Yadda aka yi Sallar Idi a Saudiyya
Al’ummar kasar Saudiyya sun gabatar da Sallar Idin Karamar Sallah a safiyar Alhamis.
Turaren wutar da ake sanyawa a Masallacin Manzon Allah (SAW) gabanin Sallar Idi. (HOto: HSharifain).
Al’ummar kasar Saudiyya sun gabatar da Sallar Idin Karamar Sallah a safiyar Alhamis.
Dubun dubatar Musulmai cikin ado ne suka halarci sallolin a Masallatan Haramin Makkah da Madina da sauran birane da misalin karfe 6.15 na safiya, agogon Saudiyya.
- Dalilinmu na Sallar Idi ran Laraba —Dahiru Bauchi
- Karamar Sallah da ladubbanta
- Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono
- Ramadan: Darussan da Muka Koya a Azumin Bana
Sheikh Saleh bin Humaid shi ne limamin da ya jagoranci hawan Idin a Masallacin Haramin Makkah.
A Masallacin Manzon Allah da ke Madinah kuma Sheikh Ahmed Talib Hameed ya jagoranci Sallar.








