Sarautar Rano: An yi arangama tsakanin ’yan daba da matasa

Shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar da wakilin Sarkin Kano na 16, sun tsere da ƙafarsu.

Sarautar Rano: An yi arangama tsakanin ’yan daba da matasa

An shiga fargaba a yayin da wasu ’yan daba da mazauna yankin tsohuwar fadar sarkin Rano a a Jihar Kano suka yi arangama.

Rikicin ya haifar da ruɗani, wanda ya sa shugaban rikon ƙwarya na ƙaramar hukumar, Farfesa Dahiru Yakubu Rano, da wakilin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, suka tsere da ƙafarsu.

Wani ganau, Naziru Salisu Mato, ya bayyana cewa ’yan daban sun shafe kwanaki a fadar, inda suke haifar da tashe-tashen hankali a garin.

Mazauna garin ba su ji daɗin zuwa ’yan daban ba, domin sun yi imani cewa fadar na da isasshen tsaron da ta ke buƙata.

Rikicin ya yi tsamari ne lokacin da shugaban riƙon ƙwarya da wakilin Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II suka yi ƙoƙarin shiga fadar.

Mazauna yankin sun yi adawa da matakin ƙoƙari shiga fadar, wanda hakan ya jawo ’yan daban suka fara sara kan mai uwa da wabi.

Duk da haka, mazauna yankin sun yi ƙoƙarin dakatar da ɓata garin, inda suka dinga korar mutanen da ƙoƙarin shiga fadar.

Duk da cewar daga baya komai ya lafa, wasu ɓata-garin sun laɓe a wasu wurare, daga bisani suka kai wa mazaunan yankin hari, lamarin da ya haifar da mummunan yanayi a ƙaramar hukumar.

A yayin rikicin, an lalata motocin mutane da dama, musamman a sakatariyar ƙaramar hukumar.

Mazaunan da ke ƙarƙashin Kungiyar Masu Kishin Masarautar Rano, sun koka kan yadda ’yan daban suka mamaye garin.

Sun aike da wasiƙa ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, kan neman ɗauki daga gungun ɓata garin da ke barazana ga zaman lafiyar a garin.

Mazaunan garin sun jaddada aƙidarsu ta zaman lafiya da bin doka.

Sun ce duk da tashe-tashen hankali da aka samua a garin biyo bayan rushe masarautun Kano da gwamnatin jihar ta yi, hakan bai sa sun ɗauki doka a hannu ba, lamarin da ya sa suka bar wa kotu damar yanke da hukuncin da ya dace.