Yadda ake ado da gashin idon zamani

Akwai gashin ido na kanti wanda ake karawa a kan fatar ido domin kara wa gashin idon tsayi da kyau. An kirkiro irin wannan gashin idon ne don kara fito da kyawun mata musamman ma yayin gasar kyawu. A yanzu an wayi gari wannan gashin idon ana amfani da shi wurin yi wa amare kwalliya […]

Yadda ake ado da gashin idon zamani

Akwai gashin ido na kanti wanda ake karawa a kan fatar ido domin kara wa gashin idon tsayi da kyau. An kirkiro irin wannan gashin idon ne don kara fito da kyawun mata musamman ma yayin gasar kyawu. A yanzu an wayi gari wannan gashin idon ana amfani da shi wurin yi wa amare kwalliya yayin bikinsu domin kara musu kyawu da kwarjini. Mun kawo muku yadda ake sanya wannan gashin idon.

·        Yana da kyau a sanya gazal a kan fatar ido domin boye gashin idon kanti saboda kada a gano cewa ba na mai idon ba ce.
·        Daga nan a sanya maskara mai kauri a kan gashin domin su hadu da asalin gashin ido, hakan sai sanya gashin kantin ya zauna da kyau.
·        Kafin a sanya gashin idon kanti yana da kyau a dan rage musu tsawonsu da almakashi domin sukan zo da tsayi.
·        Bayan haka, sai a sanya gam kadan da dan yatsa kafin a dora gashin idon.
·        Sai a dora gashin idon a kan gam din da aka shafa a fatar ido. Yadda zai kama da asalin gashin ido.
·        Za a iya kara shafa gazal tsakanin fatar idon da gashin idon kanti.
·        Sannan sai a dada sanya maskara.