Yadda aka zabi Shugabannin kungiyar NFS masu barin gado

A yayin taron kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya na bana da za a gudanar daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2018, za a gudanar da zaben shugabannin kungiyar, yayin da tsofaffin za su sauka. Shin ta yaya kuma yaushe ne aka zabi shugabannin kungiyar masu barin gado? A ranar Alhamis 3 ga Afrilu, […]

Yadda aka zabi Shugabannin kungiyar NFS masu barin gado

A yayin taron kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya na bana da za a gudanar daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2018, za a gudanar da zaben shugabannin kungiyar, yayin da tsofaffin za su sauka. Shin ta yaya kuma yaushe ne aka zabi shugabannin kungiyar masu barin gado?

A ranar Alhamis 3 ga Afrilu, 2014 ne  aka gudanar da Babban Taron kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya ta Najeriya, a zauren taro na Musa Abdullahi da ke harabar Jami’ar Bayero, Kano.

Taron, wanda ake gudanar da shi kowace shekara, shi ne na 11 kuma an yi masa take ne da: ‘Bunkasar Tatsuniya: Jiya Da Yau Da Kuma Gobe.’ Haka kuma, an sadaukar da taron ne ga Shugaban Kwamitin Farfado da kungiyar, Dokta Bukar Usman, wanda kwararren marubuci ne a fagen Adabin Gargajiya.

Kuma an gudanar da kwarya-kwaryar zaben shugabannin da za su tafiyar da kungiyar na tsawon shekara biyu. Wadanda aka zaba a mukamai daban-daban sun hada da Dokta Bukar Usman, a matsayin Shugaba, sai Farfesa Olusegun Adekoya na Jami’ar Obafemi Awolowo, Ife a matsayin Mataimakin Shugaba na daya, sai Farfesa (Uwargida) Asabe Kabir Usman, ta Jami’ar Usman dan Fodiyo Sakkwato a matsayin Mataimakiyar Shugaba ta Biyu.

Sauran sun hada da Farfesa Sani Abba Aliyu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a matsayin Babban Sakatare. Wanda aka zaba a matsayin Ma’ajin kungiyar shi ne Farfesa Abdu Yahaya Bichi, na Jami’ar Bayero, Kano. Sakataren Kudi: Dokta Aloy N. Obika na Jami’ar Madonna, Okija. Jami’in Hulda da Jama’a: Dokta A. B. Kofa, na Jami’ar Jihar Kaduna. Editan Al’amuran kungiya kuwa shi ne Farfesa Mkem Okoh na Jami’ar Fatakwal. Mataimakin Edita: Farfesa Maikudi karaye na Jami’ar Bayero, Kano. Mataimakin Sakatare kuwa Dokta Bosede Afolayan, na Jami’ar Legas. Wanda aka zaba a mukamin Manajan Kasuwanci shi ne Dokta Daniel Omatsola na Jami’ar Abuja. Mai Binciken Kudi, Farfesa Ademola Dasylba na Jami’ar Ibadan.

Haka an kafa Kwamitin Amintattu na kungiyar a karkashin Shugabancin Farfesa G. G. Darah. Sauran mambobin kwamitin sun hada da Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa Bade Ajuwon, na Jami’ar Obafemi, Ife da Mista Ben Tomoloju da Farfesa Zikky Koforowola, na Jami’ar Ilorin da Farfesa Angela Miri, ta Jami’ar Jos da kuma Farfesa Afam Ebeogu, na Jami’ar Jihar Abiya.

A matsayinsa na sabon Shugaba a lokacin, Dokta Bukar Usman ya nemi zababbun shugabannin kungiyar da sauran mambobi su hada hannu domin yin aiki wurjanjan da nufin daga martabar kungiyar. Ya ce a iya lokacin da za su gudanar da al’amuran kungiyar, za su gudanar da tsare-tsare masu muhimanci, wadanda za su taimaka wajen bunkasa Adabin Gargajiya. Ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta yi kokarin fara buga ingantacciyar mujallar nazari, wadda za ta kunshi takardun bincike da nazari daga masana, kuma ya ce za a kafa jaridar da za ta rika bayyana labarun aikace-aikace da al’amuran kungiyar.