Yadda ake bikin murnar rabuwar aure a kasashen Larabawa

Tsohuwar al’adar al’ummomin da ke yankin sahara da ta zama banbarakwai ita ce ruguntsimin muranar da ake shirya wa matan da aka saki (ko aurensu ya mutu). Kuma wannan al’ada ta karade kasashen larabawa, musamman a kasashen ke Gabas ta Tsakiya. Irin nau’ukan bukukuwan sun bambanta a tsakanin rukinin iyalai, gwargwadon wadatarsu, amma dai babbar […]

Yadda ake bikin murnar rabuwar aure a kasashen Larabawa

Tsohuwar al’adar al’ummomin da ke yankin sahara da ta zama banbarakwai ita ce ruguntsimin muranar da ake shirya wa matan da aka saki (ko aurensu ya mutu). Kuma wannan al’ada ta karade kasashen larabawa, musamman a kasashen ke Gabas ta Tsakiya. Irin nau’ukan bukukuwan sun bambanta a tsakanin rukinin iyalai, gwargwadon wadatarsu, amma dai babbar manufar ita ce a yi murnar tarbar ’yar da ta komo cikin zuri’arta.

Da take bayanin kan irin halin da ta samu kanta a cikin, Hayat ta ce: “An tarbe ni da matukar farin ciki a gidan iyayena, inda mahaifiyata da da dimbin kawayena suka hallara. Sun yi kade-kade da raye-rayen al’ada na Hasssani, inda suka raba madara da dabino, ni kuwa na taka rawa tare da kawayena.”

Hayat Hussaina, wata da aurenta ya mutu, ta yi bayanin yadda ake gudanar da wannan biki na murnar dawowar wadda aka saketa, inda iyalai ke nuna goyon bayansu ga matar da aurenta yam utu. Bikin murnar rabuwar aure sako ne ga matar da aka saka; ba a yi watsi da ita ba, sabanin yadda ake dauka; domin zuri’ar waddda aka saki suna daukarta a matsayin matar da ke kiya daukar babban nauyi. An fi daukar shawararta da muhimmanci kanal’amuran iyali bisala’akari da gogewarta. Iyalai na da matukar zakuwar nuna wa ’yarsu cewa ita fa ta su ce, ba ta zama wani nauyi a gare sub a, don haka ka da ta shiga cikin damuwa.”

Hayat  ta ce ba ana yin bukukuwan ba ne don cusa haushi ga tsohon mijin matar da aka saka. Domin a cewarta: “Kawai ana isar da sako ne ga wadda aka saka cewa har yanzu tana da kimar daraja a al’ummarta, ba wai don a ci zarafin mijin da ya saketa ba ne, wanda a mafi akasarin lokuta shi ma ya fito ne daga zuri’ar da ke da yawa. Martaba dangantakar iyalai da girmama zumunta har yanzu lamari ne da ake gudanarwa.”

Fatimtu Dah ,wata matar da ta yi bikin murnar rabuwar aurenta (da mijinta) ta ce:”Bikin na nuni da bude sabon babin rrayuwa, wato matar a sshirye take ta sake yin wnai auren, musamman a al’ummomin da ke cikin Hamada da suka fi son matar da aka saketa, saboda tana da basira da gogewa kan al’amuran rayuwa da ta samu daga auren da ta yi a baya. Bikin dai iyaye ne da kawaye ke gudanar da shi don kwantar mata da hankali, sannan su tunatar da matar da aka saki cewa rayuwa ba ta kare a gidan tsohon mijinta kawai ba.”

Alghalia Mgharbilha ’yar jarida ce a birnin Ayoun el Atrous da ita ma aurenta yam utu. Alghalia ta uyi hira da kafar sadarwa ta ‘Dune boices,’ kan murnar bikin rabuwar aure, inda ta ce: “Sun yi mini kwarya-kwaryan biki da salon kidan al’ada na Hassani. Mun ci abinci tare, sannan muka zauna tsawon tare tare da juna (’yan uwa da kawaye).

Al kitb Takioullah, masani mai bincike kan al’ummar yankin sahara a Mauritania, ya ce: “Idan aka saki mace, sai ta koma wajen iyayenta, inda za ta same su tare da kawayenta su tarbe ta da madara da dabino da wake-wake masu tausasa zukata, don karfafa mata gwiwar ci gaba da harkokin rayuwa.”

Takioullah ya yi nuni da cewa, wannan dadaddiyar al’ada ce a Murtania, kuma mazan kasar Murtaniya sun fi son matar da ta taba yin aure aka saketa, saboda  gogewarta a harkar zaman aure da sadaukarwa.”

Ruguntsimin bikin murnar sakin aure lamari ne da ya karade kasashen Larabawa, har ta kai ga a kasar Saudiyya irin wwannan biki yana gogayya da na aure, kamar yadda jaridar Arabnews ta ruwaito. Kodayake a wannan lokacin ne bikin muranar sakin auren mace ke tashe a masarautar (Saudiyyya), ai ba sabon abu ba ne a daukacin Gabas ta Tsakiya, a cewar Jaruman fina-finan Larabawa, Mohammed Fawzi da Madiha Yousri, wadanda aka ce su ne farko a jerin shahararrun mutane da suka fara gudanar da wnanan biki. Sai ma da suka gayyyaci ’yan jarida da abokan huldarsu, wato kawaye da abokai, sannan suka bayyana rabuwarsu ta zaman aure tare.

Masana dai sun soki lamirin murnar bikin rabuwar aure bisa la’akari da yawan rabuwar auren da ake samu. Kafar sadarwa ta  shafin ‘The Media Line’ ta baje alkaluma karkashen taken “karuwar yawan sakin aure a Saudiyya,” inda aka yi nuni da karuwar sakin aure a masarautar. An bi kadin alkaluman Ma’aiaktar sharia, inda alkalumanta na shekarar 2016 suka ruwaito cewa kimanin rubuwar aure 127 na aukuwa kowace rana a masarautar. An ce a Jeddah kawai yawan rabuwar aure ya karu da kashi 50 cikin 100.

Reema Samir, matashiya mai shekara 30, kuma ma’aikaciyar wani kamfani mai zaman kansa a kasar Saudiyya ta ce: “Bikin murnar rabuwar aure shirme ne kawai. Kodayake akwai dimbin matsalolin da ke haifar wa ma’auarata rabuwa, amma murnar bikin ba matakin da ya dace ba ne. Ina ganin mace ko namjin da suka gudanar da irin wannan bikin suna da matsala a kwakwalwarsu ko sun damfaru da rudanin tunani. Domin mafi yawanci wadanda suka samu kansu a matsalar rabuwar aure sukan yi harigido a tsarin rayuwarsu, har ta kai ga sun sauya salo, ta yiwu saboda takaici ko irin kaduwar da ta same su.

“Hatta a kasashen Turai da al’adar ta samo asali kuma hada-hadar kasuwancin kayan makwalashen kek din sakin aure ke bunkasa, mutane cike da mamakin mutanen da hulda da kamfanonin shirya bikin murnar sakin aure. Domin a cewar kafar sadarwa ta Heathen Women:  “Wannan masana’anta mai karfin hada-hadar Dala biliyan 50, ba ita ce abin mamaki ba, illa dai mutanen da ke sarayar da kudinsu a cikinta don gudanar da bikin,” (https://heathenwomen.com/2016/07/28/the-diborce-industry/).