Yadda aka yi fashin banki da tsakar rana

Sun tsare kwastommi da ma’aikata a cikin bankin, suna kuma harbin wadanda ke waje

Yadda aka yi fashin banki da tsakar rana

‘Yan Sanda

’Yan fashi sun kutsa wani banki da tsakar rana, suka yi awon gaba da miliyoyin kudade bayan sun ritsa ma’aikata da kwastomomi a Jihar Delta.

’Yan fasin sun yi dirar mikiya a bankin ne a yayin da ake gudanar da harkoki, inda suka dauki tsawon lokaci suna cin karensu babu babbaka, har suka bindige wani mutum a ranar Talata a garin Issele-Uku.

Ganau sun ce ’yan fashin bankin, sun rarraba junansu ne a wasu muhimman wurare da ke cikin bankin, suka rika bincike da kwasar dukiyoyi tun daga harabar barkin ba tare da wani kalubale ba.

Sun kuma tsare kwastomomi a cikin bankin na tsawon kimanin awa daya, yayin da na wajen kuma suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi babu kakkautawa.

A haka ne suka bindige wani dan tireda dan asalin kauyen Ogbeofu, wasu da dama kuma suka tsallake rijiya da baya da raunin harbi.

Mai magana da yawaun Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin amma yana ganawa da Babban Ofishinsu da ke Issele-Uku domin samun karin wasu bayanai.

Wadanda lamarin ya faru a kan idonsu sun ce, a kusan awa daya da ’yan fashin bankin suka yi barnar, babu ko jami’in dan sanda daya da aka gani ya kawo dauki.

Mazauna sun bayyana mamakin rashin ganin rundunar tsaron hadin gwiwar gwamnatin jihar ta “Operation Delta Hawk”, da ta saba yin sintiri a garin, a lokacin da abin ya faru.

Kimanin shekaru uku da suka gabata, ’yan fashi sun kai kwatankwacin hannan hari a bankin, suka kuma yi awon gaba da miliyon kudade.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna