Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

Manoma a yankin Birnin Gwari sun fara konawa garuruwansu da fatan fara shirye-shiryen noma bayan Gwamnatin Kaduna ta yi sulhu da ’yan bindigar da ke addabar Jihar.

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

’Yan bindiga da ke addabar ƙananan hukumomi biyar a Jihar Kaduna sun sha alwashin ajiye makamansu tare da daina ta’addanci, a wani yunƙuri na zaman lafiya.

Waɗannan ’yan bindiga sun daɗe suna addabar ƙananan hukumomin Chikun da Kajuru da Kagarko da Birnin Gwari da Giwa, inda suka mamaye dazuka tare da kai hare-hare ga qauyuka da garurwa da kuma a manyan hanyoyin Kaduna-Birnin Gwari da Funtua-Birnin Gwari sai kuma Kaduna-Abuja.

Aminiya ta halarci zaman sulhu tsakanin wakilan gwamnatin jihar da haɗin gwiwan wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya inda gaggan ’yan fashin daji tare da muƙarrabansu suka halarta. An xauki kwanaki uku a watan Disambar bara ana tattaunawar, inda wakilinmu ya bi tawagar zuwa maboyan ’yan ta’addan domin ganin wainar da aka.

’Yan bindiga xaure da manyan makamai iri-iri sun halarci taron a Dajin Tsohuwar Gayan da ke Ƙaramar Hukumar Chikun a rana ta farko, na Dajin Rima da Maidaro da ke Giwa a rana ta biyu. A rana ta uku aka ziyarci ƙauyen Kamfanin Doka a kan hanyar Funtua-Birnin Gwari domin zantawa da ƙasurgumin ɗan bindiga Yellow Jamburos, wanda ya addabi hanyar Kaduna-Birnin Gwari yana sace mutane.

Majiyoyinmu tsaro sun shaida mana cewa kimanin watanni biyu da suka wuce aka fara tattaunawar a yunƙurin gwamnatin Kaduna na amfani da lallashi da kuma ƙarfi wajen kawo ƙarshen ta’addanci.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dai bai bayyana matsayar gwamnatinsa kan sulhu da ’yan bindiga ba, amma dai sulhun da gwamnatocin bayan suka yi a jihohin Zamfara da Katsina bai biya kuɗin sabulu ba.

Masana na ganin rashin samun shugaba ɗaya a tsakanin qungiyoyin ’yan bindiga ke kawo matsala wajen tattaunawa da su, amma wasu ganin duk da dole a kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa Maso Yamma, yankin da suka halaka rayuka da dukiyoyi tare da raba mutane da muhallansu.

Karɓar tubar ’yan bindiga:

A watan Nuwamban 2024 ne Gwamna Uba Sani ya karvi wasu tubabbun ’yan bindiga a shirinsa na ganin sun ajiye makamansu a Yankin Birnin Gwari.

Ya ce gwamnati ta samar da shirin sulhun ne tare da masu ruwa da tsaki domin kawo ƙarshen ta’addanci a jihar. Ya ce duk da gwamnati ta karbi tubar waxanda da suka zaɓi zama lafiya, amma ba za ta yi wata-wata ba wajen hukunta masu tuban muzuru.

Sulhu da ’yan ta’adda:

Wakilinmu ya halarci tattaunawa da aka yi da su a Chikun da Kajuru da Giwa da Birnin Gwari inda ’yan bindiga irin su Boka da Yellow Jamboros da Sadiq Yellow da Saleh Horror da sauransu suka yi alƙawarin ajiye makamansu.
Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar cewa ta halaka ’yan ta’adda 10,937 ta kama 12,538 ta kwato mutane 7,063 a qasar a shekarar 204.

Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ya sanar da hakan bayan alqaluman Hukumar Ƙididdiga ta Qasa sun nuna an kashe ’yan Najeriya 614,937 an sace 2,235,954, inda aka iya kuxin fansa aqalla Naira triliyan 2.2 a faxin qasar daga watan Mayun 2023 zuwa Afilun 2024.

Alƙawari da sharaɗin ’yan bindiga:

Awajen taron, jagororin ’yan bindiga sun bayyana buqatunsu, tare da nuna rashin jin daxi kan abubuwan da suka aikata, suna masu alƙawarin miqa makamansu da takatar da hare-hare. Sun qara da cewa buƙatar sojoji su daina kai musu hari sannan gwamnati ta sako ’yan uwansu da take tsare da su, sulhun zai tabbata.

“An ɗauki lokaci mai tsawo gwamnati ba ta nemi mu ba a kan batun zaman lafiya, hakan ne ya sa batun ya taɓarɓarewa. Muna ta rasa mutane babu gaira babu dalili a dukkanin ɓangarori. Amma a yanzu muna fatan cewa batun sulhun nan zai tabbata,” in ji Boka a lokacin da yake bayanin dalilinsu na ɗaukar makami.

Boka ya ce jami’an tsaro sun kashe musu mata da yara, “shi ya sa muka nemi makamai domin kare rayukanmu. Ba mu da bindigogi a shekarun baya an fi sanin mu (Fulani) ne da sanda da muke amfani da shi wajen kiwo, amma a yanzu da wuya ka ga Bafulatani da sanda sai dai bindiga”

Ya ba da tabbacin cewa mutanensa za su daina kai hari muddin jami’an tsaro suka daina kawo musu faramki. “Ya kamata gwamnati ta kula da mu kamar sauran ’yan kasa ta hanyar daina kai mana hari. Za mu daina satar mutane,” in ji shi

Sadiq Yellow, wani ƙasurgumin ɗan bindiga, ya jaddada bukatar a sako ’yan uwansu da ke tsare musamman a gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda ya ce yin hakan zai tabbatar musu da cewa da gaske ake zancen zama lafiya.

Shi ma wani xan bindiga, Musa da ya zargi jami’an tsaro da ’yan sa-kai da kai wa rugagen Fulani hari, ya nemi su bari sannan ya bukaci mutane da aka kora daga gidajensu da su dawo ba tare da tsoro ba.

Shi kuma Hassan Zubairu, mataimakin Yellow Jamboros, ya bada tabbacin cewa daga yanzu hanyar Kaduna-Birnin yanzu ta samu lafiya domin kuwa tuni sun daina hai hari a kanta.

A dajin Rima a Ƙaramar Hukumar Giwa qasulgumin ɗan fashin daji Haruna Ɗanduƙununu ya ce sun mika makamai ga gwamnati a baya kuma za su mika wasu idan zaman tsulhun ya ɗore.

‘Burinmu a samar da zaman lafiya’

Daya daga cikin masu shiga tsakani a wurin tattaunawar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya tabbatar wa ’yan bindigar cewa gwamnati da gaske take batun tsulhun. Ya ce “kamar yadda kuka roqa a sakar muku mutane da ke tsare, gwamnati za ta yi nazari a kan buqatunku idan zaman lafiyar ya xaure. Sai dai za mu buqaci ku saki duk mutanen da ke a hannunku a yanzu ba tare da sai kun jira gwamnati ta aikata hakan ba,” in ji shi.

Ra’ayoyin mazauna:

Mazauna yankin sun bayyana jin daɗinsu, inda Alhaji Idris Ardo Barka Sake daga garin Sabon Gayan da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja ya kira ga vangarorin da su ji tsoron Allah wajen tabbatar da ɗorewar sulhun. Ya roqi ’yan bindigar da su ba maraɗa kunya kada su juya wa tsulhun baya. Ya kuma yi fatan nan bada daxewa ba ’yan bindiga za su miƙa duk makamansu ga gwamnati.

Wani dattijio, Malam Abdulfatai, cikin farin ciki ya bayyana cewa shekara biyar rabonsa da shiga Tsohuwar Sabon Gayan, “saboda tsoron kada a sace ni ko kashe ni. Babu mai zuwa nan amma ga shi a yau duk mun zo saboda zaman lafiya.

Muna murna da wannan ci-gaba da aka samu har na ƙosa in koma gonata,”, inji shi a yayin da yake nuna gonarsa da hannu.

Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah a Birnin Gwari, Babangida Adamu ya ce yanzu al’ummar yankin hankalinsu ya fara kwanciya.

“Muna farin ciki da sulhun domin yanzu hanyar nan ta Funtua zuwa Birnin Gwari matafiya na bain ta ba tare da wata matsala ba. Sai dai kurum daga yankin Katsina akwai sauran yara da ke damun matafiya, don haka muke kira ga Kachalloli a yankin da su taimaka wajen hana su,” in ji shi.

Dagacin Kamfanin Doka, Ibrahim Musa a Birnin Gwari ya ce, “Muna rokon shugabanin Fulani da su sanya idanu a kan yara Fulani da ke kai Dabbobi suna cinye wa manoma kayan gona. Muna fatan ba na mu yi noma domin samun abinci da za mu ci da iyalanmu tunda an yi tsulhu.”

Maryam Abubakar mazauniyar qauyen Maidaro a Ƙaramar Hukumar Giwa ta nemi gwamnati ta samar musu da makaranta da asibiti domin ’ya’yansu sami ilimi, su mata su samu inda za su rika zuwa neman magani da haihuwa.
Ta kuma ce duk da tana noma tana fatan a bana zata samu damar yin noma cikin kwanciyar hankali kamar kowa saboda an samu zama lafiya.

Shirin dawowar ’yan gudun hijira:

Aminiya ta lura da mata da yara sun halarci taron a Tsohuwar Gayan inda suka riqa shiga gidajensu da suka gudu suka bari suna dubawa da shirin su dawo idan komai ya daidaita.

“Muna murna da komowa garinnu, muna san komawa rayuwarmu yadda take,” in ji wata matar aure.

Wakilinmu ya kuma lura da cewa matafiya da motoci sun fara zirga-zirga akan hanyar Kaduna-Birnin Gwari ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba. Wani matafiyi,

Muhammadu Abubakar ya tabbatar da cewa an samu natsuwa a ’yan kwanakin nan kuma hare-hare da da garkuwa da mutane a kan hanyar sun ragu.

Gaskiya ce magoya — Masanin tsaro:

Sai dai kuma wani masanain tsaro kuma shugaban ƙungiyar kauyuka da ke a kan iyakokin Birnin Gwari da Jihar Neja Ishaq Usman Kasai, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar an faxaxa sulhun zuwa maƙwabta irinsu Neja da Katsina da Zamfara domin hana ’yan bindigar can shigowa Jihar Kaduna.

Ya jaddada “kira ga gwamnati ta samar da hanyar taimaka wa mazauna karkaru da suka cutu daga ayyukan ’yan fashin daji musamman waxanda suka rasa dukiyoyinsu da rayuka domin hakan ne zai taimaka su yafe irin wahalhalun da suka shiga,” in ji shi.

Ta leƙo ta koma?

Sai dai kuma kimanin sa’o’i 72 da yin taron tsulhu a Tsohuwar Gayan aka halaka xaya daga cikin gaggan ’yan bindigan da aka zanta da shi a wurin, Samaila Suleiman Boka, wanda ke addabar yankin Chikun da Kajuru da Kagarko har zuwa yankin Rijana a Kachia, aka halaka shi, a wani hari da majiyoyin suka ce sojoji ne suka kai masa a yankin.

Ɗaya daga cikin shugabannin ’yan bindiga da aka yi sulhu da su, Jamboros ya koka kan harin da cewa zai iya kawo tsaiko ga sulhun a yankin Birnin Gwari.

Amma wani daga cikin jagororin tattaunawar ya ce batun sulhun zai ci gaba ba tare da wata matsala ba nan ba da jimawa ba za a ga amfanin sulhun.

Abin da gwamnatin Kaduna ta ce:

Kakakin Gwamnatin Kaduna, Ibrahim Musa, ya shaida wa Aminiya cewa gwamnatin jihar ce ta ɓullo da sulhun tare da haxin gwiwar wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya da nufin samar da tabbataccen tsaro da zaman lafiya.

Ya ce, “ya haxa da ajiye makamai da maido da su cikin al’umma tare da saka jari don inganta yankin karkara da magance matsalar rikicerikice.

“Shiri ne gagarumi da zai taimaka wajen magance matsalar tsaron.
Ya hada da tattaunawar da masu ruwa da tsaki, domin tattaunawar ta kai da an yi taruka sosai da kuma tattaunawa da nufin fahimtar juna wanda hakan ya yi sanadiyar ’yan bindiga suka ajiye makamansu suka kuma rungumi zaman lafiya,” in ji shi

Ya ce a ƙokarin tabbatar da sulhun gwamnatin ta soke aikin ’yan sa-kai musamman a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari, kuma Gwamna Uba Sani zai yi adalci ga kowa — manoma da makiyaya da ’yan kasuwa, domin samar da tabbataccen zaman lafiya a jihar.

Ibrahim Musa ya ƙara da cewa yunƙurin taimaka wa ’yan bindiga tsari ne da tafiyar da shirn tattaunawa da kuma amfani da ƙarfi.

Ya ba da tabbacin cewa duk da cewa suna maraban da waxanda suka rungumi zaman lafiya, gwamnatin zata dauki tsattsauran mataki a kan duk waɗanda au ci gaba da ta’addanci.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja