Yadda aka yi jana’izar surukar Buhari a Zariya 

An yi jana’izar mai dakin surukin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Muhammad Sani Sha’aban.

Yadda aka yi jana’izar surukar Buhari a Zariya 

An yi jana’izar matar surukin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Muhammad Sani Sha’abban.

A ranar Lahadi aka yi jana’izar Hajiya Bilkisu a unguwar GRA da ke Zariya.

Marigayiya Hajiya Bilkisu Sha’aban wadda ita ce ta biyu a gidan mijinta, ta rasu ne a ranar Asabar a wani asibiti da ke Abuja bayan doguwar jinya.

’Yar shekara 52, Marigayiya Hajiya Bilkisu ta bar yara uku da mijinta, Alhaji Sani Sha’aban.

Marigayiyar ’ya ce ga fitaccen tsohon editan jaridar New Nigeria, Kaduna, Marigayi Alhaji Usman Mairiga.

Mijinta, shi ne Danburan na Zazzau kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Sani Mahmud Sha’aban.

Dansa na auren daya da cikin ’ya’yan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Cikin wanda suka halarci jana’izar, har da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa mai kula da Shiyyar Arewa maso Yamma, Honorabul Garba Mohammed Babawo.

Tuni dai aka kai ta makwancin ta a makabartar Dakace da ke Zariya a ranar Lahadi.