim biyu daga cikin yaran da aka tsinci gawarsu a cikin motar ya yi wa Aminiya qarin bayani ta tarho kan abin da ya faru. “Motar da aka tsince su a ciki tana ajiye ne a cikin garejin gidan maqwabcinmu. Kuma wannan abin da ya faru abin baqin ciki ne da firgici. Ranar Laraba da misalin qarfe 6:45 mun tafi masallaci domin bayan mun dawo sai aka rasa inda yaran suka shiga daga nan sai muka fito nemansu baki xaya tare da mahaifiyarmu.”
Ya qara da cewa: “Ita mahaifiyarmu ta shiga cikin gidan har ta haska cikin motar da tocila amma ba ta gansu ba. Sai muka bazama nemansu. Sai misalin qarfe 10:30 muka ga shi (Abdu Musawa) yana dawowa aka faxa masa cewa ba a ga yara ba ne, sai ya ce Allah Ya sa a gansu, muka ce amin. Kullum ana ta addu’a mu kuma dama a nan qofar gida muke zama hira. A ranar Asabar da misalin qarfe 3:30 sai muka gan shi ya fito daga cikin gida a firgice a razane ya ce ku zo ga yaranku. Muna zuwa sai ya nuna mana cikin mota. Ita Rabi’atu ce ta fito da kanta a motar. Muka buxe qofar motar sai muka tarar da gawar sauran yaran. Lokacin da suka vata akwai kaya a jikinsu. Amma sai muka tarar da su tsirara. Muna son a yi mana adalci domin lokacin da muka xauko gawar yaran xanyen gawa ce tunda har da jini a jikinsu.”
Sulaiman ya ce an ba su gawarwakin yaran uku sun kuma yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ya ce baya ga haka kuma an gayyace su ofishin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar a shekaranjiya Laraba inda aka buqaci su rubuta bayaninsu.
Aminiya ba ta samu jin ta bakin wanda aka tsinci gawar yaran a gidansa ba domin a ajiye motar ’yan sanda a qofar gidan saboda hana mutane shiga. Kuma an tabbatar mata cewa har zuwa lokacin rubuta wannan labarin yana hannun ’yan sanda domin amsa tambayoyi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce tuni ’yan sanda suka fara bincike domin gano abin da ya faru.
“Mun gayyaci wanda aka tsinci gawarwakin yaran a gidansa ne domin ya amsa tambayoyi. Muna kuma jiran sakamakon bincike daga asibiti,” inji shi.