Yadda aka yi jana’izar Shugaban Chadi, Idriss Deby

Idriss Deby ya rasu a fagen daga, kwanaki kadan bayan ya sake lashe zaben Shugaban Kasa.

Yadda aka yi jana’izar Shugaban Chadi, Idriss Deby

Sojoji sun dauko gawar Idriss Deby wanda rasuwarsa ke haifar da damuwa game da makomar siyasar Chadi. (Hoto: Christophe PETIT TESSON/AFP).

An gudanar da jana’izar tsohon Shugaban Kasar Chadi, Idriss Deby, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a bakin daga.

Rundunar Sojin Chadi ta ce Idriss Deby Itno, wanda ke kan karagar mulki tun shekarar 1990 ya rasu ne ranar 20 ga Afrilu, 2021 sakamakon raunukan harbi da ya samu a yayin gwabza fada da ’yan tawaye a Arewacin kasar.

Rasuwar Idriss Deby, wanda jigo ne a yaki da masu tayar da kayar baya, ta haifar da damuwa game da yanayin tsaro a yankin Sahel.

Jami’an sojin Chadi suna jiran fara bikin jana’izar marigayi Shugaba Idriss Deby a birnin N’Djamena ranar Juma’a 23 ga Afrilu, 2021. (Hoto: Christophe PETIT TESSON/AFP).
Matar Idriss Deby, Hinda a yayin da take gabatar da jawabi a wurin jana’izyar mijinta, wanda ya rasu bayan lashe zabe a karo na shida, wanda aka gudanar ranar 11 ga Afrilu, 2021. (Hoto: Christophe PETIT TESSON/POOL/ AFP).
Al’ummar kasar Chadi sun kasance jikin halin juyayi a a wurin taron jana’izar Shugaba Idriss Deby Itno. (Hoto: Issouf Sanogo /AFP).
Dakarun sojin kasar Chadi suna bankwana ga gawar Shugaba Idriss Deby. (Hoto: Issouf Sanogo/AFP).
Yadda dakarun sojin kasar suka kasance a kame a yayin taron jana’izar. (Hoto:  Christophe PETIT TESSON/ POOL/AFP).
Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron (Hagu) da Shugaban Kasar Dimokuradiyyar Kwango, Felix Tshisekedi (dama) suna yin bankwana ga gawar Idriss Deby Itno. (Hoto: Christophe PETIT TESSON/POOL/AFP).
Dan marigayin, Mahamat Idriss Deby (Hagu) yayin tarbar Shugaban Faransa, Emmanuel Macron (a tsakiya) a wurin jana’izar da aka yi a birnin N’Djamena a ranar Juma’a. (Hoto: Christophe PETIT TESSON / POOL / AFP).
Wani jami’in sojin Chadi yana sintiri a wurin taron jana’izar Shugaba Idriss Deby wanda ya samu halarcin shugabannin kasashen duniya. (Hoto: Christophe PETIT TESSON/POOL/AFP)