Yadda aka yi wa Magajin Birchi kisan gilla

Al’ummar garin Birchi da ke cikin karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina sun wayi gari a ranar Litinin wannan makon cikin firgici sanadiyar kisan gillar Magajin Birchi Alhaji Abdulkadir Birchi da wadansu mutanen da ake zaton ’yan ina-da-kisa ne suka yi, yayin wasu kuma ke cewa barayin shanu ne. Aminiya ta kalato cewa,marigayin Magajin garin […]

Yadda aka yi wa Magajin Birchi kisan gilla

Al’ummar garin Birchi da ke cikin karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina sun wayi gari a ranar Litinin wannan makon cikin firgici sanadiyar kisan gillar Magajin Birchi Alhaji Abdulkadir Birchi da wadansu mutanen da ake zaton ’yan ina-da-kisa ne suka yi, yayin wasu kuma ke cewa barayin shanu ne.

Aminiya ta kalato cewa,marigayin Magajin garin Birchi Alhaji Abdulkadir Birchi mai kimanin shekaru 83, ya gamu da ajalinsa ne ta sanadiyar kisan gillar da aka yi masa a gidansa da ke cikin garin na Birchi da misalin karfe daya na dare ranar lahadin da ta gabata, ta hanyar harbinsa da bindiga, sannan kuma aka sassare shi da gatari.
Wadanasu daga cikin ’ya’yan mamacin Lawal da Sanusi sun shaida wa Aminiya cewa, al’amarin ya faru ne da misalin karfe daya na dare ranar lahadin da ta gabata,inda makasan suka shigo cikin gidan suka tarar da shi marigayin, har ma sai da marigayin ya ba su tsabar kudi har Naira dubu 300 domin su barshi da ransa amma suka kiya. “Sun kashe shi sun fita ba tare da sun dauki ko da ashana ba a cikin gidan,” inji ’ya’yan nasa.
Wata majiya kuma ta ce,maharan sun zo bisa babura 4 ne, wanda kowane babur yake dauke da mutane uku. Wadansu da Aminiya ta zanta da su sun ce,barayin shanu ne suka aikata wannan mummunan aikin, saboda rashin jituwar da ke tsakaninsu a kan irin yadda yake daukar tsattsauran matakin tsaro a yankinsa, wanda hakan ya hana su yin rawar gaban hantsi. Wadansu kuma na danganta wannan mummunan kisa a kan ’yan ina-da-kisa ne wadanda ake biyansu don aiwatar da irin wannan aiki. Kin karbar kudin da aka ce an yi masu ta yi da kuma kin daukar komai a gidan ne ya kara karfafa zaton masu ganin cewa an yo hayar wadannan mutane ne kawai domin su kashe Magaji.
An tabbatar da rasuwarsa ne bayan kai shi babban asibitin Dutsinma. Marigayi Alhaji Abdulkadir Magaji Birchi ya bar mata uku da ’ya’ya 33 da jikoki da dama. Daga cikin ’ya’yan nasa akwai Aminu Abdulkadir Birchi,na sashen Hausa na BBC. Sai kuma Dikko Abdulkadir, jami’i a hukumar hana fasa kwabri(Custom)ta kasa.
Tuni dai akayi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya shimfida, wanda babban limamin masallacin jumma’a na garin na Birchi ya jagoranta.
Kakakin rundunar ’yansandan jahar Katsina Mataimakin Sufurutanda Aminu Sadik Abubakar ya tabbatar da faruwar wannan lamari, inda kuma ya ce, tuni jami’ansu suka shiga farautar wadannan makasa,wanda kuma yake fatan samun nasarar cafko su.