Yadda aka yi na kai ga kafa gidauniya – Fauziyya D. Sulaiman
Sunan Fauziyya D. Sulaiman ya shahara a nan Arewa sakamakon rubuce-rubucen da ta yi. A baya-bayan nan ta shiga harkar tallafa wa marasa galihu da marasa lafiya marasa karfi, inda take kai dauki ga marasa lafiya ta amfani da gidauniyarta ta Creatibe Helping Needy Foundation. Fitacciyar marubuciyar tana cikin marubuta labarin shirin Dadin Kowa da […]
Sunan Fauziyya D. Sulaiman ya shahara a nan Arewa sakamakon rubuce-rubucen da ta yi. A baya-bayan nan ta shiga harkar tallafa wa marasa galihu da marasa lafiya marasa karfi, inda take kai dauki ga marasa lafiya ta amfani da gidauniyarta ta Creatibe Helping Needy Foundation. Fitacciyar marubuciyar tana cikin marubuta labarin shirin Dadin Kowa da Kwana Casa’in na Arewa 24 da wasu fina-finan Kannywood. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana yadda ta taso da nasarori da kalubalen da ta fuskanta a harkokin da ta sanya a gaba:
Tarihina
Sunana Fauziyya Danladi Sulaiman, wadda aka fi sani da Fauziyya D. Sulaiman. An haife ni a Unguwar Fagge a Kano a 1981. Na yi firamare a Kano, na yi makarantar mata ta kwana ta ’Yar Gaya inda na yi shekara 3, daga nan na dawo GTC Dala, inda na kammala sakandare. Sannan na yi Islamiyya a Kano. Daga nan sai aka yi min aure, sai a shekarar 2003 na koma makarantar Koyon Aikin Kiwon Lafiya wato School of Hygiene, Kano, inda na yi diploma. Na kuma yi karatun kwamfuta inda nan ma na yi diploma. Na kuma yi kwasa-kwasai a harkar rubutu, wadanda yawanci a karkashin kungiyoyi muka yi kamar su ANA da sauransu, sannan akwai horo da na samu a karkashin gidan Talabijin na Arewa 24 tare da wani Bature mai suna Francis a shekarar 2015.
Ayyukana
Baya ga aikin gidauniyata da nake yi, na dan yi aiki a bangaren abin da na karanta wato bangaren lafiya duk da cewa dama can ni marubicya ce, domin da shi na fara tun kafin in fara aiki ko karatu. Na rubuta littafi kusan 23, na kuma rubuta fim kusan 100. Sannan ina cikin marubatan shirin Dadin Kowa da Kwana Casa’in. A takaice ni ma’aikaciya ce a Arewa 24 domin kusan bayan aikin rubutu da gidauniya, shi ne aikin da nake yi sosai.
Dalilin bude gidauniyata
Dalili da yadda na bude wannan gidauniya, ba na mantawa akwai wani yaro mai suna Najib da a shekarar 2014 ya samu matsalar koda, wanda ta kai ana neman kudin magani a asibitin Nasarawa amma babu kudin. Ana bukatar a rika yi masa wankin koda sau uku a mako wanda ya kama Naira dubu 15, akalla ana kashe masa kusan Naira dubu 70 a wata. Sai aka sa sanarwa a kafafen sadarwa na zamani ana neman taimako. Sai bakin ciki ya kama ni saboda dan ungurwamu Fagge ce, inda aka haife ni. Sai na shiga bakin cikin cewa yaro matashi mahaddacin Kur’ani wanda bai wuce shekara 18 ko 19 ba, kuma shi ke limanci, amma kuma a ce wai an rasa kudin da za a yi masa magani. Sai na saka a shafina a matsayina na marubuciya mai mabiya da yawa na rubuta cikin bacin rai cewa a garin Kano a Unguwar Fagge a rasa wanda zai biya masa kudin magani? Sai mutane suka fara cewa za su taimaka a bayar da asusun ajiyar kudi na banki. Sai na je asibiti na same shi na karbo asusun ajiya. Cikin kankanen lokaci sai aka samu kudi. Daga baya mutane suka ce in bayar da nawa asusun maimakon wancan domin ba su sansu ba. Sai aka tara kudi na kai wa yaron.
