Yadda aka yi wa Amurka tonon silili kan leken asirinta
Amurka na fama da tonon silili kan irin ayyukan leken asiri da take gudanarwa a fadin duniya, al’amarin da ya jefa fadar White House cikin tunanin kan yadda za ta kawo karshen bibiyar sirrin abokan huldarta na kasashen waje, kamar yadda wani babban jami’in mulki a gwamnatin kasar ya bayyana. Wannan al’amari na leken […]

Amurka na fama da tonon silili kan irin ayyukan leken asiri da take gudanarwa a fadin duniya, al’amarin da ya jefa fadar White House cikin tunanin kan yadda za ta kawo karshen bibiyar sirrin abokan huldarta na kasashen waje, kamar yadda wani babban jami’in mulki a gwamnatin kasar ya bayyana. Wannan al’amari na leken asiri da aka bankado, ya zame wa Gwamnatin Amurka baban abin kunya da take ta kai kawo a kansa.
Shafin yanar sadarwa na wikileaks ne ya fara bankado ayyukan leken asiri da Amurka ta rika yi wa kasashen duniya, inda har ta kai ga shugaban shafin Jullian Assange ya shiga rikici da gwamnatin Birtaniya da ta Amurka. Ya kuma ga Edward Snowden, wanda ya yi aiki da Hukumar Tsaro ta kasar Amurka a matsayin dan kwangila, ya bankado yadda ake bibiyar sirri da sauraro wayoyin sadarwar shugabannin kasashen duniya.
Har yanzu ba a yanke matsaya ba, sai dai ana ci gaba da nazarin aiwatar da abin da ya dace, kamar yadda jami’in ya bayyana. daukar amtakin dakatar da bibiyar sirri da leken asiri shi ya fi dacewa, domin wannan al’amarin ya haifar wa Gwamnatin Amurka bacin suna a fadin duniya, musamman in an yi la’akari da Cibiyar Tsaro ta kasa ta rika bibiyar wayoyin tarhon shugabar kasar Jamu, Angela Merkel.
’Yar majalisar dattijan Amurka, Dianne Feinstein, Shugabar Kwamittin Bayanan Sirri na Majalisar, ta bukaci a sake “fasalin shirin tattara bayanan sirri,” bisa la’akari da zargin sauraren wayoyin tarho da Angela Merkel ke yin a tsawon shekaru. a wani sako da ta aike, wannan ’yar majalisar a karkashin tutar jam’iyyar Democrat, da ta fito daga Kalifoniya, ta ce, fadar White House ta sanar da ita cewa “tattara bayanai akan abokan huldarmu ba zai ci gaba ba.”
Shi dai jami’in harkokin mulkin Amurka, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya bayyana cewa bayanan ’yar majalisa ba daidai b ane, amma ya ce akwai yiwuwar a aiwatar da wasu ‘’yan sauye-sauye, wadanda suka hada da daina jin sirrin wayoyin shugabannin kasashen da suke kawaywen Amurka ne. Wannan jami’i dai ya doge kan cewa lallai kada a ambaci sunansa, domin ba a umarce shi ya tattauna al’amarin da manema labarai ba.
Rahotanni sirri da aka samu daga Jami’in Hukumar Tsaro ta kasa, Edward Snowden, sun bankado yadda aka rika sauraren wayoyin Shugabar Jamus, Angela Merkel, har sau 34, tare da sauran shugabannin kasashe.
kasashen da suka koka da leken asirin da Amurka take yi musu, sun hada da Faransa da Sopain da Mekziko da Jamus, har ma da wasu kasashe na nahiyar Asiya da gabas ta Tsakiya, wadanda suka hada da Saudiyya da Pakistan da sauransu.
kasashen tarayyar Turai sun mayar wa Amurka martini, inda sukayi barazanar yin watsi da yarjejeniyar kasuwancin da aka kulla tsaknin tarayyar da kasar Amurka. Su kuwa jami’an hukuma a kasar Jamus, cewa suka yi, duk wata yarjejeniyar tsaro da aka kulla don toshe hada-hadar kudaden ’yan ta’adda za ta yi watsi da ita. Wani babban jami’in gwamnatin Jamus, ya bayyana cewa Amurkawa na amfani da bayanan sirrin kasarsa ne, domin su tattara bayanan sirri kan tattalin arzikin Jamus. ‘”don haka ’yarjejeniya binciken sirri game da ta SWIFT an dakatar da ita.” Inji shi.
Wani shafin yanar sadarwa na Cryptone ya bayyana cewa Amurka ta gudanar da ayyukan leken asiri har biliyan 124 da miliyan 800 a fadin duniya, cikin shekarar 2013, al’amarin da ya karade kasashen da suka hada da Saudiyya da Jordan da Iraki da Masar da Iran da Afghanistan da Pakistan.
A Masar an yi ayyukan bibiyar jin sirri da yawansu ya kai biliyan daya da miliyan 900, sai Jordan an yi biliyan daya da miliyan 600; Iraki biliyan bakwai da miliyan 800; Iran biliyan daya da miliyan 730; Pakistan biliyan 12 da miliyan 760. kasar da tafi fama da ayyukan leken asirin Amurka ita ce Afghanistan, inda aka bibiyi jin sirri har sau biliyan 21 da miliyan 980.