Yadda ake dafa dambun Kuskus
Sallama gare ki uwargida yaya fama da tarbiyyar yara? Allah Ya ba mu sa’a wajen sauke nauyin da ke kanmu. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar dambun Kuskus tare da fatar za a gwada wannan girkin ga maigida ko baki. Za a iya cin wannan girki bayan an dawo daga aiki ko a […]
Sallama gare ki uwargida yaya fama da tarbiyyar yara? Allah Ya ba mu sa’a wajen sauke nauyin da ke kanmu. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar dambun Kuskus tare da fatar za a gwada wannan girkin ga maigida ko baki. Za a iya cin wannan girki bayan an dawo daga aiki ko a ci a lokacin karin kumallo. Yana da kyau maigida ya rika ganin canji a girkin da uwargida take dafawa musamman a wannan lokaci na damina.
Abubuwan da za a bukata
- Kuskus
- Koren wake (green beans)
- Albasa
- Attarugu
- Hanta ko nama
- Magi
- Kori
- Man gyada
Hadi
A samu hanta ko nama a dafa ta har sai ta yi laushi sosai. Sannan sai a samu albasa da attarugu a yanyanka su su ma kanana. Bayan hanta ta nuna ita ma a yanka ta kanana. Kada a zubar da ruwan da aka tafasa hantar ko naman. Ana so a ajiye a gefe saboda dafa Kuskus din da shi. A dauko ruwan nama a zuba a kan danyen Kuskus da magi da kori da attarugu da albasa da man gyada. Sannan a juya su kafin a samu leda a rufe da marufi. Sai a jira na tsawon minti biyar. Sai a sauke.
Za a iya sanya zogale ko alayyahu a cikin wannan girki domin dada armashi da kuma gardi. Lallai idan maigida ya ci wannan girkin sai kunnensa ya yi motsi.