Yadda aka yi wa karamar yarinya yankar rago a Filato

A ranar Asabar ce aka kashe wata yarinya mai shekara bakwai, Juwairiya Auwal a cikin gidan tarihi na birnin Jos da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Lamarin ya faru ne bayan aukuwar makancinsa a Tudun Fera, wata alkarya a birnin Jos, inda a nan ma wasu miyagu suka yi wa wani […]

Yadda aka yi wa karamar yarinya yankar rago a Filato

A ranar Asabar ce aka kashe wata yarinya mai shekara bakwai, Juwairiya Auwal a cikin gidan tarihi na birnin Jos da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa, a Jihar Filato.

Lamarin ya faru ne bayan aukuwar makancinsa a Tudun Fera, wata alkarya a birnin Jos, inda a nan ma wasu miyagu suka yi wa wani yaro mai shekara takwas, Faruk Abubakar yankan rago yayin da aka aike shi siyo abincin dabbobi.

A cewar mahaifiyar wadda mummunan tsautsayin ya rutsa da ita, Hajiyayye Haruna, ta ce marigayiyar da kuma yayarta, Fatima Auwal, sun fita tallan tsintsiyar shara ne a yayin da suka yi kicibus da wata mata wadda ta yi batar-dabo da su inda suka tsinci kansu cikin wata bukka da ke gidan tarihi na Jos.

Hajiyayye ta ce a nan ne aka kashe karamar yayin da babbar ta tsere da kafafunta.

Fatima mai shekaru 13 wadda ta ranta a na kare daga cikin bukkar ta zayyana cewa, “muna cikin hutawa a Tudun OP a unguwar Rikkos bayan mun yi yawon talla, sai kawai wata mata ta tunkaro mu tana tambayar farashin da muke sayar da tsintsiya daya”.

“Bayan mun fada mata farashin sai ta nemi mu ba ta kyauta amma muka yi mata gardama a kan hakan. Ta na bude yatsun hannanyenta a kan fuskokinmu, sai kawai muka tsinci kanmu a cikin wata bukka da ke gidan tarihin Jos.”

“Muna bayyana a cikin bukkar, sai ta zaro wuka ta yanka kanwata. Da na fahimci ta tunkaro ni sai kawai na tsinke a guje ina neman taimako.

A nan ne na riski wani mutum bisa hanya wanda ya kai ni ofishin ’yan sandan da aka shigar da kara”.

Hajiyayye ta shaida wa wakilanmu cewa an jami’an ‘yan sanda sun tsinto gawar Juwairiyya tare da kawo mana ita har gida da yanzu tuni aka sanya ta a gidanta na karshe.

NAJERIYA A YAU: Yadda jiragen soji suka kashe fararen a karo na biyu a wata guda

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar