Yadda aka yi jana’izar ’yan Maulidi 36 a Kaduna

Motar ’yan Islamiyyar ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota, suka ce ga garinku nan

Yadda aka yi jana’izar ’yan Maulidi 36 a Kaduna

An gudanar jana’izar mutane aƙalla 30 da suka rasu a hanyar zuwa taron Maulidi a Jihar Kaduna.

Wasu 34 daga cikin ’yan Maulidin sun jikkata a sakamakon hatsarin motar da ta yi ajalinsu.

’Yan Islamiyyan sun gamu da ajalin nasu ne bayan motar da suke ciki ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota.

Hatsarin ya ritsa da su ne a yankin Kwandari da ke kusa da Saminaka a Karamar Hukumar Lere.

An gudanar da jana’izar tasu bisa tsarin addinin Muslunci.