Yadda aka yi auren gatan mutane 600 a Kebbi
Gwamnatin jihar za ta ci gaba da daukar nauyin auren gata domin rage yawan zawarawa da kuma tallafa wa masu karamin karfi
An daura auren mutane 600 a karkashin shirin auren gata a Fadar Sarkin Gwandu da ke Jihar Kebbi.
Gwamnatin jihar ce ta dauki nauyin biyan sadaki da kayan dakin kowacce daga cikin amaren 300.
An kuma ba da kayan gara da na abinci domin samar da musu sauki ga sabbin ma’auratan 600 daga kananan hukumomin jihar 21.
A jawabinsa a wurin daurin auren, Gwamna Idris, ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da auren gatan daga lokaci zuwa lokaci domin rage yawan zawarawa da kuma tallafa wa masu karamin karfi da ke son su yi aure.
- ’Yan bindiga sun sace mutum 1, sun harbe wani a Sakkwato
- Yadda Tsadar Rayuwa Ta Sa Aka Koma Hawa Jaki A Arewa, Kudu Kuma Tafiyar Ƙafa
Gwamnan ya ce auren gatan wanda shi ne na farko a jihar, an gudanar da shi ne bayan samun amincewa da shawarwarin malaman Musulunci domin tabbatar da an gudanar da shi a bisa tafarkin addinin.
Don haka ya shawarci sabbin ma’auratan da su tsarkake niyyoyinsu sannan su bi dokokin Allah wajen sauke hakkokin da ke kan kowane bangare a a matsayin ma’aurata domin samun zuri’a da kuma al’umma ta gari.
Gidauniyar NANAS ta matar gwamnan jihar, Nafisa Nasir Idris ce ta shirya auren gatan, wadda a jawabinta ta jinjina wa gwamnan kan tallafinsa ga shirin auren gatan.
Ta shawarci ma’auratan da su mutunta juna tare da kare hakkokin junansu a matsayin mata da miji.