Yadda aka yi na kai Shata Amurka – Aliyu Modibbo

Dokta Aliyu Modibbo, tsohon Ministan Ciniki kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, na cikin wadanda suka kulla kyakkyawar alaka da mashahurin mawakin nan marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina. Aminiya ta gana da shi, inda ya yi bayanin yadda ya kai Shata Amurka, ya kuma bayyana ma’anonin wasu kalamai da suka yi fice a wakar […]

Yadda aka yi na kai Shata Amurka – Aliyu Modibbo

Daga dama marigayi Mamman Shata da Aliyu Modibbo lokacin da ya kai shi Amurka.Dokta Aliyu Modibbo, tsohon Ministan Ciniki kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, na cikin wadanda suka kulla kyakkyawar alaka da mashahurin mawakin nan marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina. Aminiya ta gana da shi, inda ya yi bayanin yadda ya kai Shata Amurka, ya kuma bayyana ma’anonin wasu kalamai da suka yi fice a wakar Shata da sauran al’amuran da suka shafi rayuwar mawakin:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Dokta Aliyu Modibbo: Sunana Aliyu Modibbo, ni mutumen Jihar Gombe ne, an haife ni a Kumo (Hedkwatar karamar Hukumar Akko), nan na girma na dan yi makaranta da sauransu, na koma Mubi, inda na karasa sakandare. Daga nan na dawo na yi aiki talabijin a Bauchi; daga nan kuma na samu zuwa Amurka karatu, inda na yi Digiri na Farko a fannin aikin jarida, wato a rediyo da talabijin; bayan nan na sake yin Digiri na Biyu a fannin Harkokin Siyasar Afirka; sai kuma na sake yin Digiri na Uku a fannin Ilimi a Jami’ar Jihar Kalifoniya ta Los Angeles a kasar Amurka. Bayan nan na yi dan aiki a Amurka kadan, na dawo Najeriya, na soma koyarwa a Jami’ar Abuja; sai kuma na fara aiki a fadar Shugaban kasa, inda na zama Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa a 1995 (wato lokaicn mulkin Shugaba Janar Sani Abacha); kodayake zamanin Babangida na dawo, amma ban yi aiki na dindindin da su ba, domin nakan je a lokaci-lokaci. Na yi aiki da marigayi Janar Abacha, na zo na yi aiki da Janar AbdulSalam Abubakar.
A mulkin farar hula, bayan an koma dimokuradiyya da Cif Obasanjo ya zo, sai aka bar ni a ofishin Shugaban kasa, wato kamar babban jami’insa, wanda ake ce masa Chief of Staff. A nan na zauna har Allah Ya sanya Obasanjo ya fara ba ni Minista a shekarar 2002, kimanin shekaru 13 da suka shige. Na yi minista na farko, wato minista a ma’aikatar tama da karafa. Bayan an ci zabe da Obasanjo ya dawo, sai ya sake dawo da ni fadar Shugaban kasa dai, nan ofishin babban jami’insa, “Chief of Staff.” Daga nan sai ya nada ni Shugaban Kamfanin Fijo (Peugeot) da ke Kaduna; duk dai na hada ina aiki, ina kuma shuagaba a can. Ina aiki a fadar Shugaban kasa, a shekarar 2006 ya ba ni Ministan Ciniki da Kasuwanci. To, cikin ikon Allah bayan Malam Umaru Musa ya ci zabe, sai ya ba ni Ministan Babban Birnin Tarayya, daga nan aka yi dan shekara daya da rabi da mu a gwamnatin.
Da aka samu canjin gwamnati sai na soma harkokin kaina, na dawo tushen inda na soma aiki, wato na bude jaridar Rariya, wadda ke fitowa cikin harshen Hausa a kowane mako. Na kuma zabi wannan ne yadda kowa ya sani, za mu iya yin jaridar Turanci, tunda da Turanci aka koyar da mu aikin jarida. Abin da ya fi muhimmanci shi ne a yi da harshen da jama’a za su fi amfana da shi.
A halin yanzu ina harkokin kasuwancina, kuma ko ina so, ko ba na so, dole a jawo ni cikin harkokin siyasa.
Aminiya: Yaya aka yi ka hadu da Dokta Mamman Shata Katsina?
