Yadda aka yi amfani da asusuna wajen sace Naira miliyan 546 daga NIMASA – Wani Tela
A ci gaba da shari’ar tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa (NIMASA), Mista Patrick Akpolobokemi wani tela mai suna, Chukwuemeka Benjamin Onuoha ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan yadda aka yi amfani da kamfaninsa mai suna, Edtreme bertebed Limited wajen sace Naira miliyan 546 da dubu 800 daga […]

A ci gaba da shari’ar tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa (NIMASA), Mista Patrick Akpolobokemi wani tela mai suna, Chukwuemeka Benjamin Onuoha ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan yadda aka yi amfani da kamfaninsa mai suna, Edtreme bertebed Limited wajen sace Naira miliyan 546 da dubu 800 daga hukumar kan wata kwangila da ba a bashi ba.
Telan, shi ne shaida na biyu da Hukuma Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gabatar kan shugaban na NIMASA da wadansu mutum uku da ake zargi da sace Naira biliyan 2 da miliyan 600 daga hukumar.
Akpolobokemi wanda aka gurfanar a gaban Mai shari’a Ibrahim Buba tare da wadansu mutum uku masu suna Kyaftin Ezekiel Agaba da Ekene Nwakuche da Gobernor Juan da wasu kamfanoni uku da suka hada da Blockz and Stonz Limited da Kenzo Logistics Limited da Al-Kenzo Logistic Limited, wadanda ake tuhuma da aikata laifuffuka 22.
Hukumar EFCC, tana zarginsu da karkatar da jimillar Naira biliyan 2 da miliyan 658 da dubu 957 da 666 mallakar Hukumar NIMASA a tsakanin 23 ga Disamban 2013 zuwa 28 ga watan Mayun bara.
A zaman kotun a ranar Talata, shaidan a karkashin jagorancin lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya shaida wa kotun cewa an tura kudin ne zuwa asusunsa na bankin Zenith Bank duk da cewa bai nemi kwangila ko ya gudanar da ita da hukumar ba.
Onuoha ya shaida wa kotun cewa mutum na uku da ake zargi ne (Ekene Nwakuche) wanda abokin karatunsa na sakandare ne ya tura kudin asusunsa.
Shiadan ya bayar da bayanin dalla-dallar yadda ya karbi kudin inda ya ce a wani lokaci a shekarar 2013 lokacin da wanda ake zargi na uku ya samu aiki da Hukumar NIMASA, shi (Onuoha) ya tuntube shi ya roke shi cewa ya tuna da shi idan akwai wata kwangila da zai iya aiwatarwa. Ya ce, jim kadan bayan ya yi rokon, sai wanda ake zargi na uku ya kira shi a waya ya tambaye shi ko yana da wani kamfani da yake da rajista da za a yi amfani da shi wajen hulda da kuma asusun kamfanin.
Onuoha ya shaida wa kotun cewa bayan lokaci kadan da bayar da bayanin kamfaninsa da asusun ajiyar bankinsa ga wanda ake zargi na uku, sai ya rika samun sanarwar shigar kudi a asusunsa a kai a kai har suka kai Naira miliyan 546 da dubu 800.
Mai shari’a Buba ya dage sauraren shari’ar zuwa ranakun 2 da 5 da 16 da 19 ga Fabrairu mai zuwa.