Yadda ake cin zalin daliban Najeriya da suka makale a Ukraine
Duka da zagi da wariyar launin fata da ake nuna wa bakin dalibai da ke neman ficewa daga Ukraine
Daliban Najeriya da sauran baki da suka makale a kasar Ukraine bayan barkewar yaki sun koka kan yadda jami’an tsaron kasar suke cin zalinsu da nuna musu wariyar launin fata a kan iyakokin kasar.
Wata daliba daga Najeriya, Rachel Onyegbule, da ke karatun aikin likita a Ukraine, ta ce jami’an tsaron kasar sun tilasta mata tare da sauran dalibai da suka fito daga kasashen Afirka sauka daga wata bas a wani shingen bincike a iyakar kasar da Poland, suka sa motar ta wuce da ’yan kasar Ukraine zalla.
“Muna kallo manyan bas sama da 10 suka zo suka wuce suka bar mu; Mun yi zaton idan sun gama kwashe ’yan Ukraine za su dauke mu, amma jami’an suka ce sai dai mu taka a kasa, motoci sun kare, babu mai daukar mu.”
Racheal wadda ke shekararta ta farko a jami’ar da ke Lviv ta ce haka suka ci gaba da tsayuwa a cikin matsanancin sanyi a garin Shehyni mai nisan mil 400 daga Kiev, babban birnin kasar Ukraine, daga baya suka taka zuwa kan iyakan.
Ta bayyan hakan ne ta wayar tarho a lokacin zantawarta da kafar yada labarai ta CNN, ranar Lahadi a lokacin da take kokarin tsallakawa zuwa kasar Poland daga Ukraine.
A karshe dai a ranar Litinin da misalin karfe 4.30 na asuba, dalibar ta samu sahalewar shiga Poland.
Dalibai daga kasashen waje na yawan zuwa Ukraine domin karatun aikin likita, saboda yadda kasar ta yi zarra wajen kwarewa a fannin.
Kungiyar masu kula da ’yan Najeriya a kasashen waje ta ce daliban Najeriya sama da 12,000 ne ke karatu a Ukraine a halin yanzu.
Abigail ta ce, “ Suna hana baki wucewa, suna nuna tsananin wariyar launin fata. Sun shaida mana cewa sai ’yan Ukraine sun fara wucewa kafin baki.
“Yanzu haka da kyar ’yan Najeriya da sauran baki suke samun wucewa. Jami’an Ukraine na barin ’yan kasarsu su tsallaka zuwa Poland.
’Yan Afirka a Ukraine na neman agaji
A halin yanzu, ’yan Afirka da ke Ukrain na bayyana irin bakar wahalar da suke ciki a Ukraine, da taken #AfricansinUkraine a kafofin sadarwa na zamani.
Korrine Sky, daga kasar Zimbabwe, wadda ita ma take karatun aikin likita a Ukraine ta ce, “Yanayi ne na a-mutu-ko-a-yi-rai. Ya kamata a yi duk mai yiwuwa na gadin daukacin dalibai daga nahiya Afirka sun fice daga kasar Ukraine lafiya kuma cikin nasara.”
Sky ta bayyana haka ne a ranar Lahadi, bayan da ta samu ficewa daga kasar zuwa kasar Romania tun ranar Juma’a.
Ta ce ta samu ficewa daga Ukarine nda da taimakon wasu wadanda ta sani a birnin London na kasar Birtaniya, wadanda suka tara Dala 26,800 domin tallafa wa daliban Afirka da yakin Caribbean da suka makale a Ukraine.
An hana ’yan Iniya wucewa
Wata daliba da ke aji hudu na koyon likitanci daga kasar Indiya, Saakshi Ijantkar, ta bayyana wa CNN daga Lviv, cewa, “Sai mutum ya wuce shingayen bincike uku kafin ya kai kan iyakar kasar. Mutane sun yi cirko-cirko, ga shi an hana ’yan Indiya wucewa.”
“’Yan Indiya 30 kacal ake bari su wuce, idan ’yan Ukraine 500 sun tsallaka, kuma kafin ka zo wurin sai ka yi tafiyar kilomita hudu zuwa biyar a kasa tsakanin kowane shingen bincike.”
Dalibar mai shekara 22 ta ce, “’Yan Ukraine ana ba su bas ko tasi su hau, ’yan sauran kasashe sai dai su taka a kasa. Suna da tsananin nuna wariya ga ’yan Indiya da sauran kasashe.”
Cin zalin dalibai
Saakshi ta ce, ta kuma ga yadda jami’an tsaron iyakar kasar suke cin zalin dalibai dake jiran samu tsallakawa daga Ukraine a kan iyakar da ta hada Shehynida Medyka.
Saakshi ta ce jami’an tsaron kasar sun bar dalibai maza ’yan kasar waje na tsawon awanni a tsaye a kan layi tare da mazaje daga wasu kasashe.
“Kananan yara mata ’yan Indiya kadai suke bari su wuce. Haka muka rika durkusawa muna faduwa a kan gwiyawunmu a gabansu muna rokon su.
Rashin imani
“Ina kallo lokacin da wani dan kasar Masar da ke tsaye ya dora hannunsa a kan karfen gefen hanya; Saboda wannan kawai jami’an tsaron suka tunkude shi da karfi ya fada kan shigen da aka sanya wa kayoyi na karfe, nan take ya fadi magashiyyan.
Ta ce dalibai sun shafe fiye da kwana guda suna jira a bari su wuce, amma ita juyawa ta yi, ta koma Lviv saboda irin abin tashin hanklin da ta gani gami da tsananin sanyi, ga kuma rashin abinci da ruwan sha da isassun kayan sanyi.
CNN ta yi kokarin samun martani daga rundunar sojin kasar Ukraine game da wannan zargi, amma hakan ya gagara, har zuwa lokacin da muka samu wannan rahoton.
Amma kakakin hukumar tsaron iyakar Ukraine, Andriy Demchenko, ya musanta zargin nuna wariyar launin fata da ake wa jami’an hukumar, inda ya ce jami’an na cikin mawuyacin hali — amma a bisa doka.