Yadda ake bautar berar Kumari a kasar Nepal
Chanira Bajracharya, ’yar shekara 15, ita ce berar da mabiya addinan Hindu da Buddha ke bauta wa a kasar Nepal. Wannan bera da mabiya addinai ke neman albarkar abin bauta da ita, a halin yanzu wa’adin zamanta a dakin bauta ya kusa karewa, don haka take nema wa kanta makoma.Bera BajracharyaKumari ta dage wajen koyon […]
Chanira Bajracharya, ’yar shekara 15, ita ce berar da mabiya addinan Hindu da Buddha ke bauta wa a kasar Nepal. Wannan bera da mabiya addinai ke neman albarkar abin bauta da ita, a halin yanzu wa’adin zamanta a dakin bauta ya kusa karewa, don haka take nema wa kanta makoma.
Bera Bajracharya
Kumari ta dage wajen koyon lissafi da harkokin sarrafa kudi. Don Bajracharya na hankoron zama ma’aikaciyar banki, idan ta samu kyakkyawan sakamako a fannin anzarin kasuwanci ko lissafin shige da ficen kudi.
“Ina son yin karatun fannin harkokin kasuwanci ko lissafin shige da ficen kudi,” Kamar yadda ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai Reuters a wata tattaunawa da suka yi da ita. A lokacin da aka yi hira da ita, wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ganta sanye da kayan kawa na ado, ta rambada kwalli a geffan idanunta da gira, an kuma yi mata zane a tsakiyar goshi.
Berar Kumari da mabiya addinai ke bauta wa, ba a cika barinta ta rika hulda da sauran mutanen waje ba. Ana kuma koyar da Berar Kumaru a wani kebabben wuri da ke cikin dakin ibada. “Tana rike karatu, kuma ba ta mantuwa,” a cewar wani malaminta Abha Awale.
Tsofaffin berorin Kumari da suka yi ritaya, wasu sun kama aiki, wasu kuwa sun yi aure. Kuma a kan biya berar Kumari albashin rupees dubu da 500 a kowane wata. A kan zabi kananan ’yan mata mabiya addinin Buddha daga al’ummar Newar da ke birnin Kathmandu, su zama “abin bauta, wadanda ake dauka cewa suna rayuwa ne a siffar abin bautar Hindu da ake kira “Kali.”
Kotun koli ta kasar Nepal a shekarar 2008 ta kafa dokar ilmantar da berar kumari da ke yi wa bauta, a kuma kula da lafiyarta. Ita Bajracharya ta ce tana cike da farin ciki: “Bana da takaici, saboda ban a fita waje. Ban yi wata asarar ba. Ba ni da kawaye, amma zan iya yin wasa da kannena,” inji ta.
Mafi yawan berorin kumara a da na shan wahala wajen samun mazan aure, don wasu na tunanin mazan na iya mutuwa. Da yake an samu ci gaban zamani, yanzu har karatu suke da zarar sun cika wa’adin ikonsu na kumara, bayan cikar balaga.