Daga baya sai mutane suka fara yi min magana ta dai kafofin sadarwa cewa sun ga na taimaki wani yaro, su ma suna da marasa lafiya in taimaka musu. Sai su rubutu mara lafiyarsu da abin da ke damunsa da asusun ajiya, sai in wallafa a shafina cewa ana neman taimako a shafin. Sai a tara in ba su. Daga baya sai muka fara samun matsala da yawancin masu tara kudin ko su marasa lafiyar, da yawa mun samu wadanda suka cinye kudin musamman dangi, ko kuma ba sa yin abin da ya kamata. Saboda haka daga baya sai na ga tunda Allah Ya amshi abin, sai na ce bari in sa asusun ajiyanmu, wanda da shi muke tara kudin mu kai mutum asibiti, mu ci gaba da bibiyan lamarinsa har ya samu sauki. Daga baya kuma sai muka bude gidauniya domin abin ya zama ingantacce kasancewar lamarin ya bunkasa, wanda ko daga ina mutum zai iya taimakawa, shi ne na assasa Creatibe Helping Needy Foundatin muka yi mata rajista, inda yanzu haka da asusun gidauniyar muke amfani wajen tara kudin da muke taimaka wa mutane.
Nasarori
Nasarorin da muka samu ba za su lissafu ba gaskiya. Domin a yanzu haka mun taimaka wa marasa lafiya masu yawan gaske. Nasarorin sun kunshi taimaka wa marasa lafiya su samu sauki kamar wadanda za a yi wa aikin baya wadanda ko mikewa ba sa iya yi da wadanda aka yanke wa kafa da masu haihuwa da za a je wajen haihuwa suna bukatar a yi musu aiki babu kudi. Wadansu mun yi musu aure, wdanasu gidajensu sun rushe mun taimaka musu an gina musu. Wadansu ciwon daji ne da kuma tallafa wa marayu da suransu. Don haka gaskiya nasarorin suna da yawa, kawai sai dai godiya ga Allah.
Kalubale
Ba a rasa kalubale, amma ni a rayuwata ban samu wani kalubale ba, domin ina da sheara 19 aka yi min aure. Don haka rayuwa sai godiya kawai domin babu wani kalubale da zan iya cewa na rike ina tunawa da shi. Amma a gidauniya muna fuskantar kalubale da dama, inda a wasu lokuta nakan zama kamar marokiya wajen neman taimako ga mutane. Domin wadansu da dama suna tunanin idan suka kawo kukansu gare ni zan share musu hawaye, wadansu suna zaton ni ce ke bayar da kudin da kaina ba nema nake yi ba. Saboda haka wani lokaci za ka ga ga mara lafiya, amma mun rasa kudin da za mu taimaka masa. Za mu rubuta a shafukan amma ba a samu ba. Wani lokaci kuma da mun sa sai ka ga an samu cikin sauri.
Sai kalubale wajen marasa lafiya. Wani lokacin muna samun matsala wajensu domin wadansu suna ganin kamar kudin banza ne, ko irin kudin ’yan siyasar nan da an fara taimakonsu sai suka rika zaton dole ne a yi musu, musamman wadanda suka zo daga karkara sai ka ga wani lokacin ba sa yin abin da ya kamata. Sai ka ga muna fama da mara lafiya ya zauna a asibiti amma ya ki. Musamman idan suka ga mun ki ba su kudin a hannunsu, muna lura da su ne kawai. Musamman iyaye maza ko dangi sai ka ji suna cewa sun gaji suna da aiki ko noma. Wadansu kuma sai mun gama shirin za a yi musu aiki, kamar yadda muka yi da wata, har an gama shirin, likita ya sanya kayan aiki, an shiga da ita sai take cewa wai ba ta yarda ba inda har kafa za a yanke mata. Haka wani ya ce wai hannunsa da za a yanke da shi yake bara yana samun kudin da yake cin abinci, don haka sai an yi ta da wajewa, wai idan an yanke masa hannun da me zai ci abinci? Muna samun irin wannan da yawa wanda kuma suke kawo mana matsala.
