Yadda ake bikin Maulidi a sassan Najeriya
Al’ummar Musulmi na ci gaba da gudanar da shagulgulan Maulidi a matsayin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi. A Najeriya, Gwamnati ta ware ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun Maulidin bana, wanda ya yi daidai da 12 ga watan […]
Al’ummar Musulmi na ci gaba da gudanar da shagulgulan Maulidi a matsayin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi.
A Najeriya, Gwamnati ta ware ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun Maulidin bana, wanda ya yi daidai da 12 ga watan Rabi’ul Awwal a Kalandar Musulunci.
- Abubuwan da za ku so sani kan ’ya’yan Manzon Allah da ’ya’yansa
- Sabon Sarkin Zazzau ya kai ziyara Masarautar Kano
A bana, yawancin jihohi na bikin Maulidin ne daga safe zuwa yammaci maimakon yadda aka saba yi a cikin dare saboda dokar takaita lokutan fita da aka sanya a wasu jihohin sakamakon rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar #ENDSARS.
Aminiya ta samo hotunan yadda bikin Maulidin ke gudana a jihohin Kaduna da Gombe.