Yadda aka yi jana’izar Sarkin Ningi

Marigayin shi ne sarki ma mafi daɗewa kan karagar mulki cikin manyan sarakuna guda shida da ake da su a jihar Bauchi.

Yadda aka yi jana’izar Sarkin Ningi

An yi jana’izar marigayi Maimartaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Mohammed Danyaya, a garin Ningi a ranar Lahadi.

Marigayin shi ne sarki ma mafi daɗewa kan karagar mulki cikin manyan sarakuna guda shida da ake da su a jihar Bauchi.

Sarki ne mai daraja ta daya a jihar Bauchi, kuma ya rasu yana da  shekaru 88, inda ya shafe shekaru 46 kan gadon sarauta.

Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da shi a wani asibiti da ke Kano.

An yi sallar jana’izar sarkin wadda Babban Limamin Ningi Dokta Muhammad Umar ya jagoranta ne a fadar Sarkin Ningi, inda ya samu halartar dubban jama’a da suka hada da Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed da tsoffin gwamnoni biyu, Ahmadu Mu’azu da na jihar Jigawa Sule Lamido Sanata Abdul Ningi.

Saura sun hada da sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu, ’yan majalisar jiha da na tarayya da dai sauransu.

Da yake mika ta’aziyyarsa ga daukacin al’ummar Masarautar Ningi da ’yan uwa, Gwamna Bala ya ce marigayin ya yi rayuwa ta sadaukar da kai, kuma ya ba da shawarwari da jagoranci na uba domin zaman lafiya, hadin kai da cigaban jihar.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana marigayi Sarkin a matsayin uba wanda ya nuna mafi girman darajar shugabanci, wajen samar da haɗin kai, cigaba da ci gaba ba kawai a masarautar Ningi da jihar Bauchi ba, har ma da kasa baki daya.

Ya ce, “za a rika tunawa da Mai Martaba a matsayin uba ga kowa da kowa, ginshiki ne mai karfi, kuma fitilar haske a jiharmu.”

Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin ya kuma bai wa iyalai haƙurin jure rashin da ba za a iya cike gurbinsa ba.

Alummar masarautar Ningi sun ce mutuwar tasa ta bar wa al’ummar masarautar Ningi da jihar Bauchi da ma Najeriya baki daya wani gurbi da ba za a iya maye gurbinsa ba.

Sun bayyana Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya a matsayin mutum mai son zaman lafiya, hikima da sadaukar da kai wajen kyautata rayuwar al’ummarsa.

A tsawon mulkinsa, ya nuna misali na mafi girman darajar jagoranci, ya samar da hadin kai, da ci gaba a fadin Masarautar Ningi.

Abin da ya gada a matsayin mai kula da al’ada, al’adu, da kimar Musulunci da ciyar da addini gaba da zaburar da al’umma masu zuwa.

Sun bukaci daukacin al’ummar kasar nan da su yi masa addu’ar Allah Ya gafarta masa, ya sa ya huta.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana