Yadda ake azumi a garin da rana ba ta faduwa
Watan azumin Ramadan, lokaci ne da Musulmi ke kaurace wa ci da sha daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana. Amma wani abun mamaki shi ne a yankin arewa mai nisa na Scandinabiya, Musulmi ba sa iya banbance lokacin fara azumin da kuma na buda baki saboda yadda rana kan kasance a kodayaushe ba tare da […]

Watan azumin Ramadan, lokaci ne da Musulmi ke kaurace wa ci da sha daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana. Amma wani abun mamaki shi ne a yankin arewa mai nisa na Scandinabiya, Musulmi ba sa iya banbance lokacin fara azumin da kuma na buda baki saboda yadda rana kan kasance a kodayaushe ba tare da faduwa ba.
Wannan na faruwa ne a garin Kiruna wanda yake da yawan Musulmi da suka kai 700, galibin jama’ar cikinsa masu sana’ar hakar ma’adanai ne. Garin yakan kasance a kewaye da tsaunukan kankara a lokacin bazara kuma yawancin mazaunansa baki ne wadanda aka baiwa mafakar siyasa. Garin na karkashin kasar Sweden ne wadda take nahiyar Turai. A kowacce shekara rana kan kasance ba tare da ta fadi ba tsakanin ranakun 28 ga watan Mayu zuwa 16 ga watan Juli. A bana wani bangare na wannan lokacin ya yi daidai da kwanaki 15 na watan azumin Ramadan.
A lokacin da gidan talabijin din Aljazeera ya tuntubi wani mazaunin garin mai suna Ghassan Alankar, dan asalin kasar Siriya ya ce: “Muna fara Sahur ne daga karfe 3:30 na asuba a wani yanayi mai cike da hasken rana. A lokacin nakan sanya labule guda biyu ne a tagar dakina saboda na rage hasken ranar da ke shigowa amma duk da haka haske ba ya fasa shiga cikin dakin.”
Al’ummar Musulmi da ke can suna yin azumin ne bisa dogaro da lokutan Sahul da Buda baki akalla guda hudu.
Mista Alankar ya ce yana azumin ne bisa dogaro da lokacin garin Makkah domin yin Sahur da kuma buda baki, a cewarsa, “saboda daga nan ne addinin Musulunci ya samo asali”. Amma kuma ya bayyana damuwa cewa ko azuminsa zai samu karbuwa wajen Ubangiji ko kuma a’a. Kodayake bisa dogaro da Fatawar Majalisar Fatawa da Bincike kan Addinin Musulunci ta Nahiyar Turai (ECFR), yawancin masu azumin na dogaro ne da lokutan babban birnin kasar, Stockholm mai nisan Kilomita 1240 daga garin, domin daukar azumi da buda baki da kuma gabatar da salloli farillai biyar a kowacce rana. A birnin Stockholm rana na fitowa da kuma faduwa kamar yadda ake samu a sauran wurare daban-daban na duniya.
Mabiya addinin Musulunci a duniya na fara azumi ne bayan ganin jinjirin watan Ramadan. Lokacin azumin na kowacce shekara yana bambanta da kirgar Kalandar Nasara da kwanaki 11. Wannan kan sa bayan kowacce shekara 33 yanayin da aka yi azumin kan kewayo ya zama daidai da yadda yake shekara 33 da suka wuce. Wanda kuma yake nufin yanayin garin Kiruna na rashin bambance dare da rana a lokacin azumin bana za a kara ganinsa ne a watan Ramadan din shekarar 2047 Miladiyya wato shekaru 33 masu zuwa.