Hotuna • Created July 20, 2021 17:57
Hotunan yadda aka yi Babbar Sallah a Najeriya
Yadda Babbar Sallah ta kasance a sassan Najeriya.
Ga wasu kayatattun hotunan yadda Babbar Sallah ta kasance a masarautu da wasu sassan Najeriya, duk da cewa hukumomi sun takaita taruwar jama’a tare da soke hawan daba a Arewacin kasar.
A safiyar Talata dubban mutane suka fito kan tituna domin shaida yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tafiya mai tsawo a kafa domin halartar Sallar Idi a mahaifarsa da ke garin Daura a Jihar Katsina. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa). Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero tare da Gwamna Abudullahi Ganduje da manyan jami’an gwamnati sun bi sahun dubban masallata a babban filin idin birnin Kano. (Hoto: Sani Maikatanga). Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila a lokacin da yake yanka dabbar layyarsa bayan saukowa daga masallacin idi. Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq, yana gaisawa da Shugaba Buhari a filin idi, a gefensu, Yusuf Buhari (Talban Daura) ne tare da dan uwansa Musa Daura, Danmadamin Daura. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa). Duk da cewa an dakatar da Hawan Sallah, dubban jama’a sun zagaye Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin yi masa gaisuwar Babbar Sallah. (Hoto: Sani Maikatanga). Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir a Masallacin Idi na Tashar Mota ta Bauchi Road da ke garin Jos, Jihar Filato. (Hoto: Hussaini Isah). Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammadu Musa Dogonkadai a lokacin Sallar Idi a Masallacin Ilesik da ke Ikeja, Jihar Legas. (Hoto: Abbas Dalibi). Dubban al’ummar Musulmi a Masallacin Idi na Tashar Mota ta Bauchi Road da ke garin Jos, Jihar Filato. (Hoto: Hussaini Isah, Jos). Filin Idin Dandalin Murtala da ke garin Kaduna. (Hoto: Nasir El-rufai). Babban Limamin Kano yana jagorantar Sallar Idin Layya a Filin Idi da ke Kofar Mata, daura da titin IBB a ranar Talata. (Hoto: Sani Maikatanga). Al’ummar Musulmi da suka halarci sallar idi a Masallacin Ilesik da ke Ikeja, a Jihar Legas. (Hoto: Abbas Dalibi, Legas). Gaisuwar sallar da masu yi wa kasa hidima suka kai wa Shugaba Buhari a gidansa da ke Daura. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa). Yadda al’ummar Musulmi suka yi wa Masallacin Idi na Ali Kazaure da ke garin Jos tsinke. (Hoto: Hussaini Isa, Jos). Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a cikin masu halartar sallar idi a garin Kaduna. (Hoto: Nasir El-Rufai).