Dokta Aliyu Modibbo: Alhamdulillahi. Ka san kauna ita ta hada ni da shi. Kuma tun ina yaro, ina kauyenmu a Kumo na tuna, ina ko shekara shida ko bakwai ya zo, ya yi wasa. Muka je, muka leka ta inda ya sauka. A nan na gan shi. Daga nan dai na ji ina sha’awar wakokinsa. Cikin ikon Allah a 1987, sai Jarman Kano, Marigayi Alhaji Adamu dankabo, ya zo garin da nake a can Los Angeles (ta Amurka), sai  wani abokinmu ya ce ga Jarma zai zo, in je in tarye shi a filin jirgin sama. Ni na dauka wani tsoho ne, sai na je da motata na dauke shi a filin jirgin sama. Ya ce mini babu wanda zai dauke shi, ka dauke shi. Ashe ya zo sayen jirgin sama ne a garin da nake, wanda ake kira da Long Beach California. A lokacin kuma ina Jami’ar Carlifornia (UCLA), amma ina zaune a wannan gari na Long Beach. Na je na dauko shi daga filin jirgin sama. Ina bude mota sai ya ji wakar Shata, muna ta dan ji, sai ya ce mini, ‘kana son Shata ne?’ Na ce kwarai kuwa, sai ya ce ai ba ka fi ni ba. Da haka aka soma, sai na ce masa, a’a, ranka ya dade ina jin na fi ka son Shata. Ka ga duk babu wakar da nake ji wadda ta fi ta Shata. Na ce har da wakokinka ma, na sa masa ya ji. Ya ce mini har a Amurka kana samunsu, na ce duk lokacin da na zo Najeriya zan saya, ko in sa a aiko mini. To, lokacin duk ban taba haduwa da Shata kai-tsaye ba, sai na ce Allah Sabbi nani, ga shi ku attajirai ba ku taba kawo shi ko Ingila ba, alhali Yarbawa da ’yan kabilar Igbo suna kawo nasu (mawakan). Sai ya ce, ni kuwa na yi maka alkawari, in za ka samo masa takardar gayyata, zan kawo shi. Zan dauki nauyin kawo Shata. Sai na ce ai kuwa an dace, domin Jami’ar Kalifoniya za ta yi bikin cikar shekara 50 da kafuwa; kuma ana koyar da Hausa a wurin, sun kuma san Shata, har ma an rubuta littattafai guda uku a kansa. Wato, wadannan littattafai na Digiri na Uku (PhD) ne. Shi ne, sai na ba shi wannan labari, da na ba shi labarin, sai ya ce, wallahi ka samo mini. Ni kuwa da na je kashegari sai na samu shugaban sashin koyar da Hausar, wanda ake kira Russel Shoe, ya taba koyarwa a Jami’ar Bayero, inda aka rika yi masa lakabi da Malam Takalmi don sunansa Farfesa Shoe. Sai na zo na samu Malam Takalmi, na ce Allah gafarta Malam, don ya iya Hausa radau kamar jakin Kano, na ce masa Malam ga fa dama ta samu, za a iya kawo Shata Amurka, amma sai da takardar gayyata. Sai ya ce mini ai Modibbo ba mu da kudi, ka san ba za mu iya ba. Sai na ce masa kada ka damu, akwai wani wanda ya ce zai kawo shi. Na zo na samu takardar gayyata, Jarma ya karba, ya koma da ita Najeriya.
Da ya sake dawowa, sai ya kira ni, ya ce kai Modibbo ni fa ba zan iya zuwa da Shata ba, saboda a gaskiya wadansu hidindimu sun sha mini gaba. Na ce, akwai wani abokina zai zo, ai sai ya taho da shi. Sai ya ce, a’a, duk duniyar nan ba zai iya hada Shata da kowa ba, in ba ni ba; in ba shi zai kawo shi ba, sai ni. Sai na ce, ai kuwa yallabai zan fara rubuta jarrabawata ta Digiri na uku, wato ‘PhD.’ Sai ya ce, a’a, makonni biyu dai kuwa ai za ka iya zuwa. Sai na shigo jirgi na taho New York, wani abokina Dokta Hassan Biu ya zo ya dauke ni, ya kai ni filin jirgin sama, na hau jirgi, na shiga Swiss Air na tafi Legas, daga can na tafi Kano na dauko Shata.
Sai na biyo na zo na samu dankabo, da na same shi, sai ya ce lallai sai a je Funtuwa a zo da Shata. Sai kuma Dokta Alkali, wannan dan uwana ne, domin duk sa’adda na zo Najeriya shi yake raka ni inda duk za ni, tare muka je da shi, aka dauko Dokta (Shata). Daga ganina sai Shata ya ce raina ya kwnata da wannan yaron. Kai hatta yaran Shata irin su Ya’u Wazirin Shata da muka saba daga baya suke gaya mini cewa, daga ganinka ya ce ina son wannan yaron. Shi ke nan sai jininmu ya hadu, har ma wadansu sun shirya wata kutungwila, amma dai hankalin Jarma ya kwanta.
Sai aka ce ai Shata da yaransa ba su da Fasfo. Da za a yi masa fasfo, ni na yi masa tsari, inda na ba shi shawara cewa, ba za a tafi da yawa ba, a tafi da ’yan amshi uku da makada uku, sai ya ce ya yi. Muka je Jarma ya shirya, sai aka ce babu fasfo a Kano, sai mun je Kaduna. Muka je Kaduna da Jarma har da shi Dokta (Shata). Muka zo Kabo Guest Inn muka zauna da Shata, shi kuma Jami’in Shige da fici na manta sunansa, shi ma wani mai son Shata ne. Jarma ya kira shi, ya ce kada ka rufe yau zan zo a yi wa Shata biza, don lokacin Amurka suna bayar da biza a Kaduna, saboda suna da karamin ofishin jakadanci (Consulate) a nan titin Ahmadu Bello Way. Muka zo aka yi fasfo, amma ba a gama ba sai kusan karfe shida na yamma. Su ma ofishin Jakadancin Amurka suka ce ba za su rufe ba a ran nan har sai sun ba shi bizar. Ba su rufe ofishinsu ba har karfe takwas na dare. Muka je aka bayar da biza, aka sayi tikiti, muka shiga jirgin British Airways. Wallahi ba su rufe ba da Jarma ya kira su ya ce musu Shata ne, sai suka ce ai sun san shi. Ka ga dai ba su jin Hausa, amma suka ce za su bar ofis a bude har sai sun ba shi biza. Suka ba shi biza, muka zo Landan muka dan tsaya daga nan muka juyo. Shi ne ka ji yana cewa, “Nan ne muka zauna nan cikin tasha. Daga Landan sai Amerika.’ Da dai muka dan zauna, ba mu shiga cikin Landan ba, daga nan muka tafi Los Angeles. Da muka sauka, dama kafin in tafi na gaya wa wasu abokaina, gaskiya zan je in dauko Shata ya kamata a taimaka mini, tunda ba zai yiwu in yi dawainiya da mutum bakwai ba ni daya, amma wallahi duk sai suka dare; kowa sai ya kauce sai ni daya. Sai shi Dokta ya ga kamar ni hankalina ya tashi, domin lokacin da muka isa da magariba ne, kuma ranar da za a yi wasan a ranar muka isa.
A wannan ranar ya yi wakar Shata Bakon Amerika. Domin da muka sauka ko masauki ba mu je ba, sai muka zarce wurin da ake wannan taro na bikin cika shekara 50 a cikin sashin nazarin harkokin Afirka “African Unibersity Centre of UCL” da ke Jami’ar Kalifoniya a Los Angeles. Muka zauna, a nan ne ya yi wakar Shata Bakon Amerika. Ba mu bar wurin ba har sai wajen karfe 11 na dare, da muka je otel sai ya ce, to Modibbo mutane da suke cewa, ko muna yin irin na su dankwairo, sai an tsaya ana ta bin waka ana bin ta, tun daga Kano ka ga na zauna da yarana? Na ce ban gani ba, ya ce, to ka ga ni haka muke yin wannan. Ka san yaransa suna ba shi girma, idan ya zo Iliya zai zauna shiru, yaronsa ne dan aike; sai Ya’u Waziri, wanda ya ce mini suna tare da Shata tunda aka yi musu auren fari. Don haka duk da dai yaronsa ne, Shata yana girmama shi, shi ma yana girmama Shata. Sai ya ce mini ka ga dai yadda ake yin wakar. Daga nan muka kwana daya, ya sake wasa, sai muka tafi Washington, can ma muka samu dankabo na jiranmu da muka gama sai muka tafi Landan.
A Washington ya je ya yi wasa, a rediyon Muryar Amurka (bOA). Ka ji sabonmu ke nan bayan nan da na dawo Najeriya, duk in na dawo hutu sai na je Funtuwa, lokacin Sanusi (autan Shata) yana karami. A lokacin akwai wani dan Shata da ya rasu, sunansa Babangida mutum mai fara’a, shi Shata ke kira ya kai ni ya sauke ni a otel din Mairuwa. Haka dai aka yi ta yi, har na gama na dawo. Da na dawo zan yi aure na kai masa kati, ban san ma zai zo ba. Ya ce mini dai shi ke nan ya ji zai zo. Kafin a daura auren mun je Gombe, sai muka koma kauyenmu Kumo da safe sai aka zo, aka ce mini wai Shata ya zo da tawagarsa, kuma ba mu yi masa tanadin masauki ba.

Ya zo da doguwar bas, dukkansu sun zo, kuma ya kwana cikin mota. Na ce, Subhanallahi! Muka ruga aguje, na zo na dauka ransa zai baci, na ce Dokta ban ji dadin wannan abu ba. Ni ban san za ka zo ba, kaza-kaza. Ya ce, ai tunda ka kawo mini gayyata dole in zo; aurenka ai ko a Amurka ne dole in zo, tunda dai akwai kauna tsakaninmu. Da hankalina ya tashi, amma daga baya Ya’u Waziri yake gaya mini cewa a’a, ai ba komai. Ya ce inda ba ya sonka, ai ba za ka gayyato Shata babu masauki ba, da tuni an bata. Kuma inda da ne da sai mu koma bayan gari, can gindin bishiyar kuka ko tsamiya mu yi kwanciyarmu. Ya’u Waziri ya ce tabbas Shata yana sonka ne, domin in har ka gayyace shi, ya zo babu masauki, to da tuni an bata. Da na fara aiki a fadar Shugaban kasa, in ya zo Abuja, sai ya zo gidana, ni kuma in sama masa otal, wata rana ma ya zo da mahaifiyar Sanusi ta yini ko ta kwana a gidana; ko kuma shi ma ya zo ya yini a gidana na Asokoro, sai in sanya masa fim din kokowar Turawa; yana son Wrestling ya yi ta kallo. Da ma sa’adda nake Amurka tsarabar da nake kawo masa ke nan kaset din kokowar Turawa.
Aminiya: Yaya za ka iya kwatanta basirar Shata da ta sauran makada da mawakan wannan zamani?
Dokta Aliyu Modibbo: Ai ba ma makada ko mawaka ba, ko masu rubutu ko masu kaifin ilimi da ake kira masu falsafa, Shata yana cikinsu. Ka san kowane karni, kowace al’umma Allah Yana jefo musu wani mutum mai wata basira da ta wuce kimantawa. Kuma ina jin shi ya sa wata rana ya ce mini Modibbo ka san abin da ya sa nake sonka, kai ba ka ma kallon kidan. Domin ni a Amurka bai yi mini waka ba, in ban da dai ambatona da ya yi ‘ni da Aliyu Modibbo’ har ya dawo, a sabonmu tun daga 1988 zuwa 1992 bai yi mini waka tawa ba. Sai da ya zo bikina ne sai ya soma yi mini waka. Ni kuma bai dame ni ba. Don in muka zauna za mu yi ta tadi ne, in ce masa wannan me ake nufi, me ya sa ka fadi wannan?
Ka san shi Shata ba ya son ya ji wakarsa.  Don ko Amurka ina yi masa haka. Lokacin da muka je Los Angeles sai na sa masa wakar Gagarabadau sai ya ce, don Allah don Annabi ka cire, sai na ce, amma dai dan kadan, shi kuwa sai ya ce, amma dai da an yi lalata. Sai ya ce don Allah ka cire, da na cire sai ya ce ka san fa mun shirya. Ka san fa mun yafe wa juna, mun shirya. Kuma muna zumunci, kuma abubuwa ne da aka yi da, da yarinta da nishadi da sauransu.
