Yadda ake amfani da kwai a magance kurajen fuska
Kasancewar kuraje daga cikin ababen masu bata fuska, ya sa yake da kyau mu rika kula da fatar fuskarmu. Kula da fatar fuska na da matukar amfani musamman ma a lokacin damina inda fuska kan yi kuraje. Yadda za a rabu da gishirin fuska Hanyoyi mafiya sauki da za a inganta kwalliya Ababen da […]
Kasancewar kuraje daga cikin ababen masu bata fuska, ya sa yake da kyau mu rika kula da fatar fuskarmu.
Kula da fatar fuska na da matukar amfani musamman ma a lokacin damina inda fuska kan yi kuraje.
- Ababen da ake bukata:
- Kwai guda daya
- Takardar ’tissue’ guda daya
- Yadda ake yi:
- A fasa kwan a cire gwaiduwar.
- A kaɗa farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa.
- A shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.
- A lullube fuskar musamman daga kan hanci har zuwa kumatu da dan ’tissue paper’.
- Idan ya bushe sai a wanke fuskar.
- Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon mintoci 15.
- Daga nan sai a wanke fuskar.
- Amfanin kwai ga fuska:
- Kariya daga kuraje
- Kara hasken fuska
- Rage maikon fuska
Yadda ake amfani da kwai wajen gyran kurajen fuska ke nan.
Da fatanz a gwada a gani.