Abin tunawa
Abin da nake so ko bayan raina a rika tunawa da ni, shi ne ina matukar son sa wa mutane farin ciki. Domin wani lokaci nakan kasa danne kaina, idan ina da kudi, sai na ga sun kare. Kuma duk wanda ke kusa da ni a lokacin shi ma zai samu. Don haka babban abin da nake so a rika tunawa da shi shi ne ina son sanya wa mutane farin ciki a rayuwa.
Wanda nake koyi da shi
Gaskiya na taso taimako yana
cikin raina domin na taso ina cewa idan na yi kudi zan taimaki wane da wane musamman idan na ga halin da talaka yake ciki kuma an yi watsi da shi. Don haka kai-tsaye babu wanda zan ce ina koyi da shi, taimako wani tsohon burina ne.
Amma kuma wata rana lokacin na fara wannan harka jifa-jifa, sai na ga ana hira da wata uwar marayu a tasharmu ta Arewa 24 da har tana da gida da take sauke ’yan gudun hijira da marasa lafiya. Sai na ce ni ma zan ci gaba insha Allahu domin ta burge ni, amma ni ta fuskar marasa lafiya. To wannan hirar ta kara min karfin gwiwa.
Burina
Babban burina a rayuwa yanzu shi ne wannan gidauniya ta samu ta zauna da kafarta. Wato in ga an samar wa wannan gidauniyar jari mai karfi ko hannun jari, ta inda idan mun samu mara lafiya ba sai mun nemi taimako wajen wani ba. Sai dai mu diba a cikin kudin da muke da su mu je asibiti mu lura da shi har ya warke. Sannan ko bayanmu wadanda za su gaje mu su ci gaba wannan abin da muka assasa na taimakon marasa karfi.
Shawara ga mata
Shawarata ga mata ita ce kowace mace ya zama tana da wani tunanina na son ta tallafi al’umma ba wai ’ya’yanta kawai ba, domin mace ce ake kallo a fagen tarbiyya da taimakon al’umma. Idan kuma al’umma ta gyaru, dukkan duniya za ta gyaru. Ki sa wa ranki cewa ko a gida ne za ki iya taimakon na kusa da ke ba sai kin je waje ba, sannan ki koya wa ’ya’yanki wani abu da za su yi koyi da shi. Sannan ina kira ga mata mu yi kokari wajen rike aurenmu, duk wadda ta yi wa mijinta biyayya za ta samu hadin kansa, domin idan kina da aure kika samu hadin kan miji an fi samun nasara. Wadansu suna ganin sai sun kashe aurensu ne za su samu abin da suke so, wannan ba haka ba ne. Don haka mu daure mu sanya hakuri a zamantakewar aure.
Sannan iyaye mu dage wajen kula da tarbiyya da ilimin ’ya’yanmu na boko da addini. Abin da za ka yi wa yaro ka taimake ke nan. Mu yi iya yinmu wajen ba su ilimi, mu dage wajen bayar da tarbiyya. Tun suna kanana mu sanya musu son taimako da jinkai. Domin rashin koya musu taimako shi ya kai kasar nan inda take yanzu. Kowa ya samu kansa kawai. Amma idan muka fara gyarawa nan gaba insha Allahu za a samu abin da ake bukata.
Taimakon da ba na mantawa
Akwai wani Murtala da ya yi shekara kusan 8 yana jinya a kwance cikin daki, komai a nan yake yi; fitsari da bayan gida. Ya ce babban burinsa a duniya shi ne ko sauki ya samu ya gan shi a keken guragu yana tafiya. Da muka shiga cikin lamarinsa da taimakon manya ciki har da Uwargidan Shugaban Kasa, A’isha Buhari aka kashe masa kusan Naira miliyan 10. Yanzu haka yana tafiya da kujerar guragu, an cika masa burinsa. Idan na tuna wannan nakan yi farin ciki. Haka mun taba samun wata kafafunta biyu sun rube, aka yanke kafafun aka yi mata dashen kafa. Akwai wata mata ma za ta haihu tana zubar da jini ga yaro a cikinta, inda ta galabaita sosai, da aka cire mata yaron nan sai na ga kamar ni aka cire wa yaron. Akwai irinsu da yawa gaskiya da ba zan manta da su ba, domin dama burina shi ne in ga mutane suna farin ciki.