Yadda aka yi wa ’yan banga kisan gilla

“Allah Ya isa, ba za mu taba yafewa ba.’’ Wannan shi ne irin kalaman da mazauna ’Yargalma suke furtawa a lokacin da Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari da mukarrabansa suka je jana’izar mutanen da aka yi wa kisan gilla a garin na ’Yargalma da ke cikin msarautar dansadau a karamar Hukumar Maru, bayan kwana […]

Yadda aka yi wa ’yan banga kisan gilla

“Allah Ya isa, ba za mu taba yafewa ba.’’ Wannan shi ne irin kalaman da mazauna ’Yargalma suke furtawa a lokacin da Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari da mukarrabansa suka je jana’izar mutanen da aka yi wa kisan gilla a garin na ’Yargalma da ke cikin msarautar dansadau a karamar Hukumar Maru, bayan kwana biyu da kashe sama da mutum 22 a garin ’Yartsaba a masarautar Zurmi da ke karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.
Idan ba a manta ba, ranar Talatar  makon jiya ne kungiyar ’yan banga da maharba ta jihohin Zamfara da Kebbi da Sakkwato da Katsina suka shirya wani taro don samun mafita kan yawan kashe-kashen da yake addabar jihohin, musamman saboda abin da suka kira gazawar gwamnatocin jihohin wajen shawo kan lamarin.
Sai dai kuma wannan taron wata sabuwar matsala ya haifar maimakon samar da mafita, ta yadda aka samu wadansu suka zagaya suka bayyana wa barayin cewa za a yi taro a rana kaza, lokaci kaza. Wannan ya sanya barayin suka aiko da sakon bukatar a dage wannan zaman, tare da gargadin cewa kada a kuskura a gudanar da shi. Amma wadanda suka shirya taron ba su yarda da abin da aka aiko musu da shi ba, suka ci gaba da gudanar da taronsu.
A ranar Asabar da rana ana cikin cin kasuwa, kuma masu gudanar da taron suna ci gaba da gudanar da taronsu, sai ga gungun mutane kan babura sama da dari, a kan kowane babur akwai mutum biyu. Sai suka zagaye inda ake taron suka rika harbin kan mai uwa da wabi, nan kam sai wanda kwanansa bai kare ba, sai kuma wadanda suka rika bacewa.
 Wani dan banga  mai suna Hussaini ya shaida wa manema labarai cewa, “Da suka zo sai suka zagaye mu,  kowannensu da bindiga sabuwa AK 47, babu abin da suke yi sai harbi, nan Kurma ya bace, ni ma na bi shi, ba mu sake haduwa ba, sai dai yanzu da muka dawo jana’iza.’’
Malam Abdullahi shi ma wani dan banga ne da aka fafata da shi, ya bayyana cewa bayan sun gama da masu taron sai suka shiga kasuwa, nan ma suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, wadanda suka gudu suka shiga daji aka bi su, dayake sun ajiye wadansunsu mutane a cikin dajin. “Idan suka harbe ka suka ga ta ki kamawa, sai su kama ka da karfi su murde maka kai, wuyanka ya karye, ko kuma su dauko dutse su kwada maka, ko kuma su zarge wuyanka da waya, ta haka za su kashe ka.’’
Malam  Muhammad shi ma wani dan bangan ne, ya bayyana cewa bayan kashe mutane sun kuma shiga gari suna kwashe kayan shaguna kuma sun kona shagunan, wadansu kuma sai kawai su banka musu wuta. “Wani abin ban mamaki da barayin shi ne yadda ba su taba yarda su bar gawar wani nasu ba, idan sun kasa daukar gawa sai su bata masa fuska da harsashi da kuma kafafuwarsa don  kada a gane shi”.
Shi kuwa Mai unguwa, Malam Adamu bayyanawa ya yi cewa, “Da farko sai da aka kawo mana gawarwaki guda 85, daga baya aka kawo 20, aka sake kawo 8, to ga shi har yanzu ba a daina kawo su ba, tun ana kirgawa har an daina.
 Zuwa lokacin hada wannan rahoton an samu kusan gawarwaki 215, tsakanin wadanda aka yi wa sallah da wadanda ba a rufe ba, wadansu kuma an kwashe su ne aka kai su kauyukansu.
Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari ya zargi wadanda suka shirya taron da alhakin kisan da ya faru, domin ya ce sun gudanar da taron ne babu izini, don haka a cewarsa, za a hukunta duk wani wanda aka kama yana da hannu cikin shirya taron.
Ana cikin wannan halin sai kungiyar ’yan banga ta Jihar Zamfara, a karkashin  jagorancin Alhaji Bashir G. Biyu Gusau, suka fidda wata sanarwa mai dauke da sanya hannun shugaba da sakatarensa , Alhaji Lawalli Musa Tsafe, suna nisanta kansu da wannan taron da aka gudanar tare da ’yan banga a garin na ’Yargalma da ke masarautar dansadau a karamar Hukumar Maru, inda suka nuna cewa taro ne tsakanin maharba da ’yan tauri, ba ’yan banga ba, kuma an gudanar da taron ne a karkashin jagorancin wani wanda ba su san shi ba, wai shi Kurma ’Yargalma, Don haka suka ce a daina jingina su da wannan taron da ba su san asalinsa ba, don kungiyarsu ba ta da wata masaniya kan taron.
Cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai shugaban ’yan sanda mai kula da jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara, Alhaji Mamman Sule, da Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Muhammad da kwamishinan ’yan sanda na Jihar Zamfara Ahmad Ibrahim, da dai sauransu.
Wani abin ban mamaki shi ne, bayan tsinuwa da gwamnan ya sha, a lokacin da zai koma, wadansu sun yi ta jifa, wanda ya sanya manema labarai da yake motarsu ce a baya suka sha duwatsu, aka farfasa musu gilashin motar da suke ciki, bayan gwamnan ya wuce.
Sanata Sa’idu dansadau ya zargi babban jami’in ’yan sanda na yankin dansadau da kuma Sarkin dansadau da nuna halin ko-in-kula game da kisan wadannan bayin Allah da ’yan bindiga suka yi.  Ya ce, “Mun gamsu cewa jami’in ’yan sanda (DPO) da Sarkin dansadau ne suka yaudari gwamnatin Jihar Zamfara ta dauki matakin rashin tausaya wa wadanda aka fada musu da kisa ba don sun yi laifi ba, sai don kawai suna kokarin gano hanyar da za a samu kwanciyar hankali a yankunansu”.
A ’yan watannin dai wani bangare a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna ya yi fama da hare-haren ’yan bindiga, wadanda ake danganta su da Fulani makiyaya, amma kungiyar Miyetti Allah ta nuna cewa wadansu ne suke shiga irin ta Fulani suke kai wa mutane hari, domin bata wa Fulani suna.