Yadda aka yi jana’izar ’yar Sarkin Katsina
Marigayiyar ta rasu tana da shekara 35, kuma ta bar yara uku.
’Yar Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Khadijah, wadda aka fi sani da Andijo, ta rasu.
Ta rasu a Abuja tana da shekara 35, kuma ta bar ’ya’ya uku.
- Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin
- Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata
An yi jana’izarta a fadar Sarkin Katsina ƙarƙashin jagorancin Imam Mustapha Gambo.
Ɗaruruwan mutane sun halarci jana’izar, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da kuma al’ummar gari.
Bayan kammala jana’izar, Gwamna Radda ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai tausayi kuma mai son zaman lafiya.
Ya roƙi Allah Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa iyalanta haƙurin wannan rashi.
Haka kuma, Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya raya ’ya’yanta uku da ta bari.
Daga cikin manyan baƙi da suka halarci jana’izar akwai Mataimakin Gwamnan Katsina, Hon. Faruk Jobe; attajiri Alhaji Dahiru Mangal; Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Bello Shehu; Daraktan DSS, Jabiru Tsauri.
Sauran sun haɗa da Lamidon Katsina, Alhaji Usman Abba Jaye; Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman; Dan Malikin Katsina; da kuma Wazirin Katsina, Alhaji Ida, da sauransu.