Yadda ake azumi a garin da rana ba ta faduwa 1

Watan azumin Ramadan, lokaci ne da Musulmi ke kaurace wa ci da sha daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana a kullum har na tsawon kwanaki 29 ko 30. Amma wani abin mamaki shi ne a birni na biyu mafi girma a kasar Rasha, St Petersburg da wasu yankuna na arewacin kasar, Musulmi ba sa iya […]

Yadda ake azumi a garin da rana ba ta faduwa 1
Yadda ake azumi a garin da rana ba ta faduwa 1

Watan azumin Ramadan, lokaci ne da Musulmi ke kaurace wa ci da sha daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana a kullum har na tsawon kwanaki 29 ko 30. Amma wani abin mamaki shi ne a birni na biyu mafi girma a kasar Rasha, St Petersburg da wasu yankuna na arewacin kasar, Musulmi ba sa iya bambance lokacin fara azumin da kuma na buda baki saboda yadda rana kan kasance a kodayaushe ba tare da ta fadi ba, kamar yadda jaridar Birtaniya ta The Guardian ta bayyana.

mai nisa na Scandinabiya, Musulmi ba sa iya banbance lokacin fara azumin da kuma na buda baki saboda yadda rana kan kasance a kodayaushe ba tare da faduwa ba.
Kamar yadda shugabannin mabiya addinin Musulunci a birnin suka bayyana,“tsawon lokacin azumin a bana, wani abu ne na gwada karfin imanin mazauna birnin.” Mazauna birnin dai suna kwashe akalla sa’o’i 21 zuwa 22 daga sahur zuwa lokacin shan ruwa. Hakan na nufin cewa mazauna St Petersburg suna yin kasa da sa’o’i biyu zuwa uku ne daga lokacin buda baki zuwa daukar wani azumin.
Kodayake, babu alkalunman yawan Musulmin da ke zaune a birnin, lokacin karamar Sallar bara, akalla mutune dubu 42 ne suka halarci sallar idin a manyan masallatan birnin biyu, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta bayyana. Kuma kamar yadda yake faruwa a sassan duniya daban-daban, wasu masallatan sun yi sallah ne a kan titunan da ke kusa da masallatan.
Wasu malaman addinin Musulunci fitar da wata fatawa da ke cewa mazauna wadannan yankunan suna iya ajiye azumin zuwa lokutan da tsawon da dare da rana yake daidaita.
Kodayake, akwai wata fatawar da take cewa mazauna yankin suna iya yin azumin tare da amfani da lokutan fitowar alfijir da shan ruwar birnin Makkah, ko kuma na wani birnin da ke kusa da su.
Har ila yau, a lokacin azumin bara ma an samu irin wannan yanayi a wani gari mai suna, Karuna da ke kasar Sweden.