Yadda ake dafa-dukan Kus-kus da naman kaza
Yadda ake dafa-dukan Kus-kus da naman kaza
Barkanmu da sake kasancewa a wannan filin na Girke-girken Azumi.
A yau Aminiya za ta kawo maku yadda ake hadin dafa-dukan Kus-kus da naman kaza.
Kayan hadi
⁃ Kus kus
⁃ Albasa
⁃ Attarugu
⁃ Tattasai
⁃ Gayen ‘parsley’
⁃ Naman kaza
⁃ Sinadarin dandano
⁃ Man gyada
⁃ Kukumba
⁃ Tumatir
Yadda ake hadawa
⁃ Da farko za a wanke naman kaza sai a zuba su curry da thyme da magi a cikin naman.
⁃ A wanke Attarugu, Albasa, da Tattasai, sai a markada sannan a zuba a cikin naman kazar.
⁃ A saka hadin kazan a firji na minti 10.
⁃ Bayan minti 10 sai a dora tukunya a wuta sai a zuba man gyada.
– Idan mai ya yi zafi sosai sai a soya naman kazan har sai ta soyu sosai sai a kwashe a zuba a kwano.
⁃ A dora wani tukunya a wuta, a zuba ruwa a bari har sai ya tafasa.
⁃ A zuba kus kus a kwano mai dan girma sai a barbada man gyada kadan.
– A zuba tafasasshen ruwa sai a juye a rufe na minti 10.
⁃ A yayyanka albasa da tumatir da tattasai da gayen ‘parsley’ da kukumba sai a ajiye a gefe.
⁃ A zuba man gyada a wuta sai a zuba albasa da tumatir da tattasai da sinadarin dandano sai a jujjuya a kashe wuta.
⁃ A zuba kuskus sai a juye sosai a zuba kukumba da ganyen ‘parsley’.
Shike nan kus-kus ya yi, a zuba a kwano sai a sa naman kazan a gefe.