Yadda aka yi jana’izar Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri

Gwamnan Gombe ya yi alkawarin kamawa da kuma hukunta wadanda suka kashe Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri a gidansa a jihar

Yadda aka yi jana’izar Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri

Jana’izar Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri

Dubban al’ummar Musulmi sun halarci sallar jana’izar fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Musa Ibrahim Albani Kuri, wanda ’yan fashi suka kashe a gidansa.

Da azahar din ranar Laraba aka yi jana’izar Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri a Masallacin Juma’a na kungiyar Izala da ke Bolari a garin Gombe.

A lokacin da ya halarci jana’izar, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi alkawarin “kamowa da hukunta wadanda suka yi wannan aika-aika domin ya zama darasi ga masu shirin yin haka a nan gaba.

“Sannan za mu fatattaki masu aikata miyagun laifuka daga duk sassan jihar nan, ” in ji gawmnan wanda ya ce kisan Sheikh Albani Kuri a gidansa ya girgiza bangaren tsaron jihar da a baya take zaune cikin aminci.

A cewarsa, hakan ya nuna muhimmancin gwamnati da al’ummar jihar su kara farga tare da daukar matakan da suka dace game sha’anin tsaro.

A safiyar ranar Sakataren Kungiyar Izala na Kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya sanar da rasuwar Sheikh Albani Kuri a hannun ’yan fashin da suka kutsa gidansa da ke unguwar Tabra a garin Gombe.

A ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ibrahim Musa da kungiyar Izala, gwamnan Inuwa ya bayyana malamin a matsayin kogin ilimi da ke hada kan al’umma ba tare da nuna bambanci ba, “wanda kuma koyarwarsa ta amfani al’ummar Musulumi.”

Rasuwar malamin, a cewarsa, ta samar da gibi mai wuyar cikewa, kuma za a jima ana kewarsa.

A karshe ya lashi takobin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi  jihar, ta hanyar bullo da sabbin dabaru da kuma daukar matakan da suka dace a kan kari.