Yadda ake cin naman jakuna a Abuja

bata-garin mahauta da wadansu masu wuraren cin abinci a yankin Abuja da suka jima suna safarar naman jaki zuwa wadansu kasuwannin da gidajen abinci na yankin, sun fada komar kungiyar mahauta, inda a ka samu nasarar kama wadansu daga cikinsu bayan gano wajen da su ke yanka jakunan da kuma wuraren da su ke kaiwa […]

Yadda ake cin naman jakuna a Abuja

 Naman jaki da a ka kwace daga hannun yan tallabata-garin mahauta da wadansu masu wuraren cin abinci a yankin Abuja da suka jima suna safarar naman jaki zuwa wadansu kasuwannin da gidajen abinci na yankin, sun fada komar kungiyar mahauta, inda a ka samu nasarar kama wadansu daga cikinsu bayan gano wajen da su ke yanka jakunan da kuma wuraren da su ke kaiwa don sayarwa.
Aminiya ta samu labarin cewa lamarin,  ya biyo bayan korafin yawaitar matsalar ga masarautar fawa ta yankin Abuja da wadansu mazauna yankin suka yi ne, wanda ya sanya masarautar sarkin fawan ta himmatu wajen gano wuraren da ake aikata al’amarin da kuma yadda ake safararsa.
Sarkin fawan Abuja, Alhaj Usman Datti ya sanar da Aminiya cewa, bayan ya samu korafin ya tura  wadansu matasa daga babbar  kwata ta Abuja da ke cikin kasuwar dabbbi ta Deidei zuwa kauyen Idah da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, inda aka gano babbar mayanka da ake fede jakuna ana kawo su yankin Abuja.
Alhaji Usman Datti ya ci gaba da cewa, tawagar, wadda ta kunshi mutum biyar, da farko ta fuskanci tirjiya a mayankar, wanda ya sanya suka hanzarta ficewa daga wajen don gudun tashin hankali. Sai suka koma wani wuri suka jira har mahautan suka gama aikinsu, sannan suka bi sawunsu har zuwa garin Deideiei, inda wadansu suka dauki hanyar zuwa cikin gari, wadansu kuma suka dauki hanyar zuwa Gwagwa, kafin daga bisani aka kama su.
Ya ce adadin motocin da suka bi sun kai guda goma, kowanne da naman jaki don kaiwa kasuwanni ko gidajen abinci. Sai dai a cewarsa, motoci uku ne kawai suka samu nasarar kamawa. Haka nan ya ce an kama wadansu mahauta da ke safarar naman zuwa kasuwanni da kuma wadansu mata masu kaiwa gidajensu na abinci don sayarwa ga al’umma, sai kuma masu soya naman suna zagayawa da shi a cikin roba a wuraren taruka.
Da yake bayyana yadda ake bambance naman jaki da na saniya, sarkin na fawa ya ce naman jaki ba daya yake da na sa ko na rago ko na tunkiya  ba. “Naman jaki mugun nama ne, ba shi da launin ja da kyautatuwa irin na naman saniya, za ka ganshi fari kamar an wanke shi da sabulu, kuma shi bai da kitse kamar na alade, bai da mai, ba shi da kitse kamar yadda na sa yake da shi. Haka nan alamunsa yake, kamar dai na naman biri ko na kare. “Kuma idan ya yi jan launi za ka ganshi fau, bai da kala da za ka gani ka yi sha’awa kamar  naman sa, idan an soya sai ya kudundune ya y i baki, ga shi nan a kan titi ko’ina ana talla. Shi ko na sa za ka ganshi da kyallinsa da kyawunsa, yadda da ka ganshi za ka yi sha’awa.
Alhaji Usman Datti ya ce sun dauki matakan magance al’amarin, wanda ya hada da sanar da sarkin fawan Kaduna, kasancewar a kasarsa ce a lamarin ya faru, kuma suna shirin ziyartar fadan Ona na Abaji, wanda shi ne shugaban majalisar sarakuna ta Abuja, don sanar da shi al’amarin da nufin ya isar da sakonsu ga ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello na bukatar ya tattauna al’amarin da takwaransa na jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad el-Rufa’i, don kawo karshen mayankar, wanda ya ce mutanen sun jima suna damfarar jama’a da naman jakuna a matsayin na saniya.
 Ya ce, wajen ya shekara sama da talatin ana harkar, inda idan aka tinkare su sai su ce suna kai naman ne zuwa yankin kudu maso gabashin kasar nan, amma kamar shekaru uku ke nan da suka gawurta suka rika kawo naman zuwa Abuja ba tare da suna boyewa ba.
Sarkin fawan na Abuja ya kuma ce akwai wadansu wurare da ake gasa naman jakin, da suka hada da garuruwan Jere da Sabon-Wuse da kuma Dikko, amma sai a rika sanya alamun da ke nuna naman sa ko na rago a jikin naman.

Yadda muka kama su
– Sarkin samari
Isa Garba shi ne sarkin samarin Deidei, shi ya jagranci matasan da suka je mayankar jakunan, ya bayyana wa Aminiya irin arangamar da suka yi da mahautan a wajen. “Bayan labari a kan mahautan ya zo ga sarkin fawa, ya umarce mu da mu je wajen, kuma a nan muka sanar da karamin ofishin ’yan sanda na Deidei. Mun je mahautar da ke kauyen Idah kuma adadin jakunan da muka samu, wadanda suka hada da masu rai da kuma matattu, sun haura dari, kuma abin mamaki sai ga wadansu ’yan fawa da dama da muka sani a wajen, yawancinsu mata. Su ke jigilar kai naman zuwa kasuwanni da gidajen abinci, kuma dukkansu kabilun yankin kudu ne, da suka hada da ibo da kuma yarbawa, amma shugaban mahautar bahaushe ne.
“Bayan gabatar da kanmu a wajensu, sai suka nemi yin arangama da mu, amma sai muka ja da baya don magance tashin hankali, muka ci gaba da zama a garin na tsawon lokaci har suka fara lodin naman a mota, kuma a nan muka bi motocin a baya, dama mun sanar da jagoran ’yan sanda na Deidei al’amarin, sai dai tun a Mararrabar Bwari muka rabu da wadansu motocin, wadansu kuma mun rabu da su ne a shingen bincike na sojoji na Deidei. Mun  samu nasarar kama wadansu daga cikinsu a yankin Gwagwa da kuma Zuba, tare da taimakon ’yansanda.’’
Aminiya ta samu labarin cewa, wadanda aka kaman da adadinsu ya kai 11, yawancinsu sun samu beli tun a wajen ’yan sanda, a yayin da mutum uku kuma da aka gabatar da su a gaban babbabar kotun lardi mai daraja ta daya da ke Zuba, an ba da belinsu a kotun tare da dage ci gaban zama a kan lamarin zuwa ranar 29 ga watan Yuli.