Shata da wasu daga cikin yaransa lokacin da yake wasa a AmurkaDa idan dankabo ya zo abubuwa suka cabe masa, sai ya ce ka je ka dauko mana mutumin naka. Wata rana na dauko shi daga Funtuwa. To, ni zai yarda ya zo, a wannan zuwan sai na taho da shi a mota, sai na saka masa wakar Sarkin Daura, ya ce ba ya so ya ji, na ce a’a ina so in yi maka tambaya ne, inda kake cewa, “Sarari mai kare gudun doki dan Musa.” Sai na ce, me kake nufi Dokta? Sai ya ce, to za ka kashe idan na gaya maka? Na ce, ‘eh.’ Sai ya ce mini “An yi wani lokaci da na jera idan na je gidan Sarki, na  ga mota, sai in ce a ba ni mabudi, in aka ba ni sai na tafi da ita, kuma da Sarki Bashar ya fito in ya tambaya wa ya dauki mota, in aka ce Mamman ne, sai ya yi shiru.” Ya ce: “Modibo ina daukar mota daya bayan daya sai da na dauki mota 15 da sabuwa da tsohuwa, kuma har yanzu da nake yi maka magana Sarki bai taba tambaya ta shin me ka yi da motocin nan ba. Shi ya sa ni ma na ce “Sarari mai kare gudun doki dan Musa.” Daga nan ni ma sai na daina sanya masa.
To, al’amura irin wadannan za ka ji su a dunkule, abu ne mai saukin fada, amma akwai tarihi da bukatar fassara a tattare da abin.
Aminiya: A matsayinka na tsohon malamin jami’a kuma dan jarida, yaya kake ganin za a alkinta wakoki da tarihin rayuwar Shata yadda za su amfani al’umma?
Dokta Aliyu Modibbo: To, Alhamdulillahi. Jami’o’i sun yi, mutane da dama sun yi rubuce-rubuce a kansa, kuma har yanzu ana yi, kuma ba za a daina yi ba. Muddin dai ana raye, na san dai ba za a daina ba; za a ci gaba da rubutawa. Abin takaici dai shi ne, zamanin da ya yi babu abubuwa irin na adana bayanai na fasaha, wato “Technology,’ tunda bai kai irin na yanzu ba. Kuma in ka ji kaset din wasu wakokinsa, sai ka ji suna wata irin kara; ka ji su babu dadin ji, ko suna wata iska-iska haka. Sai dai duk da haka masoyansa ba su damu da wannan ba. Kai ba kamar yanzu yadda ’yan fiyano da sauran masu wakokin zamani za ka ji su sarai ba. Wannan dai kawai shi ne za a ci gaba ka san ana cewa wai in ya mutu ba za a sake jin wakarsa ba; ba za a ji kaset dinsa ba, na tambaye shi. Da na sake matsa masa, sai ya ce ba haka ake nufi ba. Sai ya ce, to yanzu, cikin wakokina kai wacce kake so? Sai na ce na fi son waccan da waccan, sai ya ce ai akwai wata wadda ba ka ji. Sai ya ce, ai haka ne, akwai wasu wakokin a haka za su bata, amma ba za su bace wa wani ba, kuma za su bace wa wani, domin shi ba zai ji su ba; ba zai kuma same su ba. To, akwai wasu da sam ba za ka ji su ba. Saboda haka ni ma ina cikin mutanen da ke alfahari da cewa na tara wakokin Shata kusan dubu a kwamfuta, amma sai ka ga wata rana wani ya ba ni wadda ban taba ji ba. A zauren Alhaji Mamman Shata na facebook, akwai Sule Umar a Jigawa, kwanan nan ya ba ni guda 300. Za ka ga abubuwa da dama, to irin wannan ba zai taba karewa ba. Za a yi ta fahimtarsa, kuma za mu yi ta yi masa addu’a Allah Ya jikansa. Don na taba haduwa da wani malami da Dokta Umar Faruk na BBC ya hada ni da shi, da ya gabatar da ni sai malamin ya ce kai ne Dokta Modibbo da ka kai Shata Amurka? Ya ce ai ni ma ina son Shata. Sai ya ce mini, Shi Allah ba haka yake abinSa ba; ka san a kan abu guda sai Allah Ya yafe wa Shata. Ka san inda yake cewa ni abin nan na ban tsoro, na abin yana ban tausayi saduwarmu da Allah gobe don kuwa ’yar gaskiyarmu Shata. Ya ce ai ya yi nadama, in ma akwai kuskure ya yi nadama. Ko kuma inda yake jadadda Allah daya; “Ni ba malamai ba ne, ba na bori ba na tsafi. Ni haka Allah Ya yi ni.” To ka ga ni ya jadadda Allah. Ka bar maganar wasu abubuwa shi tsakaninsa ne da Allah kawai. Kuma ka ga Shata bai taba nunawa ya yi wa Allah tarayya ba. Don haka sai mu yi ta yi masa addu’a.